💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_3 - 4_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Tajima tana kukan kafin tajuya takoma saman gado tazauna,
Filo ta janyo ta rufe fuskarta, sai kuma taci gaba da kukanta,
Da karfi taji anturo kofar d'akinta, tayi sauri ta share hawayenta,
Abdul ne yashigo da gudu yafad'o saman gadon datake zaune, yana dariya cike da nishadi yanuna mata wayarsa "kinga koh mutane dadama sunyi liking wannan video, kuma sunyi comments sosai, duba kiga mesukace"
Subeey Tayi saurin kirkirar murmushi, sannan takarbi wayar tana dubawa, da gaskine kuwa taga anyi comments sosai, daga cikin wad'anda sukayi comments taga wani yace "wow amma dai yarinyar ta had'u saidai matsalarta d'ayace, edon nan nata dabatada lafiya, da edon kalau yake, da wannan ko a India albarka" kafin takarasa karantawa Kwalla suka cinciko mata edo kiris take jira tafashe da kuka, sai kuma tayi karfin hali ta mayar da kukan,
Ta mika masa wayar tace " nagani"
Abdul Yana dariya yace "to me kika ce "
Mikewa tsaye tayi tana kokarin fita tace " duk abinda kaga yadace shinace "
Abdul yadube, sai a alokacin ya lura da irin yanayin datake ciki,
Tsayar da dariyarsa yayi yan cewa " subeey miye, meya faru da edonki naga ya kumbura ko kuka kike ne, to meya sakaki kuka"
Harta tafara tafiya saikuma tajuyo ta dubesa a lokacin har kuka yazo mata tace "kaine yaya abdul"
Abdul ya zare edo " ni kuma..amma meyasa ni... "
Bata jira yakarasa maganarba tafita dakin da gudu, tana kuka, yatashi yabi bayanta yana kiran sunanta,
Momy na zaune a bakin gado tana ninke tufafi sabeey ta fad'o dakin tana kuka tafad'o jikin momy,
Damamaki Momy tadubeta tace "yan matana lafiya kuwa, waya tabaminke"
Subeey tana kuka tace momy bakomai,
Cike da mamaki momy tace " kamarya bkmai"
Tun bata rufe bakin taba abdul yashigo dakin,
Ganinta subeey a jikin momy tana kuka yasa yayi tsaye yana sosan keya,
Momy ta lura da yadda yake kallonta hakan yasa tagano cewa bayada gaskiya, ta kwala masa harara tace "kaine koh"
Noke kai Abdul yasoma yi kamar bayason yin magana yace " uhmm a a momy bani bane"
Momy tace " karyane fad'amun gaskiya ko yanzu nabata ranka yab'ace"
Abdul yana sosan kansa yace "momy bafa komai bane kawaidai munyi video ne, shine nace zan daurata a instrgrm ko Allah zaisa tasami mai sonta shikenan fa"
Momy ta hararesa tace " to waya gayama neman kai muke da ita dahar zakaje nema mata miji, ko angayama cewa tayi kwantaine, karka mata irin haka, batason miji yarinya karatu take" tana karasa maganar ta juya tad'ago kan subeey tana
murmushi tace "kyaleshi kinji subeeyn daddy, ai koshi bayada mai sonsa, kinma fishi" takarasa maganar tana sharewa subeey hawaye,
Maganar da momy tafad'a tasa subeey ta danji sanyi, takara share hawayenta sannan tad'ago kanta cike da shagwaba tace "momy kice karya sakemun irin haka"
Momy tayi murmushi ta kalli abdul tace "karka sake, kaji idan kasake zansa abbanku yamaka duka domin kataba masa yar lelensa"
Abdul yana dariya yace "tohm momy"
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment