♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
69
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Banda Rabi'ah babu wanda ya lura da irin kallon da Yasseer ke yima Saude, Najib da Momie ma maganarsu suke hankalinsu baya wurin, tuni ta ɓata rai fuska a cusgune tace "Hniee ana gaidaka fa"
baimasan tana yi ba, tana ta mishi magana hankalinshi duk yana kan Saude, saida taje har inda yake ta taɓoshi sannan ya ɗauke idanunshi a rikice, "me...meya faru" ya tambayeta yana susar k'eya.
"gaisheka ake mana"
Ya k'ara kallon Saude da har lokacin idanunta ke a k'asa, "Lafiya lau ya gida?"
"Alhmdlh ya hanya?"
"ba gajia" duk a ɗan rikice yake maganar, muryarta da haɗuwar idanunsu ba k'aramin rikitashi yayi ba, ita dai bata wani ja maganar ba.
Jin bazai iya juya kanshi ba, yaja Najib suka bar ɗakin, yana tafiya yana lek'en Saude harya kusa yima k'ofa karo.
Ko kaɗan Yasseer bai gane Saude ba, shi dai Saudat ya gani, Najib ma farkon ganinshi da ita a Saudat ya kasa ganeta, ballantana Yasseer da kusan shekara biyar rabonshi da ita, a can k'auyen katsina ya barota tayaya zaiyi tunaninta a Abujama? Gashi tayi wani irin kyau da wayewa, maganarta ma kawai abun kallone, ga wani irin haɗaɗɗen murmushi, komai nata cikin wayewa da nutsuwa, ko a Moscow baiga kyakkyawa kamanta ba. Wani irin yanayi yakeji a kanta daga kallo ɗaya, yanayin da baisan ta yanda zai fassarashi ba(soyayyar gaskiyar kenan😄).
Koda suka zauna cin abincin dare, gaba ɗaya ya kasa ɗauke idanunshi a kanta, su duka sun kasa cin abinci sai juya cokali suke, shi ya kasa cin komai saboda baison daina kallon kyakkyaqar fuskarta, ita kuma kallon da yake mata duk ta tsargu, gaba ɗaya zaman wurin ya isheta jikinta ya bata ita kawai yake kallo, mik'ewa tayi kawai ba tare da taci wani abun kirki ba.
Momie tace "kar dai ki cemun kin k'oshi"
"wallahi kau Momie"
Najib ya mik'e yabi bayanta, a falo suka zauna.
"ki faɗamun gaskia kodai abincinnan bakijin daɗinshi in nemo miki wani?"
"A'ah na k'oshi fa"
"me kikaci da zaki k'oshi? Ina lura dake fa babu abinda kikaci"
"na k'oshinne fa, anma mezai hanani cin abinci"
"shikenan, dare yayi da munje amsar ɗinkuna"
"sai muje da safe ai"
Yasseer ne yazo wucewa, ya gansu zaune a falon yanajin Najib ya mishi magana anma ya share, wani haushi yakeji a ranshi ganinsu tare, hakanan yakejin kishin ganinshi da Saude, shi kanshi baisan dalili ba.
Wuri ya samu ya zauna a falon, kallo ya kunna ya koma nesa dasu anma hankalinshi na a kansu duk da ba saurarensu yake ba, wani irin bak'in ciki yake ji a zuciyarshi ganin yanda suke firarsu da nishaɗi, sai dariya suke, dariyan tata abin sha'awa, daga nesa yake hangen fararen hak'oranta.
Rabi'ah ce ta iskeshi, ita ta katse mishi tunani.
"Hniee gidan fa sai yaushe?"
A harzuk'e ya kalleta, "Biki kikazo ko ganin gida? Ki jira nan ayi hidiman biki dake"
Ta sassauta murya, "duka nazo, don Allah banijin daɗin halinnan daka koya na saurin faɗa, idan kuma baka da lokaci in faɗama Momie a haɗoni da driver"
Kallon sama da k'asa ya mata cikin k'unar zuciya, "kuma a haka zakije gidan?"
"A'ah zuwa nayi in tuna maka, bara in ɗauko mayafi"
Ba daɗewa tayima su Momie sallama ta fito, Anan suka bar su Saude har tana cewa "auntie kodai muyi rakiya?"
"A'ah waceni in wahalar da Amarya? Na yafe jibi zan dawo mu fara shagali ai"
"Tohm auntie saikun dawo" ganin ya tsaya tace "muje mana" ya tafi tabi bayanshi.
Yanda Yasseer yaga ranar haka yaga daren, ga tunanin Saude da kullum dare yake dawo mishi sabo fil, da kuma tunanin Saudat daya rufe ido suffarta ce ke dawo mishi, idan ya buɗe ido kyakkyawan murmushinta ne ke dawo mishi, Najib na gefenshi yana barci hankali kwance, anma shi tunani ya hanashi, duk yanda yaso daina tunaninta, hotanta ya kasa ɓacewa a zuciyarshi.
Meke shirin faruwa dani? Saudat fa matar k'anenah ce kuma ɗan uwana da muka shak'u sosai, wanda yake shirin aura nan da sati ɗaya. Meyasa zuciyatah zatamun haka? Kullum tana kamuwa da soyayyar abunda zan rasa.
Ina bazan taɓa rasa Saudat ba!, ya bama zuciyarshi amsa, Saudat MATATAH CE, dani ta dace, ya zama dole inyi wani abu kafin in rasata.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment