New Post

Wednesday, 16 November 2016

HAKA SO YAKE 25-26

💕💕  *HAKA SO YAKE* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_25 - 26_* 💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Subeey tana rik'e da wayarta dai dai number Ahmad take kallo, ita kaɗai take murmushi tana tuna maganganunshi, Duk da babu sauran wuri a zuciyarta da zata iya saka soyayyar wani ɗa namiji a ciki, Ahmad yayi matuk'ar burgeta har take jin zata iya aminta dashi tunda bazata taɓa samun muradin zuciyarta ba.

Kamar ya sanda tunaninshi take, tare da jiran kiranshi, sai gashi ya kirata sunanshi raɗam akan screen ɗin wayarta,

Tayi jim tana kallon screen d'in zuciyarta cike da wasu-wasi tohh idan ta ɗauka me zata ce mishi? Kunyarshi ce ta lulluɓe ta edanta tuna yanda ta bashi numbarta daga tambaya,

A zuci tace " anya idanta ɗauka kiran bata zubda ajinta ba? Wata zuciyar tace "ay kin gama zubdashi kam tunda kika bashi numba" har kiran ya katse bata gama yanke shawara ba.

Cikin fargaba Ahmad yak'ara danna mata wani kiran, wayar nata ringing harya fara fidda ran da zata ɗauka, ta ɗaga kiran tare dayin sallama cikin siririyar murya mai zak'i, sai da ya lumshe ido ya buɗe sannan ya amsa shima ciki zazzaƙar murya.

Shiru sukayi gaba ɗayansu, tare kuma suka buɗe baki tace "Ya kake?" shima Yace "kina lafiya?", dariya sukayi gaba sannan suka gaisa, wani shirun ya k'ara biyowa baya.

Kowannesu sai sak'e-sak'e yake a zuciyarshi, babu wanda yayi magana sai can Ahmad yayi magana cikin zolaya "Sunana Subeey" dariya ya bama subeey sosae tace "Sunanka Ahmad ne, da Alama ka rasa Abin cewa ne kake nemar yimin k'wacen suna"

Yayi dariya Yace "Ay sunan naki ne mai daɗi subeey" tayi 'yar dariya sannan tayi shiru, su duka suka rasa abin cewa.

Ahmadne yak'ara cewa "ba tambayoyin da kikeso kiyimin?" tace "kamar wanne?" Yace "ko Abnda kikeson sani game dani" Tace "ka faɗamin duk abnda ya kamata in sani" Yace "kedai Ki tambayi abnda kikeson sani" Tace "tohh A'ah ba komi," Yace "kiyi tunani"

Tace "Tohh Zan tambayeka, Anma 20secs in baka bada Amsa ba shikenan" Yace "Na yarda"

Tace "Abincin Zamani kona gargajiya?
        "Na gargajiya"
Tace "best colour?
          "skye blue
Tace "Manyan kaya ko k'anana?
         "K'anana"
Tace "indian films ko American?
         "indian"
Tace "farar mace ko ba'ka?
           Yace  "subeey"..

Via OHW 📚

Related Posts:

  • MATATAH CE 36-40♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            36-40 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 36-40♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            36-40 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 31-35♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            31-35 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 26-30♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡           26-30 ©Rabiatu sk msh       ®NWA    &nb… Read More
  • MATATAH CE 41-45♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            41-45 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts