💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣5⃣
*NOTE:-* *kuyi hak'uri na rashin jin mu kwana biyu, hakan ya faru ne na rashin isasshen time, tests nake sosai ga kuma exam muna facing, am in need of your prayers fans, love youh all.*
**************
A mota d'aya suka d'unguma suka tafi, sai momy, ummah, mami da kuma Feenat driver ya tafi dasu,
Sosai suke gudu nan da nan sai gasu a Ajiwa, a bakin dam d'in sukaje tare da barin fitilun gurin a kunne saboda duhun dake akwai.
Sosai suka razana ganin yaran su a babbaje k'asa kamar marasa gata,
Wasun su kuka kawai suke dan babu alamar rai a tare dasu musamman ma wanda suka hango can gefen ruwa babu k'afa d'aya.
Feenat kuwa jikin ta sai rawa yake dan kar wannan halittar ta dawo dan tana matuk'ar tsoron ta, ta k'ank'ame ummanta sosai tana kuka tana k'ara tuno da yanda aka ringa illata mata abokai.
Alhaji Ma'aruf yaci gaba da dube duben inda zai hango yaran shi, daga can nesa ya hangi Reeshat k'ank'ame da MD duk kansu babu alamar numfashi, wata irin k'ara ya saki cike da tashin hankali, da k'arfi yace "idan ba tsoro ba ki fito mana! Wallahi sai na kashe ki in har yara na suka mutu, ki bayyana kanki inji wanene ubanki a k'asar nan!" Yana kaiwa nan yaci gaba da kukan shi kamar k'aramin yaro.
Su kuwa sauran suka hau bincikar yaran su,
Nan da nan kowa ya gano yaron shi amma fa duk kanwar ja ce saboda babu alamar rayuwa a tare dasu.
Sauran da babu iyayen su kuwa nan aka barsu babu galihu,
A hankali suka fara jin wata k'ara mai had'e da guguwa tana dosowa inda suke,
Sosai hankulan su suka tashi musamman yanda sukaji k'arar tana k'ara tinkaro su, ga wani irin haske daya bayyana a wurin,
Cike da tashin hankali suke kallon al'amarin,
Feenat kuka sosai take tace "ummah gata nan, ta dawo zata kashe ni, dan Allah kice mata tayi hak'uri ta koma"
Ummah ta rungume ta tace "ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu babu abunda zata miki, kici gaba da addu'ah kawai kar ki daina, kar kuma tsoro ya hana ki yi kinji?",
Kai kawai ta gyad'a mata idon ta kyam akan guguwar dake nan dunk'ulewa wuri d'aya.
Dady ya rungume momy yana fad'in "mun shiga uku! Ga Afnan bata numfashi kuma ga wannan al'amarin, mu gudu kawai mu kai 'yar mu asibiti dan tabbatar da ko tana da rai",
Cikin tashin hankali momy tace "insha Allahu ma tana raye, Alhaji ban san ya zanyi ba idan na rasa Afnan, itace 'yar budurwar da nake tak'ama da ita gashi mahaifata ta lalace" ta k'ara fashewa da kuka.
Dady yace "ki daina kukan nan kina k'ara tayar min da hankali ne, mu tafi abun mu kawai tunda dama da mota ta muka zo",
Daidai sunbi hanya zasu tafi kenan wannan guguwar ta tare su, da k'arfi iska ya ringa dawo dasu cikin mutane, duk k'ok'arin da suke na tafiya amma dawo dasu iskan yakeyi, ga Afnan dauk'e a hannun Dady, momy kuma ta rik'e shi tam saboda tsabar tsoro, tunda uwar data haife ta bata tab'a shiga tashin hankali irin wannan ba,
Dole basu dan yanda zasuyi suka tsaya cikin mutanen, shi kanshi Dady'n k'arfin hali ne kawai ya hana shi yin kuka,
Dan kuwa Alhaji Bashir yanayin daya ga Nuratun shi ciki dole shima ya shiga tashin hankalin, kuka yake sosai kamar k'aramin yaro, ga wata irin k'ara data sa babu mai jin wani idan yayi magana.
A hankali guguwar ta dunk'ule wuri d'aya inda ta koma wasu irin k'anana k'ananan halittu bak'ak'e wulik, exact abunda ya faru a baya yanxu ma shine, haka suka ringa cin junan su har suka zama babbar halitta guda d'aya.
Feenat na gani ta tabbatar da wannan halittar ce, nan da nan hankalin ta ya k'ara tashi tana k'ara tuno baya, "tou wai ma me ya dawo dani bayan ta sallame ni? Babu fa wanda yace mu bisu mune kawai mukayi niyya" maganar data ringayi a ranta kenan.
Da k'arfi halittar tayi wata irin k'ara wadda sai da komai na wurin ya jijjiga, mutanen wurin kuwa wasu suka ringayin sama da k'asa, basu samu daidaituwa ba har sai da ta tsaya da wannan k'arar ta fuskance su baki d'aya tana k'ok'arin yin magana.
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
0 comments:
Post a Comment