♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
1-5
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
GODIYA
Ta tabbata ga ubangiji mahaliccin sammai da k'assai, daya bani ikon fara rubuta littafinnan, ya Allah ka bani ikon gamashi lafiya, ka yafemun kuraren dake ciki, Ameen ya Rabbi
www.babymsh.blogspot.com
Kuka takeyi tun bayan da en tsirarun mutanen da suka rakota suka tafi, kuka take wanda tunda aka haifeta bata taɓa yin irinshi ba, duk da tunda tayi wayau bata taɓa tsallake rana ɗaya ba ba tare data zubda hawayen bak'in ciki ba, yau kukan nata har yaso ya k'arar da hawayen nata, ga wani irin shesshek'a da takeyi,
Sallamar da yayi ne ya sanyata tsagaita kukan, a hankali ta fara k'ok'arin share hawayen nata duk da kukan yak'i tsayawa,
"Har yanzu dai kukannan kike Saude?" ta share hawayenta cikin murya kuka tace "na daina fa"
"Yauwah ko kefa, ay saiki saka kanki yayi ciwo, ga gajiyar hidimar biki kuma"
"Idan banyi kuka ba Uncle Yasseer waya kamata yayi?"
"kina kuka don an haɗaki aure da mak'iyinki ko?" da sauri ta fara girgiza kai "A'ah wlhy ba haka bane, kawai dai abunne na k'onamun zuciyah, ban tunanin duk duniya akwai macen da aka taɓa ma wulak'antaccen aure irin nawa, kayi hak'uri nasan kaima ba sona kake ba lik'a makani kawai akayi, don babu ta inda muka dace"
"Who said so? Ke kyakkyawah ce saude, kina da kyawawan halaye, Ina sonki saude, fiye da yanda kowa zai soki a duniyarnan, kuma ban tunanin akwai macen dana dace da ita bayanke, idan kuma kina ganin akwai inda bamu dace ba ki faɗa mun sai in gyara"
"Akwai babban banbanci fa tsakaninmu, ni ina er k'auye, kai kuma ɗan birni kuma ɗan gayu" shiru yayi yana k'ara mamakinta, maganganun saude, wayonta da zurfin tunaninta sunfi k'arfin shekarunta, ya nisa sannan ya fara bata amsa,
"Tohh yanzu ba gani a k'auyen ba? Kinga mun zama ɗaya kenan, kuma idanna gama bautar k'asana ai dake zan tafi birnin, kema ki zama er birni, ki daina tunanin akwai banbanci a tsakaninmu, babu wanda yafi wani a wurin Allah, sai wanda yafi tsoronshi" ɗaga kanta tayi tana share hawaye, maganganunshi sunyi tasiri sosae a zuciyarta,
Hannu ya saka yana tayata share hawayen "kin daina kuka daga yau Saude, bai miki kyau, hawayen farin ciki kawai nakeson gani a fuskarki" ya jawota zai rungume a k'irjinshi, ta fara togewa tana tureshi, duk da jikinta yayi sanyi tun sanda ya fara share mata hawaye,
"bakison in taɓaki?" ta ɗaga mishi kai,
"Ai ba wani abu an miki ba kinji ki saki jikinki dani kinji, duk sanda kike cikin damuwa, anan ne ya kamata ki kwanta kiyi kukanki, duk da bazan taɓa bari ki shiga damuwa ba" ta ɗago tana kallonshi yana nuna mata k'irjinshi da hannu, ya k'ara jawota zai haɗata da jikinshi, ta mak'ale kafaɗa duk ta takure, ya saketa kawai "shikenan tashi kiyi alwala muyi sallah, nima bara inyo"
"nayi sallah fa"
"wannan ta musammance zamuyi, domin mik'a godia ga Ubangiji, da kuma neman albarka a cikin auren namu" kai kawai ta ɗaga mishi, ya tashi ya fara fita, maida kai tayi ta jinginar tana tunanin rayuwarta ta baya, da kuma haɗuwarta da Uncle Yasseer.
****
Wata rana matar k'anin mahaifinta Gwaggo Bilki, taa aiketa ebo ruwa rafi, tafiyah take a gajiye ga yunwa tun asuba take aiki ko tsugunawa batayi ballantana ta samu damar zaunawa ta huta, tana tafiya tana haɗa hanya har tazo dai dai wata bishiyar magwaro da wasu yara biyu keta faman jefa dutsi yak'i ya faɗo, ɗaya daga cikin yaran ya k'wala mata kira,
"Saude don Allah kizo ki ciro mana mangwaronnan"
Taja ta tsaya tana tunani a ranta, ko a kan lokaci ta koma gida sai gwaggo bilki tayi mata faɗa, ballantana ta tsaya hanya,
"A'ah kabiruwa, ɗebo ruwa nake idanna tsaya gwaggo zatamun faɗa, kayi hak'uri kaji"
"Dan Allah nace fa saude, ni sai in ɗebo miki ruwan" ya taho yana k'ok'arin amsar tulun a hannunta,
"shikenan anma kuyi sauri fa,"
"Tohh anma fa da yawa zaki ɗebo mana"
"naji nace" ta tafi ta fara k'ok'arin hawan bishiyar, duk da ba wani iyawa tayi ba, anma duk k'auyen su kabiruwa na ɗaya daga cikin yaran da basu mata rashin kunya.
Saida ta gama, jefo mangwarorin a k'asa, taa fara k'ok'arin saukowa, taji k'afarta taa zamo, da sauri ta rik'e wani reshe, anma kasancewar baida k'wari taji ya fara ɓallowa gashi har lokacin su kabiruwa basu dawo ba, ta rink'a kuka ta rasa yanda zatayi, saidai taji taa faɗa k'asa tim saman wani abu.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment