New Post

Sunday, 27 November 2016

HAKA SO YAKE 47-48

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_47 - 48_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

_WASHE GARI_

*BIRNI*

Da maraice Abba da momie na zaune yana K'ara lallashin ta, saboda duk ta damu da tafiyar subeey, kowa na gidan yana kewar tafiyar subeey dadinma kanshi yana cikin damuwa. Gida yakoma tsit saikace gidan makoki, Abdul tun safe yafita yabar gidn domin bayajin dad'in zama gidan idan ba subeey,

Sallamar da akayi a waje shine ya sanya daddy tashi ya fita, motoci yatar a harabar gidansa birjin,  tunda ga nesa yake yima mutanen kallon rashin sani, sai dai ya saki fuska suka gaisa.

Wani daga cikinsu ne Yace "mune iyayen Ahmad, mai neman Yarinyar wajensu subeey," Abba yayi shiru cikin jimami ya tuna da momie tayi mishi maganar Ahmad ɗin, fuskarshi cike da jimami Yace "Tabbas hajia taimun bayani a kan zuwanku, anma k'urewar lokaci ya sanya bamu muku bayani ba"

Cike da rashin fahimta kawun Ahmed Yace "Kamarya Alhaji da wata matsala ne?"

Abba Yace "tohh maganar gaskia itace jiya mahaifin suwaiba yazo ya tafi da ita k'auye a can yayi mata miji, sai dai hak'uri"

Kawun ahmed yace "tohm shikenan Alhaji" jikinsu a sanyaye sukayi mishi sallama sukaja motocinsu suka bar gida,

Ahmad nazaune a falo shida ummansa suna jiran dawowar kawunsa, kawai sai ganinsu yayi cike dadamuwa, nan suka gaya masa labarin cewa subeey takoma kauye,
hauka kaɗaine baiyi ba, ya dinga kuka kamar k'aramin yaro Umminshi na lallashinshi, daƙk'yar ta lallasheshi ta hanashi tafiya k'auyen don cewa yayi sai yaje can ya dawo da subeeynshi,

*KAUYE...*

A ranar Alhajin birni yaje wurin subeey, hauwa sai k'ara shisshige mata take, malam habu da kanshi ya rakata inda Alhajin birni yake, an shimfiɗa mishi sabuwar tabarma, ta koma gefe ta tsuguna ta gaisheshi tana satar kallonshi.

Don kyau kam ba laifi yana dashi, Amma girman nashi har yayi yawa ga jinkai da nuna isa a lallai shi mai kuɗi ne.

Basu yi wani fira sosae ba yace ta tashi ta shiga ta turo mishi malam habu, ta mik'e ta shiga cikin gidan ta faɗa ma mahaifin nata saqon Alhajin birni.

Via OHW📚📲

Related Posts:

3 comments:

Popular Posts