[11:35pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page3⃣
*Karfe 1:30pm*
*~Gidan su Iby.~*
"Yaya Mukhtar dan Allah zaka bani aron motar ka anjima?",
"Me zakayi da ita?" Yayan nashi ya fad`a yana latsar system nashi.
"Yaya zanje wani wuri ne?"
"Shi wurin baya da suna ne?"
"yana da suna yaya, ganin abokina zanje",
"Ganin abokin ka kuma shine bazaka iya d`aukar mashin d`in ka kaje ba dole sai a mota?", yayan nasa ya fad`a a lokacin da ya dawo da kallon shi ga Iby.
"yaya wai me yasa kake min haka ne? Yaya na yana da kud`i ina alfahari da hakan amma kuma baya kyautata min, me yasa yaya bazaka so aga k`anin ka da manyan harkoki bane wai?",
Cikin mamaki Mukhtar ya kalli Iby yace "au! Ashe abun ma hakane, tou tunda hakane ma bazan bayar ba, kaje ka nemi loud speaker kayi shela akan nak`i ara maka mota ta kuma bayan ina da motocin da yawa, sai inga idan akwai wanda ya isa yamin wani abu",
Tashi Iby yayi yana gunguni can k`asa k`asa,
"Me kake fad`i!?" Mukhtar ya fad`a a hayak`e.
"B..b...bance komai bafa yaya" ya fad`a in tammered.
*Karfe 2:30pm*
*~Gidan su Shareef da Shareefat.~*
Shareefat ce kwance kan doguwar kujera ta rasa abunda yake mata dad`i dan tunanin rashin kayan da zasu saka wurin party`n kerry, alamar tafiya taji tayi saurin duba ko waye, ganin Shareef ne yasata ajiye nannauyan ajiyar zuciya tare da fad`in "Reesha dama ina jiran zuwan ka",
"Menene?" Ya fad`a yana kallon ta,
"Mubar area`n nan dan kar mamy taji mu",
Barin parlor`n sukayi suka koma can kusa da gate d`in gidan,
"reesha dama in fad`a maka wallahi banda kayan sakawa anjima, nasan kuma kai kana dasu, ya za`ayi dan Allah",
Dariya yayi sosai yanayi yana nuna ta da yatsa, sai da yayi mai isarshi lokacin har Shareefat ta k`ule,
"Tou Reeshat ni yanzu me zan miki? Kije kiyi aro kawai",
K`ara b`ata fuska tayi tace "ai wallahi inda akwai inda zanyi aron da nayi, dan bazan yarda kowa da anko ni banda shi ba",
Shareef yace "kar ki damu zan nemo miki shi yanzu, amma fa ban iya zab`e ba zakiyi hakuri da duk wadda na siyo miki?",
Kallon shi tayi sosai tace "kai Reesha ka tafi dani dan Allah",
Zaro ido yayi yace "idan na fita dake yanzu anjima idan zamu fita k`aryar me zan ma mamy? Kedai kiyi hak`uri kawai zan duba miki mai kyau, kuma koya take indai kalar ta hau ai shikenan",
"Ehh haka ne kuma, Reesha, pls nidai mai kyau nake so", da wannan maganar Shareef ya tafi, shareefat kuma ta koma cikin gida.
Amrah and Rerbeeart sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:45pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page4⃣
Haka dai gidajen su *Arewa stars* d`in suka kasance, kowa ya nemi kalar kayan da da suka zab`i sakawa a birthday party`n kerry d`aya daga cikin members na *Arewa Stars,* murna fal a zukatan su, sun d`au dogon lokaci suna tsumayen wannan ranar duk da yawan party da suke amma na kerry ya banbanta saboda asalin ta ba tashin Nigeria bace a America ta tashi, tasan duk wani salo na wayewa da gayu, sannan kuma iyayen tama suna bakin k`ok`arin su ganin sun mata duk abunda take so, yanzu ma haka bata k`asar ta tafi Dubai inda za`a d`inka mata rigar da zata saka yau wurin birthday party`n ta kuma a yanzu suke sa ran isowar ta saboda gashi rana har tayi.
*K`arfe 3:20pm* yayi daidai da dirar jirgin su Kerry a babbar airport d`in aminu Kano dake cikin jihar kano, jikin ta har rawa yake taga ta fito daga jirgin dan bata san tsawon lokacin da zasu d`auka a mota basu isa katsina ba, gashi kuma bata son African time a harkar ta.
Da sauri ta fito daga jirgin ta fara hangen inda zata ga Dad nata, da sa`a kuwa can ta hange shi sanye da suit black and white yana kalle kallen ta inda zaiga fitowar tilon `yar sa.
Da gudu ta iso gaban shi tare da hugging nashi sosai kamar mata ta rungumi mijin ta,
"Welcome back my daughter" Dad d`in nata ya fad`a bayan ta sake shi yana mata murmushi.
"Thank you Dad, amma ya kamata muyi sauri Dad, kaga time is going friends d`ina har sun fara shiri I know",
"Ok lets go dear" ya fad`a suka kama hanyar fita.
Gaban parking area naga sun nufi wata had`ad`d`iyar corolla s fara tas, tun daga nesa ya latsa remote motar ta bud`e kanta, gaban motar Kerry ta zauna bayan ta zauna ya rufe mata k`ofar sannan shima ya shiga ya rufe tashi k`ofar. Da k`arfi yaja motar jin autar shi tace suyi sauri su isa katsina.
"I missed youh so much my Dad, tafiyar kwana biyar amma ji nake kamar nayi one year ban ganku ba",
"Muma munyi kewar ki my Kerry, musamman ma Mum inki kamar zata min kuka wai sai ta biki, sai da nata bata baki sannan ta hak`ura"
"Dad pls ka k`ara gudun nan bai fa ishe ni ba"
Gudun ya k`ara sosai kamar mai shirin tashi sama, ba dan komai ba sai dan yaga ya farantama Kerry rai.
*Karfe 4:34pm*
A wannan lokaci ne su Kerry suka iso garin Katsina, sai a lokacin kuma ta kunna wayar ta, nan taci karo da sak`onni sosai na *Arewa Stars* wanda suka neme ta a waya basu same taba, suna son jin kota dawo dan kar suita wahalar shiri bayan kuma bata dawo ba.
Data ta kunna ta shiga watsapp,
*Arewa Stars* taci karo dashi a farko, nan taci karo da conversations da yawa duk suna magana ne akan jin ta shiru da akayi bayan kuma sun gama plans d`in komai da zai wakana a gurin.
Guntun murmushi tayi sannan ta rubuta
"Kar ku damu *Arewa Stars Allah ya min dawowa kuci gaba da shirin ku daga inda kuka tsaya, birthday party na dole sai anyi shi babu gudu ba ja da baya.*
Nan suka hau replying na dad`in da sukaji, sauka tayi daga watsapp d`in ta kira Deezee makeover akan tana son ganin ta yanzu sannan ta shiga wanka.
bata wani b`ata lokaci ba sai gata ta fito daga wankan.
Trolly bag d`in da ta dawo dashi ta bud`e ta ciro wata riga, "shantalin uwar nan kai" sis Rabi`ah ta fad`a a lokacin data kalli rigar, ni kam uwar gayyar kasa fad`in komai nayi saboda tsantsar kyawun ta.
Doguwar riga ce irin mai bin jikin nan, an tsaga gefe gefen ta, complete pink ce rigar arm less, an k`awata ta da wasu irin manyan stones masu walk`iya tamkar zinari, wuyan ta kuma V neck ne inda aka zagaye shi da sirfani da stones a jiki, a daidai k`irjin rigar kuma anyi wani rubutu da stones din an rubuta *"AM PLUS 1",* Sannan aka zagaye rubutun da zanen flower daya k`ara k`awata rubutun, daga bayan rigar tayi nan ma naga an rubuta *"IT`S KERRY"* shima an k`awata shi kamar yanda akayi ma na gaban, "tir k`ashi!" Kawai na iya furtawa, ba komai na fad`a maku akan kyawun rigar ba, idan nace sai na zayyane maku yanda take duka tou za`a ci 10 pages ne, just close your eyes ku hango yanda rigar take (lol..).
Da gudu wata budurwa ta shigo wadda da ganin ta an san `yar aiki ce, fad`i k`asa tayi cike da girmamawa kanta sunkuye alamar tana son yin magana amma sai an bata izini sannan zatayi.
"Go on" kerry ta fad`a cike da raini.
"Ma You have a visitor",
"Let her in" ta fad`a a tak`aice.
Kamar yanda ta shigo d`in haka ta fita, tsaki Kerry tayi a bayyane wanda yayi daidai da shigowar Deezee.
Amrah and Rerbee`art sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
0 comments:
Post a Comment