💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_15 - 16_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Tana komawa d'aki tatarar da momy zaune tana jiranta, da kuka tashigo d'akin, takarasa kusa da momy ta rumgume tana kuka tace "momy yaki saurarona, wai nafitar masa daga d'aki, nabarshi harya samu salamar zuci,," takarsa maganar tana kuka,
Momy tarika bunbuga bayanta "yi shiru subeey kiyi hakuri bari naje nasamesa "
Dasauri subeey tace "karkije momy, banason kowa ya yasakashi yayi hakuri dole, nafiso nida namasa laifi nizan bashi hakuri"
Momy tasauke nunfashi tace "toh shikenan, Allah yasa ya hkura, " tace ameen,
Nan dai momy taci gaba da lallashinta , harta samu tadaina kuka sannan momy tace "yanzu kitashi kije kiyi wanka, idan kika fito kizo ki kwanta insha Allah zaki samu natsuwa"
Tohm kawai tacewa momy, sannan tatashi tacire kayanta ta d'aura tawol tafad'a toilet, Saida tashige toilet d'in sannan momy tabar d'akin,
Bata jima acikin toilet d'inba tafito domin bawani dad'in wanka takejiba, saboda damuwar dake damun zuciyarta, bayan tafito, ko mekup bata tsaya yiba, mai kawai tashafa, sannan ta janyo wata doguwar riga tasaka, takoma kangado ta kwanta,
Tunani kala2 yarika zomata, tayi nadama sosai da abinda tayi, kalaman da abdul yafad'a mata sune suka rinka dawo mata akwakwalwa, duk taji bata yiwa kanta adalciba, a hankali hawaye suka rinka zomata, muyar a saukake tasoma fad'an "kowane mutum datasa kaddara, toni wannan KADDARA TACE, kuma tazomin a daidai lokacin daya dace, Ya Allah kabani ikon cin wannan jarrabawa, inaso namanta dashi a rayuwata, sonsa yafita a cikin zuciyata, dole na manta dashi, yazama dole nadaina sonsa" ita kadai take magana tana hawaye,
Sai kuma tayi Murmushi sanna ta furta "yaya abdul kenan, Allah yabaka wacca tafini" tana gama fada tashare hawayenta, sannan ta janyo filo ta gyara kwanciyarta,
Tafi minti ashiri amma bacci yaki Zomata, sai rabon edo take tana kallon silin d'akin,
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sai karfe biyar da rabi na yamma sannan tasamu tafito daga cikin d'akinta,
Falo tadawo tazauna ta kunna tv tana kallo, jitayi ana murza kofar d'akin abdul ana kokarin fitowa
A hankali take juyowa kamshin turarensa ya daki hancinta, ta lumshe edo tana murmushi, a lokacin taganshi yana kokarin fitowa sai kuma ta kura masa edo,
Shirin fita yayi cikin wasu kananun kaya, wadanda suka kara masa kyau sosai,
Saida yagama rufe d'akin Sannan yajuyo a lokacin sukayi edo hudu da subeey, ya d'aure fuska, kamar wanda aka aikowa mala'ikan mutuwa
Murmushi subeey tayi tace " yaya Abdul za'a fitane"
Tsaki yaja, ko uffan baice da itaba, yafice yabar gidan, tabi kofar daya fita da kallo,
Bayan yafita ta girgiza kanta tana murmushi, batason lokacin data soma yin hawayeba, ita dai kam yaza tayi da soyayyar abdul a cikin zuciyarta,,,,
Hakadai suka wuni, suka kwana agidan, fuskarnan tashi a daure, gabaki daya yaki sakewa a gidan,
*Bayan kwana biyu*
Kwata kwata abdul
yadaina sakewa subeey fuska, duk ta masa magana komai sanyinta toshi damai zafi yake mayar mata da amsa, Duk tashiga damuwa, harta soma ramewa,
'Yan kwana kinnan da suka sanu matsala tunda safe yake fita yabar gidan baya dawowa sai da yamma,
Momy kuwa zuba musu edo kawai tayi tana kallonsu, tunda Subeey tahanata zuwa tabawa abdul hakuri, ita ala dole da kanta takeson tabashi hakuri,
Yau subeey tatashi cikin tsananin damuwa, har saida tasomajin kanta na ciwo,
Saukowa tayi daga kangado takarasa bakin drowaer ta janyo wata doguwar riga tasaka sannan tafita tanufi d'akin abdul,
Yana tsaye a tsakiyar d'akinsa yana kokarin shirin barin gidan, yad'auko turarensa yafesa,
A daidai lokacin subeey ta turo kofar d'akin Nasa tashigo, Suna hada edo ya yatsuke fuska yayi tsaye euri d'aya yana kallonta yaji dame tazo,
Taku tafarayi hartazo daf dashi, suna facing d'in juna, Durkusawa tayi har kasa, sannan tad'ago kanta ta kallesa, a daidai lokacin hawaye suka sauko kan kumatunta tace "shine kadai lafina dan nace inasonka ya abdul, to bakin daya furta so, a yanzu shizai furta baya so, yaya abdul bazan iya jurar ganin fushinkaba, ko zan rasa nunfashina nemai nema maka farin cikine a duk inda yake, Dan Allah yaya abdul kadaina fushi dani wlh najima dabawa zuciyata hakuri akan ta hakura dakai, a yanzu so daya yarage a cikin zuciyata shine son yaya da kanwarsa, uwa daya uba daya, kuma kaima inason kakalleni da wannan fuskar, kayi hakuri yaya abdul.." kuka ya kube mata ta soke kanta kasa, taci gaba da kukanta,
Duban tausayi yamata, tayi matukar bashi tausayi, ajiyar zuciya yayi sanna yasa hannu yad'agota ya mikar da ita tsaye yana murmushi " na hakuri, sister subeey, kuma a yanzu na yarda da maganarki, zan rika kallonki a matsayin kwanta ta jini, kidaina kuka kinji" yafada yana kokarin share mata hawaye,
Dadi taji harcikin zuciyarta a hankali ta furta masa "nagode yaya abdul, amma ni sainaga kamar baka hakur.." Dasauri ya dora hannusa akan lips d'inta yace "shiiii, basai kin fad'aba nagaya miki na hakuri, idankuwa baki yardaba, mekikeson namiki wadda zai tabbatar miki dacewa na hakura"
Murmushi tayi sannan tace "kaje dani shopping yau kuma a yanxu"
Abdul yace "toshikenan jeki kishirya kizo muje" yakarasa maganar yana murmushi,
Takara share fuskarta tana dariya tafice tabar dakin cike da farin ciki,
Tana karasawa dakinta tafad'a toilet shap shap tayi wanka tafito, tazo tayi mek up, tayi kyau abinta, sannan tafito tanufi d'akin abdul, koda taje shima har yagama shirinsa,
A tare suka jero suka fito, momy tana zaune a falo taga sun fito, tabe baki tayi ta bisu da kallo sukuwa sai faman murmushi suke mata kwanin sha'awa, momy tace " yau naga ikon Allah, ayi fad'an ba'a sanar daniba, kuma a shirya ba'a sanar dani, ehhh lallai kuce kuncireni daga cikinku"
Subeey tana dariya tace "a a momy bahaka, ai tsakanin kanwa da yayanta sai Allah, ta juya gefen abdul tana kallonsa sannan tace "koba hakaba yaya abdul"
Abdul ya wangale baki " hakane fa kanwata"
Momy tadubesu tana dariya tace "to ina kuma zuwa haka"
Abdul yace "shopping zamuje"
Momy tayi Murmushi tace "toh Allah yakaiku lfiya yadawo daku lfy"
Su suka amsa da ameen suna dariya sannna suna fice sukabar falon,
Abdul ne yaja motar har suka karasa bakin plaza, sannan suka fito, suka nufi cikin,
Sunyi siyayya sosai, sannan suka fito, a but abdul yasaka kayan sanna suka shiga mota,
Bayab sun shiga motar Abdul yana kokarin yin reverse yaji yadaki wani abu a bayansa, kashe motarsa yayi sannan yafito domin yaduba yaga meya daka,
Wata motace zata shigo wurin sukayi karo, kuma fitilar motar d'aya ta fashe,
A sannu bakin Abdul ya furta " ohh shett" yana kokarin karasawa wurin mai motar,
Wani matashin saurayi ya bud'e kofar motar yafito ransa a bace yana shirin fara masifa, a daidai lokacin subeey tafito itama domin taga halin da ake ciki, a lokacin sukayi edo hud'u da matashin saurayin, turusss yayi yana kallonta...
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment