[11:54pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page5⃣
Har k`asa Deezee ta duk`a ta gaishe da kerry,
"Thank you" kawai ta fad`a tare da zama bakin gado.
"Can I start?" Kerry ta tambaye ta cikin ladabi kamar tana magana da babarta.
"Yes you can, ina son makeover na kirki wanda baki tab`a yiwa kowa ko mai kama dashi ba, zan baki naira dubu hamsin idan kika min na kirki, pink, ash and black ne za`a had`a",
deezee lashe money😜 tuni ta fara rawar jiki da fara`a taji zancen kud`i, "fara saka kayan dan kar ayi kuma wurin sakawa a b`ata wani abu",
"Good idea" kerry ta fad`a tare da zira had`ad`d`iyar rigar a jikin ta.
Nan suka hau makeup baji ba gani, abunka ga mutun kyakkyawa dama, babu kwalliyar ma tayi kyau ina ga Deezee makeover ta mata.
*Karfe 4:45pm*
*~Gidan su Afnan.~*
Bayan ta gama kwalliyar ta duka ta saka kayan ta d`aura after dress akai, nan fa ta fara tunanin yanda zata fita, gashi kuma ta fad`awa Momy bata da lafiya d`azu,
D`aukar wayar ta tayi ta kira MD, bugu d`aya kuwa ya d`aga,
"MD ba kanta fa" ta fad`a bayan ta koma kan gadon ta.
"Me ya faru ne `yan mata?",
"Na rasa kalar k`aryar da zanyi in bar gida fa, gashi nama momy k`aryan banda lafiya da safe dan kar inje islamiya„ ka bani idea pls".
Shiru yayi na wani lokaci kafin yace "to fa! Bari zan kira ki yanzu".
Tsinke wayar yayi ya fara tunanin kalar k`aryar da Afnan zatama momy, "yess" ya fad`a a lokacin da wani tunani yazo masa, kiran wayar ta yayi ringing d`aya ta d`auka,
"MB ya?" Ta fad`a rud`e.
"Idan kinyi kwalliya ki goge ta, ki nemi after dress ki d`ora hijabi a kanta, ki k`irk`iri kukan k`arya sosai kice baban su Esee ya mutu, yanzu aka kira ki aka fad`a miki shine kike so kje, idan tayi insisting zata biki jana`izar sai kisan yanda zakiyi ki hana ta",
sosai taji dad`in wannan shawarar, "saisa nake sonka MD, a duk *Arewa Stars* kafi kowa brain mai kyau", daga nan ta tsinke wayar tana mai jn dad`in shawarar da MD ya bata.
*karfe 4:50pm*
*~Gidan su Feenat.~*
Ummah ce zaune akan sallayar ta tunda ta gama sallar la`asar take zaune tana ta lazumi, a hankali Feenat ta fito cike da tsoro ta duka har k`asa, ta kasa fad`in komai jikin ta sai rawa yake, har a ranta tayi nadamar shigar ta group d`in *Arewa stars* sai dai kuma duk wanda ya shiga baya fita kuma tasan haka, tausayin ummanta take sosai yanda take k|ok`arin tarbiyyantar da ita ba dare ba rana.
Ganin Feenat ta zauna kusa da ita kuma tayi shiru yasa ta ajiye casbahar hannun ta tace "Safeena ya akayi ne? Knzo kin tasa ni gaba kuma kin kasa fad`in komai",
Da k`yar ta iya furta "ummah d`azu bayan tafiyar Afnan ta koma gida ne ta kira ni wai an kwantar da momy`n ta asibiti, bata da lafiya sosai dan aiki ma za`a mata gobe,shine nake son naje ganin ta",
"Ashsha kuwa abu bayyi dad`i ba, ya kamata kam ki hanzarta ki gano ta, ki gaishe min da ita sosai" ta ciro d`ari uku daga jikar ta ta mik`ama Feenat tace "ki sai mata kayan marmari da wannan ki kai mata, wannan d`ari biyun kuma sai ki hau napep dashi" ta sake mik`a mata wasu kud`in.
Wasu irin hawaye suka fara ma Feenat ambaliya, sosai ta k`ara jin tausayin ummanta, me yasa ta zab`i wannan rayuwar fiye da farin cikin ummanta? Tunanin da take kenan a ranta,
"Tou ki daina kukan mana Feenat insha Allahu zata samu lafiya, ki tafi ki kula da kanki kiji tsoron Allah kuma", duk lokacin da Feenat zata tafi wani wuri ko makaranta ne sai ummanta tace mata taji tsoron Allah, takan yawan tuno da wannan maganar a duk lokacin da zata je wani party.
Amrah and Rerbee`art sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[12:00am, 20/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page6⃣
*Karfe 4:56pm*
*~Gidan su Afnan.~*
Tuni Afnan ta k`wak`ulo hawayen dole tana mitsitstsikar ido kamar da gaske, ba wuya kuwa idon ta yayi jajir, da gudu ta fita parlor tana kiran "momy! Momy!!",
Momy`n na daga d`akin ta tace "gani a d`aki na Afnan, lafiya!?"
"Ba lafiya ba momy" ta k`ariso d`akin tana ta sauke ajiyar zuciya kamar da gaske.
Momy tace "lafiya? Me ya faru?"
"Momy baban su Ihsan Abdallah ne ya rasu yanzun nan ta kira ni, bama a kawo gawar sa ba wai sai gobe da yake hatsarin jirgin sama ne sukayi",
Momy ta dafe k`irjin ta tace "mun shiga uku! Allah sarki na tausaya masu, yanzu shikenan sun zama marayu, in ko haka ne barin saka hijabi na sai mu tafi tare",
Saurin katse ta Afnan tayi tace "noo momy ki zauna kawai tunda ba`a kawo gawar saba, nasan sai zuwa gobe za`ayi jana`izar shi kinga sai kije goben, yanzu zanje inta bata hak`uri dan nasan yanzu tana can tana kuka",
"To ba damuwa Afnan, Allah ya mashi rahama, idan ta kama ma sai ki kwana acan tunda mutuwa ta kauda komai",
Sosai Afnan taji dad`i amma a zahiri ta nunar da wannan mutuwar ta tab`a ta sosai.
*Karfe 4:58pm*
*~Gudan su Ruky.~*
"Mamy har na shirya kin ganni nayi kyau?", Ruky ta fad`a tana wani jujjuyawa a gaban Mamy`n su.
"Kinyi kyau sosai auta na, ina mai tabbatar miki da yau sai kinfi kowa haskawa a gurin, su o'e da ba`a waye ba kuma a haka za`a k`are fad`in Allah yace annabi yace kamar kansu farau musulunci" ta k`arisa maganar tana kallon Rumaysah, itakam ko a jikin ta, dan tasan duk da tsanar da mamy ke gwada mata saboda bata halayen banza bazai hana ta samun mijin kirki ba, kullun tana ma mamy da k`anwar ta addu`ar shiriya dan wannan hanyar da suka d`auka hanyar kirki sam ba hanyar kirki bace.
Key`n motar mamy ta d`auka sannan ta fice, nan ta kira Triple A ya fad`a mata a inda za`ayi.
*Karfe 4:59pm*
*~Gidan su Iby.~*
har a wannan lokacin Iby na zaune ya rasa yanda zayyi ya d`auki d`aya daga cikin motar yayan sa, ganin yake girma ya fad`i idan ya hau mashin ya tafi, barin kuma a dam d`in Ajiwa za`ayi party`n ba cikin gari ba, sand`a yayi a hankali ya shiga d`akin Mukhtar, ya samu baya nan tunda ya tafi masallaci bai dawo ba, makullin camry CE ya d`auka cike da murna ya tafi.
*
*Karfe 5:15pm.*
*_~AJIWA DAM~_*
A daidai wannan lokaci ne kowa ya hallara a bakin ruwan ajiwa, an k`awata gefen ruwan da kyakyawan decoration, abunda yafi komai kyau a wurin shine yanda kowa ya saka kaya ash, pink and black, ga wani sauti da yake tashi a hankali a hankali, Kerry uwar birthday kuma tana cikin mota bata fito ba har sai DJ ya gano wak`ar da zata shigo da ita.
Muje zuwa (inji Asea Bashir),
This is just the beggining.
Amrah nd Rerbeeart sk novels.
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
0 comments:
Post a Comment