New Post

Monday, 7 November 2016

HAKA SO YAKE 3-4

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_3 - 4_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Tajima tana kukan kafin tajuya takoma saman gado tazauna,
Filo ta janyo ta rufe fuskarta, sai kuma taci gaba da kukanta,
  Da karfi taji anturo kofar d'akinta, tayi sauri ta share hawayenta,
  Abdul ne yashigo da gudu yafad'o saman gadon datake zaune, yana dariya cike da nishadi yanuna mata wayarsa "kinga koh mutane dadama sunyi liking wannan video,  kuma sunyi comments sosai, duba kiga mesukace"
Subeey Tayi saurin kirkirar murmushi, sannan takarbi wayar tana dubawa, da gaskine kuwa taga anyi comments sosai, daga cikin wad'anda sukayi comments taga wani yace "wow amma dai yarinyar ta had'u saidai matsalarta d'ayace, edon nan nata dabatada lafiya, da edon  kalau yake, da wannan ko a India albarka" kafin takarasa karantawa Kwalla suka cinciko mata edo kiris take jira tafashe da kuka, sai kuma tayi karfin hali ta mayar da kukan,
Ta mika masa wayar tace " nagani"
Abdul Yana dariya yace "to me kika ce "

Mikewa tsaye  tayi tana kokarin fita tace " duk abinda kaga yadace shinace "
  Abdul yadube, sai a alokacin ya lura da irin yanayin datake ciki,
  Tsayar da dariyarsa yayi yan cewa " subeey miye, meya faru da edonki naga ya kumbura ko kuka kike ne, to meya sakaki kuka"
   Harta tafara tafiya saikuma tajuyo ta dubesa a lokacin har kuka yazo mata tace "kaine yaya abdul"
  Abdul ya zare edo " ni kuma..amma meyasa ni... "
  Bata jira yakarasa maganarba tafita dakin da gudu, tana kuka, yatashi yabi bayanta yana kiran sunanta,
  
Momy na zaune a bakin gado tana ninke tufafi sabeey ta fad'o dakin tana kuka tafad'o jikin momy,
  Damamaki  Momy tadubeta tace "yan matana lafiya kuwa, waya tabaminke"
Subeey tana kuka tace momy bakomai,
  Cike da mamaki momy tace " kamarya bkmai"
Tun bata rufe bakin taba abdul yashigo dakin,
  Ganinta subeey a jikin momy tana kuka yasa yayi tsaye yana sosan keya,

  Momy ta lura da yadda yake kallonta hakan yasa tagano cewa bayada gaskiya, ta kwala masa harara tace "kaine koh"
Noke kai Abdul yasoma yi kamar bayason yin magana yace " uhmm a a momy bani bane"
    Momy tace " karyane fad'amun gaskiya ko yanzu nabata ranka yab'ace"
Abdul yana sosan kansa yace "momy bafa komai bane kawaidai munyi video ne, shine nace zan daurata a instrgrm ko Allah zaisa tasami mai sonta shikenan fa"
  Momy ta hararesa tace " to waya gayama neman kai muke da ita dahar zakaje nema mata miji, ko angayama cewa tayi kwantaine, karka mata irin haka, batason miji yarinya karatu take" tana karasa maganar ta juya tad'ago kan subeey tana
murmushi tace "kyaleshi kinji subeeyn daddy, ai koshi bayada mai sonsa, kinma fishi" takarasa maganar tana sharewa subeey hawaye,

  Maganar da momy tafad'a tasa subeey ta danji sanyi, takara share hawayenta sannan tad'ago kanta cike da shagwaba tace "momy kice karya sakemun irin haka"

  Momy tayi murmushi ta kalli abdul tace "karka sake, kaji idan kasake zansa abbanku yamaka duka domin kataba masa  yar lelensa"
   Abdul yana dariya yace "tohm momy"

Via OHW📚📲

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 35ABDUL WAHAB 35 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Mi'kewa tayi zumbur kamar antsikareta, idonta harya fara canja kala, dai-dai sanda Abdul yaturo 'kofar d'akin ahankali yashi… Read More
  • ABDUL WAHAB 37ABDUL WAHAB 37 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Tsayawa yayi daga baya yana sosa 'keya yace "sannu da zuwa hajia," ta amsa mishi tana mishi kallon marar gaskia. Sai data za… Read More
  • ABDUL WAHAB 39ABDUL WAHAB 39 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Tafiya kawai take tana jefa ƙafarta harta fito daga gidan, batasanma unguwar ba ta tsaya tana kallon hanyar da zatabi t… Read More
  • ABDUL WAHAB 38ABDUL WAHAB 38 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Tun daga ranar ta koma rufe 'kofarta da makulli ta barshi a jiki, bata fitowa ko falon d'akinta sai Abdul bainan, ta k… Read More
  • ABDUL WAHAB 36ABDUL WAHAB 36 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Kwana biyu tayi suna jinya ita da Abdul, ko motsi zatayi ji yake kamar yayi mata, kulawa sosae yake bata, yaa tattara ya daw… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts