New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 66

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             66

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    A baya Saude ta zauna, ta koma can gefe ta rakuɓe tanata zullumi a ranta, yana drivin yana hangenta ta mirrow, k'arar shigowan message taji a wayanta, ta duba daga Najib ne.
        "Ya dai?" kallonshi tayi ta mirrow, ya ɗaga mata gira yana murmushi.
   "Meka gani?" ta mayar mishi.
  "Kinyi shiru kamar kina da damuwa, ko duk kunyar Momie ne?"
   Sai data murmusa data gama karantawa, sai ga wani text ɗin nashi ya k'ara shigowa, "wannan fuskar nakeson gani har muje, murmushi yafi miki kyau" dariya tayi kawai ta tsura mishi ido ta mirrow shima tana kallonshi, duk Momie na lura dasu, ciki-ciki take musu dariya.
  Mik'a hannu tayi ta anshe wayar tashi, "kana wannan gudun kuma bazaka maida hankali a tuk'i ba" da sauri yabi hannunta zai ansa wayan,
  "plz momie ba wani abu nake ba, lokaci nake dubawa"
   "kana duba na motan tohh"
Ta cikin mirrow ta mishi gwalo tana dariya, ya harareta da wasa, bata daina mishi dariyar ba.

  Kwata-kwata ta manta da Momie a wurin, ta kwanto jikin kujerar da yake, suna kallon juna ta cikin mudubin kowanne ya kasa ɗauke idonshi, sak'on soyayyar da suka kasa furtawa a baki saboda Momie na wurin ne suke aika ma juna ta kallo.
   Garin kallo sunje shiga wani gari, bai lura da bump ba ya faɗa mishi kawai, su duka saida suka razane banda Momie da daman tana sane dashi, ta wutsiyar ido yake kallonta, saida taga abun nasu bamai k'arewa bane, ta saka hannu ta juya mirrow ɗin, su duka har saurin kai hannu suke su gyara, saida Saude ta lura Momie ce ta koma a kunyace ta zauna.
    Saida suka isa garin Katsina suka tsaya sukayi Sallah, wani restaurant sukaje sukaci suka k'oshi, sannan suka kama hanyar k'auyensu Saude.
 
  Da yake akwai nisa daga katsinarma, saida suka k'arayin tafiya mai nisa sannan suka isa k'auyen, Najib dai bin k'auyukan wurin kawai yake da kallo, wai anan Saude tayi rayuwa, nan wurin  har akwai halittar dake rayuwa.
   Itama bin k'auyen kawai take da kallo, tayi kewarshi da yawa, shekara ɗaya da en watanni ko zagayoshi bata k'arayi ba, ba laifi k'auyensu an samu en canje-canje, anma bazata iya mantawa da k'auyenba, kai tsaye take nuna mishi hanyan gidan Kawu duk da k'auyen ba yawane dashi ba. Yananan inda yake, sai dai yaa k'ara lalacewa, ginin jar k'asar duk ya zaganye sai tsummuna ne aka ɗaure akayi kamar katangar dasu, suma duk sun ciccire, wurin dai babu kyaun gani, cikin zuciyarta tayi mutuk'ar tausaya musu,
   Momie tace ta shiga ta fara sanar musu zuwansu,ta buɗa motan ta fita, tana k'ara k'arema wurin kallo.

  Cikin gidanma duk ya lalace, k'asan tayi gamsa kuka da ciyayi ko ina, ɗaki ɗaya tal ya rage a gidan, shima rufin duk ya zazzare, tana daga bakin ƙofa sai rangaɗa sallama take babu alamun kowa a gidan, harta fara gajia, saiga Gwaggo ta fito daga bayan gida, can gefen ɗakin aka zagaye wani wuri shima da tsummokara, tana ganin Saude ta washe baki.
    "A'a'aah sannu da zuwa, sannu da zuwa" duk ta rasa inda zata sakata don murna, don ko kaɗan bata ganeta ba.
  Can gefe ta tillar da gwangwanin ruwan hannunta, ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma da tsintsiya, ta share wuri sannan ta shimfiɗa mata tabarmar ta zauna, ita dai Saude sai binta da murmushi take ganin yanda take ta zakwaɗi tasan lalle gwaggo bata gane ta ba.
   "daga ina? Halan bak'in gidan mai gari ne? Sannu fa kunsha hanya"
   "A'ah nan gidan nazo gwaggo"
   "Gwaggo kuma? Kai gaskia badai ni ba, bansan kowa a birni ba, ki dai tuna gidan da kike nema"
   "Gidan da nake nema nazo Gwaggo bilki, gidan Kawo Ado"
  "eeh gaskia gidanne kikazo" gwaggo ta faɗa cikin sanyin jiki tana ja da baya, "Allah yasa dai ba wani abunne kikazo dashi ba baiwar Allah"
   "ki kwantar da hankalinki Gwaggo, Alkhari kawai nazo dashi"
  "tohh wacece ke?"

  Kawu Ado ne ya shigo gidan har yana tuntuɓe, yake k'walama gwaggo kira, burki yaja a tsakar gidan ganinta da bak'uwar fuska. Shima dai washe bakin yayi suka gaisa da ita, sannan yaja gwaggo can gefe.
   "Ina Mak'era aka faɗamun bak'i sun tsaya da k'atuwar mota k'ofar gidannan, nama ɗauka matsiyacin yaronnan ne"
  "bashi bane, bak'uwa ce dai mukayi daga birni"
  "gidan mai gari tazo ko gidan sarkin noma?"
   "gidannan tace tana nema, anma dai bata faɗi daga inda tazo ba"
   "tohh fa, Allah yasa ba sace mana kawuna tazo cikin k'atuwar motarnan ba"
   Suka jiyo su duka sunason tambayarta, su duka sun k'ara tsufa, kawu Ado duk gashin jikinshi ya cika da furfura.
    "baiwar Allah daga ina? Kuma wa kikazo nema?" kawu Ado ya mata tambayar.
  Tana murmushi tace, "Kawu daman Saude...."

   "Sauden K'aniya, idan ma nemanta kikazo kinzo gidan da bazaki dace bane, tunda tsohin mijinta ya gudu ya barta itama ta gama gabanta, tun kafin magana tayi nisa tsakaninmu kibar gidannan kije can kici gaba da dubata gidan karuwai"
   Rumtse idonta tayi sosai maganar ta soketa
  Gwaggo ta tari numfashinshi, "Malam anyi haka?"
  Idonta a rufe, tanajin k'una a zuciyarta tace "Sauden ce kawu"
    "Saude?" suka maimaita a tare, ta ɗaga musu kai, kunya saita kama kawu ya fara kame-kame.
   "Saude kece kika zama haka? Kin tafi birni kin manta damu, munanan muna ta addu'ah Allah ya kawoki, yasa kina cikin k'oshin lafiya, ko bilki?"
   "eeh eeh mana"
      "Alhmdlh Saude ina kika shige haka? Don bamu muka haifeki ba shikenan kika manta damu, anma dai aimu muka rik'eki har girmanki"
   "eeh mana, baki kyautaba Saude kinbar iyayenki cikin fargaba, ni banmasan ta inda zan fara bayyana farin cikin dana shiga da ganinki ba" kawu ya k'arasa maganar yana sharar k'walla.
   "kuyi hak'uri kawu, nima kuna raina"
   Nan fa suka sanyata gaba, ganin yanda ta koma lallai tayi kuɗi tana cikin jin daɗi, sunma rasa inda zasu sakata.

Saida taga sun ɗan natsa, tace "bani kaɗai nazo ba, harda hajiar da nake gidanta, da kuma ɗanta, kuma dai da maganar da sukazo da ita"
    "tare kukazo kuma bazaki shigo dasu ba? Kai Saude kinanan dai da halinki na kawaici" kawu ya faɗa, harda dariya shinan ya faɗa abun kirki.
    "tohm malam a shigo dasu bara a musu shinfiɗa"
   Gwaggo ta kwaso wasu tabarmun ta shimfiɗa musu kafin ya shigo dasu, su Kawo har kyarmar jiki ake, da hannu bibbiyu suka tarbesu, aka shimfiɗesu saman tabarma.

  Gwaggi da kanta ta saka mayafi, bashin ruwan laida mai sanyi an sakashi a randa ta anso musu, ta kawo sannan suka shiga gaisawa, en k'auyen har an fara cika gidan suna murna Saude ta dawo, ta canja ta zama er gayu. Bata k'yamacesu ba ko kaɗan, ta shiga cikinsu suna ta labari, har dare suna tare. Najib dai fita yayi ya basu wuri bayan sun gama gaisawa.
   Da yake dare yayi, kuma babu wurin da zasu kwanta a gidan, sai suka koma cikin gari babu nisa da k'auyen, a can suka samu hotel zasu kwana, banda Saude, cewa tayi a gidansu zata kwana.
  Gatan da bata taɓa tunanin samu ba su kawo suke nuna mata, don gaba ɗaya fita sukai daga ɗakin sukace ta kwanta ita zasu kwana a waje, tace su barta ta kwana inda ta saba anma sukak'i, duk yanda taso, anma a ɗakin dai suka bar mata ta kwana ita kaɗai.
  Su Momie sun tafi a zuwan sai gobe zasu dawo ayi magana.

   ©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts