New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 64

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
              64

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Yasseer ya mik'a hannu zai amsa wayan kenan kiran Saude ya shigo a wayan Najib, murmushi yayi,
    "Halan ita ke maka waya?"
        "itace fa, Bara inje in amsa"
  "ai naga alama kam tunda kake murna, wani lokacin naga hotan"
   "tohm shknan bruz"
Falo Najib ya koma ya amsa kiran Saude, kusan raba dare sukai suna waya, lokacinda ya koma d'aki Yasseer har yayi barci, tunda safe kuma ya wuce k'yauyensu Saude.
   Tafiya mai nisa sosae yayi kafin ya isa k'yauyen, yasha bak'ar wahala sosai ga gajia da zaman mota, dak'yar ya iya gano gidansu Saude inda su kawu Ado suke, a waje ya tsaya aka mishi sallama dashi.
  Saiga Kawu ya fito yana washe baki, da sauri ya koma kawo mishi tabarma a soro ya shimfid'a mishi, sannan suka gaisa.
    "Sannu fa da zuwa Yaro"
        "Yauwah baba, baka ganeni ba ko?"
    "eeh tohh gaskia bangane ba"
  "Yasseer ne mijin Saude" ya fad'a yana sunne kai. Nan take Kawu Ado ya d'aure fuska.
    "toh toh, toh naji sai akai yaya?"
   "daman zuwa nayi inji kota dawo ko kuma an samu labarin inda take"
   "babu abunda ya shafemu da Saude da labarinta, tunda muka baka aurenta muka gama fita sha'aninta, yanzu wama yasan inda take? Oho! K'ilama tana can yawon karuwanci, ko kuma namun daji sun cinye namanta!"
   Cikin k'ara Yasseer yayi magana har saida ya tsorata kawu, "na rok'eka kawu karka danganta Saude da wannan maganganun naka"
   Kallonshi kawu yayi yana tab'e fuska, "da rayuwar Saude, da mutuwarta bata da wani banbanci a wurinmu, karka k'ara zo mana da maganar Saude, bamusan inda take ba, itama in tana da sauran hankali bazata nememu ba, don bazamu tab'a sonta ba"
    "zan koma, anma don Allah idanta dawo a sanar dani"
   Juya mishi baya kawu yayi bai k'ara cewa komi ba, ya zaro kud'i Aljihunshi masu yawa ya mik'a mishi, hannu ya zuro ya warce kamar yana tsoran karya maida, haka ko godia bai mishi ba harya tafi.

   En k'auyen ya shiga tambaga ko akwai wanda yasan inda Saude take, anma babu wani labari mai dad'i, gashi baba Haja bata cika zama k'yauyen ba daman babu wanda yasan takai Saude birni, har dare yana yawo k'auyen babu wani nasara.
   Duk ya gaji ga yunwa da kishirwa, sai da duhu yayi sannan ya hak'ura ya koma cikin gari, wani d'an k'aramin hotel ya kama ya kwana, washe gari ma ya koma k'auyen, babu dai labarin Saude haka ya hak'ura ya koma Abuja.

  Cikin wani irin yanayi ya isa gidansu, d'aga k'afa kawai yake anma baisan inda yake sakata ba, cikin sa'a babu kowa a falon, kai tsaye d'akinsu kawai ya wuce, kamar yanda ya zata Najib bainan, ya fad'a saman gado kawai dafe da kanshi.   Momie taji shigowarshi anma shiru bata ganshi ba, duk ta damu ta ganshi daman, kuma tunda taji shiru tasan ba lafiya ba, ta tashi ta nufi d'akin nasu.
   Yana zaune ya had'a kai da gwiwa, sautin shesshek'ar kukanshi ne kawai ke tashi, ta tsaya bak'in k'ofa tana kallonshi cikin mamaki da tashin hankali, kuka yake sosae yana dukan kanshi kamar wanda yaji sak'on mutuwa, a rikice Momie ta k'arasa shiga falon ta rirrik'e mishi hannuwa.
    "ki barni Momie, ki barni don Allah in hukunta kaina akan laifin dana aikata da har yanzu nake biyan bashinshi, qila hakan zaisa na rage zugin da zuciyatah kemun, Momie na aikata laifi, wallahi na aikata babban laifi a rayuwatah" ya k'arasa maganar yana fashewa da wani kukan.
    "Subhanallahi! Yasseer wane irin laifi ne wannan dake ma farin cikinka katsalandan? Fad'amun wanne irin laifi ne wannan da har ya sakaka zubda hawaye haka"
    "Bazan iya ba Momie, lokaci ya riga ya k'uremun, yanzu fad'a mikin baida wani amfani"
   "nifa mahaifiyarka ce, kana da wacce ta fini ne?"
   "babu Momie, shiyasa nakeso ki tayani da addu'ah, don Allah karki matsa saikinsan abunda ke damuna"
   "tohh shikenan, Allah ya yaye maka"
   "Ameen Momie, kaina ciwo yakemun sosai, jikina ko ina zafi, na rasa inda zan saka raina"
   "ka sauk'ak'a zuciyarka Yasseer, komai yayi zafi, ka dage da Addu'ah, bara inma Najib waya yazo muje Asibiti"
   "A'ah zanji sauk'i Insha Allah Momie basai munje ba"
   "Tohh kasha magani dai, saika kwanta ka huta, zuwa anjima in bai bari ba sai muje asibitin"
   "tohm Momie" dak'yar yake magana, hawaye kawai ke fita a fuskarshi, saida ta tabbatar ta d'an kwantar mishi da hankali sannan ta fita ta barshi.

    Tana fitowa saiga Najib da Saudat sun shigo, sun dawo daga wurin k'unshi da gyaran gashi, ta taresu tanama Saude sannu da zuwa, har k'asa ta gaishe da Momie.
    "Ya gajiyan hidima, ya Auntynki?"
   "lafiya lau take, tace a gaisheku" taci gaba da wasa da yatsunta su duka sunyi shiru, sai Najib ne ya fad'ama "wai sannu da zuwa mukazo tayima bruz, munyi waya dashi yace yana hanya"
    "Ayyah! Aikam bai dad'e da dawowa ba, baijin dad'i ya d'an kwanta ya huta"
    "Allah sarki, Allah ya sauwak'e"
     "Ameen"
   Tsarabar Husna ta had'a mata, da kuma nata duk da bada sunanta aka siyo ba, tayi godia sosae, basu dad'e ba suka tafi don zata fara aiki, gashi daren Sallah, Momie tana ta sa mata albarka.
    Suna fita Yasseer ya fito da shirin zuwa Masallaci, jikinshi duk ba k'wari daka ganshi yana cikin damuwa.

Bayan Sallah da kwana biyu, Yasseer da Rabiah sukaje gidan Husna bankwana sun kusa komawa, tunda yazo bai ganta ba ko sallah bata iya zuwa gida ba, kamar tayi me don murna da ganinshi.
   Saude na kitchen ita da Najib, don har gidan Husna ma ko yaushe suna tare, cewa yake bai damu gidan k'anwarshi bane, ko ina yake Saudat kawai yake gani, kuma bazaiso tasha wahala ba.
   Yana jinsu ya fita falon, suka fara mishi tsiyar yanzu har aiki yakema Husna kawai don Saude na gidan.
   "ai ba don ita nake ba, Saudat nake tayawa, idan kuma aka matsa in d'auke matata mu tafi"
    Rabi'ah tace "lallai mai Matah"
   "eeh Aunty MATATAH CE Saudat, laifine don na fad'i?"
   "A'ah mamakin yanda so ya canjaka nake, kamar ba Yaya Najib d'in da ko Motsa baki wahala yake mishi ba"
   "Da kenan Matar Yayanmu"
   Husna tace "Ai kad'an kikaji indai labarin soyayyar Najib da Saudat ne"
   Yasseer na gefe sai faman duba Agogo yake, ta rik'o hannunshi, "badai tafiya ba?" ya d'aga mata kai, "kinsan dai sauri nake" a gabansu ta marairaice fuska kamar zata fad'a mishi, "nidai ka bari muyi yinin tare, saimu tafi"
  "Zan dawo d'aukarki, nima ban gama gaisawa da sista ba"

  Husna tace "Munata fira ma Yayanmu ko ruwa bakasha ba, bara a kawo muku" ta k'wala ma Saude kira, "Aunty Saudat, a kawoma su Yayanmu drinks" Najib ya mik'e, "yanzu wannan d'inma ita zaki saka?"
     "Nikam dai Allah ya bani lafiya in huta da fad'a, ni don su gaisa da Yayan ma nasan itama har yau basu had'u ba"
   A hanyar fitowa suka had'u da Saude, ya ansa na hannunta sannan ya juya yakai musu, ruwan roba kawai Yasseer ya d'auka, "ba'a k'inshan ruwan zumunci anma a k'oshe nake"
    "Ai nasan Auntyna bata wasa da bama Yayana Abinci"
   "kamar tafiya zakayi, ka jira Saudat tazo ku gaisa plz"
  "Sauri nake, idanna dawo ma gaisa" suka fita da Najib ya rakashi, yana fita Saudat ta fito da kulolin Abinci.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 21-22[15:10, 4/17/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts