New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 25

ABDUL WAHAB 25

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Da'kyar ta share hawayenta, ni'kab dinta ta ciro ta maida, kanta na 'kara tsananta mata ciwo kamar zai rabe biyu

Haka ta fito duk gidan cike da mutane ta fara ra'basu ta wuce babu wanda ya ganeta, harta gama fita daga gidan jefa 'kafarta kawai take, daman a waje tayi parking motarta ta shige ta koma gidansu.

Babu kowa sai masu aiki ta haye upstars dakinta ta shige ta fad'a saman gado ta saki wani sabon kukan, da'kyar ta iya lalubo maganin ciwon kai tasha, ta koma ta kwanta ta rufa da bango saboda zazza'bin daya rufeta.

Tananan kwance cikin jinyar kanta har bayan magrib, kiran wayar Alhajinsu ya shigo mata da'kyar ta iya d'auka, tohm kawai naji taace sannan ta tashi tsaye ta fara bin bango harta isa d'akinshi.

Alhaji, mami, Abdul wahab, fatima, da qanwar maman hajia ne zaune a wajen, kamar wadda ake jefawa ta samu wuri da'kyar ta zauna, ba tace komi ba anma yanayinta kawai zaka gane tana cikin damuwa.

Sai da Alhaji ya gama yima fatima nasihar zaman aure sosae, mai ratsa jiki, tana ta kuka, sadeey ma duk taa nutsu tana saurare, sannan ya dawo kanta, kiran sunanta yayi ta d'an dago kai ba tare data kalleshi ba, yace "kinsan dalilin da yasa muka kiraki anan? Girgiza kanta tayi dake mata barazanar rabewa biyu gabanta naa matsanancin fad'uwa.

Yaci gaba "wani hukuncine muka yanke akanki ba tare da neman shawararki ba, kasancewarki mai matu'kar biyayya da bin umarninmu, kuma munsan insha Allah a wannan karon ma zakiyi biyayya ki kar'bi abnda mukazo miki da hannu biyu.

Duk maganar da Alhaji keyi jinshi kawai take, ko kad'an bata fahimta kamar wadda akaima satar 'kwalwa, tana can duniyar tunani da rud'u kamar daga sama taji Alhaji yace "A yau ne Aka d'aura aurenki da yayanku Abdul," da sauri ta juyo tana kallon Alhaji, kamar zararra ta fara 'karema 'yan cikin d'akin kallo.

Maminta ta tsura ma ido tana so ta gaskata Abnda Alhaji ya fad'a, wani irin kuka ta fashe dashi tana girgiza kai tace "bazan iya ba, wlhy bazan iya ba dad, bazan iya auren yayanmu ba har in zauna dashi, bani yakeso ba, saboda yaa rasa wacce yakeso ne yakeso yayi auren huce haushi dani, kuma bazan taba zama ba," A marairece ta kalli mami tace "don Allah maminah ki sanya baki yayanmu ya sauwa'kemin, don bazan iya......, wata irin tsawa Alhaji ya daka mata Yace "ke wacce irin macece sadeey? Tarbiyar da muka baki kenan? A gabanmu mijin da kowa ya shaida aurenku zaki ce ya sauwa'ke miki? Kina son tsinuwar mala'iku ta fad'a kanki?

Dafe kanta tayi, wani irin zogi takeji a zuciyarta, taama rasa abn fad'a, hawayen dake sanya mata sassauci a zuciya suma sun tsaya, mi'kewa tayi tabar d'akin da gudu, a 'kofar d'aki ta fad'i.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts