New Post

Monday, 7 November 2016

HAKA SO YAKE 13-14

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_13 -14_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Bayan wasu 'yan mintina kad'an ta d'ago kanta, sannan tashare hawayenta,
Jikinta ba kwari tafita daga falon, tanufi d'akin momy, bayan takarasa d'akin, momy da abdul tatarar zaune suna kallo,
Sukuku takarasa bakin kujera tazauna, momy ta dubeta, taga yanayin fuskarta ya chanza "subeen dady menene, ko yayan nakine yataba ki" momy tafad'a tana murmushi
Subeey takara d'aure fuska, a lokacin tad'ago edonta ta dube momy tace " a a momy bakomai"

Momy tace "bakomai amma kike cikin damuwa, nifa banason zurfin cikin nan naki, momy tad'an sauke murya tace "haba subeen dady fad'amun menene"

Wasa take da yatsunta domin duk jikinta yad'au rawa tarasa ta yadda zata yiwa momy bayani, edonta duk sun cinciko da kwalla, cike da inda2 tasoma magana "amm damanm...momy.."

Abdul dake zaune duk ransa yabace, akan maganar datake, mikewa tsaye yayi, yaja tsaki, sannan ya dube subeey yace "kada kiyi wahalar sanar da ita komai,  domin fad'a matan dazakiyi  bazai amfana miki komaiba.." yana gama fad'a yafice yabar d'akin,
Mamaki yacika momy, akan maganar da abdul yafad'a,
Subeey kuwa tuni hawaye suka soma ambaliya akan fuskarta, amma takasa kuka, ta sunkuyar dakanta kasa,,,

Bayan yabar falon d'akin momy ta dube subeey cike da mamaki " kewai meyake faruwane, nifa duk kun sakani a duhu"

Kanta a sunkuye takasa dago kanta ta kalle momy,

Momy takara cewa "Subeey dakefa nake magan kinyi shiru meke faruwane"

Muryata narawa tasoma fad'an "bakomai mo...." bata karasa maganar ba kuka ya kube mata, da sauri ta mike ta toshe bakinta, da gude tafita daga d'akin ta nufi d'akinta,

Cike da mamaki momy take kallonta kifar dan bayan tabar d'akin, a hankali momy ta furta "ikon Allah, daga magana sai kuka"
Sauke nunfashi tayi, itama takasa samun sukuni, Dole tamike tabi bayan subeey,

Subeey nashiga dakin ta sake bakinta tafashe da kuka, tafad'a kan gado cike dajin zafin abinda ta aikata, da tasan hakan abdul zai mata dabata furta masa wannan kallamarba, da tasan hakan zai kawo sabani a tsakaninsu da ta bawa zuciyarta hakuri, koda kuwa hakan zai iya illatata,
A hankali taji anturo kofar d'akinta, ko d'ago kanta batayiba kawai taci gaba da kukanta,

Momy takaraso kusa da ita tazauna, tad'an tsaya tana kallonta nadan wani lokacin kafin tasa hannu tad'ago, tasaka jikinta, tana shafar bayanta,

A hankali take rage sautin kukan datake, momy tana shafar bayanta har tadaina kuka, sautin shanshekar kukanta kawai kakeji, cikin sanyi murya momy tace " subeey kifad'amun meke faruwane tsakaninki da yayanki, laifi yamiki ne"  Subeey ta girgiza kai, tana harbar majina tace " a a momy, nice namasa laifi"
    Momy tasauke nunfashi tace "laifinme kikayi masa "
Saida Subeey tafito daga jikin momy sannan tashare hawayenta tace " momy wannan laifin banawa bane laifin zuciyatane, dahar..." sai kuma takasa karasa maganar, tana shirin yin kuka,
Momy tayi saurin dakatar da ita dacewa "relax subeey, nafahimci bakison fad'amin laifin nan, nibazan takuraki ba, amma inaso kisani, komai girman laifi, yanada mafita da za'a iya neman gafarar wanda akayiwa laifi, dan haka kije kibashi hakuri"

Tana shanshekar kuka tace "toh momy" Momy tace "kije yanzu yana d'akinsa"

Kai kawai Subeey ta girgiza mata sannan tatashi, tafita tabar d'akin, a zaune tabar momy saman gado,

Bakin kofar d'akinsa tazota tsaya zuciyarta na duka tara2, ta tura kofar d'akin tashiga, sallama tayi cikin sanyi murya, yana kwance akan gado yayi sauri mikewa, edonsa sunyi ja sosai, ya kura mata edo,
Suna hada edo tasauke kanta tana hawaye tace "yaya abdul kayi...."
Cikin tsawa yad'aga mata hannu, "banason jin komai daga bakinki, meye amfanin zamana dake tunda har zaki iya sha'awar zama matata, nina daukeki amatsayin kanwata jini daya uwa daya uba daya, ko a mafarki banyi tunanin kalmar so zata fito daga bakinkiba, meye amfanin zuciyarki dahar tayi wannan mummunan sakaci nafadawa  son wanda baya sonta, wlh badan inajin tausayin kiba dasai nace tir da wannan rayuwar taki tunda har zaki iya ganin sha'awar yayanki"

Tunda yafara maganar subeey take kuka, duk taji tatsani kanta, why meyasa zuciyarta tamata hakan, da kyar ta iya tsayar da kukanta tad'ago kanta takara dubansa sannan tace "yaya abdul..." bata karasa maganar ba yakara dakatar da ita dacewa "banason jin kalamanki kibarni na huta, banajin zan iya saurarenki a yanzu, kije idan na huce kya dawo, kifita daga d'akin nan" yanuna mata kofar fita,

Tana shanshekar kuka tajuya tafice tabar d'akin,
Tana fita yaja tsaki "rubbish girl, ko narasa mai sona  a duniya ke zan sokine mai edo d'aya, mstw, " ransa abace ya koma kwance, zuciyarsa cike da takaicin subeey..

Via OHW📚📲

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 1-20[10:36, 3/9/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 1-10 Kishingide take saman lumtsumemiyar kujerarta 2seater da remote a hannunta! Masu aiki nata yi mata hidima, daya dga… Read More
  • MAKASHINKA 65-66```MAKASHINKA...```           65-66 ©Rabiatu sk msh ƘARSHE Sadeey Sai zagaye ɗakin take cikin fargaba, a zuciyarta kuma addu'ar samun nasara kawai take, kasa haƙ… Read More
  • MAKASHINKA 63-64```MAKASHINKA...```           63-64 ©Rabiatu sk msh Damuwah ta ƙara yima sadeey yawa, kwana ukku ta ina zata samu hujjojin da kotu zata gamsu baida laifi? Ya Anwar ta kir… Read More
  • MAKASHINKA 59-60```MAKASHINKA...```            59-60 ©Rabiatu sk msh Tana shiga ta tada mota ta tafi, shamsuddeen ya duƙar da kanshi yana hawaye, shin wai meke faruwa dashi ne?meyas… Read More
  • MAKASHINKA 61-62```MAKASHINKA...```           61-62 Washe gari... Aka mik'a shamsuddeen a gaban kotu, *A KOTU* An cika a kotun kowa yana jiran yaji ya wannan shari'ar zata kasance, Bayan alkali y… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts