New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Sunday, 18 February 2018

MAFARIN SO 1-5

♡♡MAFARIN SO♡♡
   ♡♡♡♡♡♡♡♡      
         ♡♡♡♡♡
                1-5

©Rabiatu sk mashi
         ®NWA

Rerbeeart_sk @wattpad

www.babymsh.blogspot.com

Tafiya take cikin nutsuwa, burgewa, da takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan material, kalan brown da milk, saita yafa k'aramin mayafi akai, tana rik'e da wasu littafai a hannunta.
      Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin k'unar zuciya ta ɗago da kanta tana k'arema wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da ɗaliban jami'ar kuma kusan duka hankalinsu na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne, juyawa tayi ta watsa mishi harara.
    Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan,
    "zo mana" ya kirata da hannu, yana zaune saman motah da en korenshi zagaye dashi, taso ace zata iya komawa ta sauke mishi duk masifan dake ranta, anma jin kanta da tak'ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana maida magana dashi ba. Juyawanta kawai tayi taci gaba da tafiyanta,
      Batasan sanda ya diro daga saman motan ba, sai dai kawai taji yana neman rik'o hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta wankeshi da marin da yazo mishi a bazata, ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan kowa ya fara k'ok'arin riƙe dariyanshi don babu wanda baisan halin Abdallah ba.
       "Ni kika mara?"
     "an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da kake"
        "ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi dana sanin marina da kikai"
     "Anma bakasan wacece Rabi'ah ba, kuma ina mai baka shawaran karka zaƙe akan saika sani ɗin"
     Nunata yayi da ɗan yasha, "zan ramane a inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi soyayya dani"
    Tofar da yawu tayi a k'asa, "Allah ya kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye" ta juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama kasa maida mata magana, ya watsa ma mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace, ya shige motanshi ya jata a guje.

Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka fito tare da Aminiyarta Amrah,  hannunta taja suka koma gefe,
      "Faɗamin Rabi'ah meye gaskiyar abinda naji wai kin mari Abdallah"
     "toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman wani babban abune ya faru?"
    "haba Rabi'ah, naga hankalinki kwance kaman bakisan halin Abdallah ba"
    "ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban taɓayin abunda nayi dana sani ba"
     "hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake"
     "kinma warware,"

Tun daga bakin gate, ma'aikatan gidan ke kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu isheshi ba, ganin motoci da yawa ya tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin Governor ya wuce,
      Zaune yake yana amsa waya, bodyguards nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa gama ba ya katse wayan.
     "Yadai Son?" cikin sham ƙamshi ya kalli bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito, cikin bin Umarni duk suka fita.
      "waye kuma ya taɓomin kai?"
   Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya fara magana, "Haba Dad! Ni bansan me yasa baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka dani sai harkan siyasarka kawai"
     "akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi maka bane?"
     "A'ah kawai dai wannan ne nake tunanin bazan samu ba"
    "babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai a duniya babu abinda zaka nema bazanyi maka ba"
      "I know Dad, but uh should promise me"
     "promise"
   "thank you Dad, i love you"
Sannan ya fara fara'a, jinsa yake wasai kaman yama riga da yaa rama abinda Rabi'ah ta mishi.

Follow me On wattpad @Rerbeeart_sk

©Rabiatu sk msh

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.