New Post

Saturday, 5 November 2016

A YINI ƊAYA 11-12

[11:36pm, 23/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

           Page1⃣1⃣

Ba'a jima ba kuwa sai ga maigadi tafe Alhaji Abdallah a bayan shi,
       A kid'ime Dady ya mik'a mashi hannu suka gaisa  tare da cewa "bismillah ga wurin zama",
    Alhaji Abdallah ya zauna sannan yace "nazo ne dama inji ko lafiya tun da yamma Ihsan ta baro gida tace nan zata zo wai Afnan bata da lafiya, kuma gashi har yanzu bata koma gida ba"

     Ido bud'e momy ta kalle shi cike da mamaki tace "Alhaji ai muma nan tun yamma Afnan tabar gidan nan wai kayi accident da jirgin sama ka rasu",

     Salati Alhaji Abdallah yayi a bayyane yana mamaki, a ranshi yace "kenan Ihsan bata zo nan ba?",

     Momy tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun! k'arya Afnan tamin kenan dama ba can zataje ba?",

      Ummah dai na tsaye cikin tashin hankali tana sauraren su, sun jima d'akin babu wanda ya kuma cewa wani abu kowa da abunda yake sak'awa a ransa, sai daga baya ummah tace "in kuwa hakane tou duk inda yaran nan suke suna tare, babu mamakin ko wani wurin sukaje shine suka tsara mana k'arairayi mu kuma muka yarda, Allah dai yasa lafiya suke".

     Dady yace "wannan hakane baiwar Allah! Tou ina yaran nan sukaje ne?",

    Alhaji Abdallah yace "nima tunanin da nake kenan, wai yara k'anana har sun san su had'a mana k'arya idan zasu tafi, kuma ni wallahi bana kullen Ihsan sosai, inda ma ace ina mata tsanani ne da sai ince banga laifin ta ba".

        Dady cikin tashin hankali yace "barin tafi Office yanzu nasan Sajent Musa yau night gare shi, inspector Bala ma kamar night ne saboda sanda na baro office lokacin yaje, barin hanzarta in tafi",

     Alhaji Abdallah yace "na manta ashe tare nake da DSP, ai da sauk'i ma kenan, sai mu tafi tare".

    Wayar Dady ce ta d'auki k'ara, dubawar da zayyi yaga Inspector Ashir ne, d'aga kiran yayi tare da fad'in "akwai magama inspector, gani nan zuwa Station d'in yanzu",

     "Yallab'ai nan ma dai akwai matsala, mutun biyu sukazo wai suna so a masu cigiyar yaran su sun fita tun yamma basu dawo ba, d'ayan ma wai twins ne yaran", inspector'n ya fad'a cike da girmamawa.

     Dady ya kalli Alhaji Abdallah sannan yaci gaba da fad"in "same case da zai kawo ni station d'in, ka jira ni yanzu zan taho" yana kaiwa nan ya kashe wayar tare da d'aukar key'n mota ya fita, Alhaji abdallah ma ya mara masa baya.

      Basu jima a hanya ba suka isa station d'in, cikin hanzari Dady ya nufi office d'in Inspector Ashir ya samu mutun biyu dattijai zauna sai raba ido suke kamar sunyi k'arya an turke su (lol..).

     Bayan inspector Ashir ya saaraa ma Dady sannan yace "yallab'ai kamar yanda na fad'a maka to ga mutanen nan, amma dai kaji daga bakin su",

      D'aya daga cikin su yace "sunana Alhaji Ma'aruf, yara na 'yan biyu Shareef da Shareefat ne suka bat'a",
   Cikin mamaki Dady yace "b'ata? Garin ya hakan ta faru?"
    Alhaji Ma'aruf yace "d'azu ne da yamma lokacin da bana nan Shareef yaje wurin Mamin su yace wai zasu je wata gaisuwar rasuwa baban classmate d'in su ya rasu, to da naji su shiru shine na gano inda sukace sunje d'in da k'yar da wahala ma na gane gidan, naje sun shaida min su babu wanda ya rasu a gidan su, suma 'Yar su ta fita tun yamma bata dawo ba, duk gidajen dangi da nake tunanin yaran nan zasuje naje amma ban same su ba, ga lambobin wayar su bata shiga, hankali na ya tashi sosai shine nazo nan ko da wani abu da za'a iya yi min".

     nannauyan ajiyar zuciya Dady ya sauke, gaban shi ya k'ara fad'uwa yayin da bugun xuciyar shi yake tafiya da sauri sauri, ya jima a haka kafin yace "to kai fa bawan Allah me ya faru?"

     D'ayan mutumin yace "nifa tawa 'yar gidan mahaifiya ta tace min zataje ta duba ta wai ta dad'e bata je ba, nikau har da dad'i naji ta kula min da uwa, jn ta shiru har dare yayi bata dawo ba yasa na kira ta amma tak'i shiga, na kira mahaifiya ta tace min ai Nuratu bataje inda take ba, hankali na ya tashi sosai, nayi iya bincike na amma ban same ta ba, shine na yanke hukuncin zuwa nan nasan insha Allahu zakuyi bakin k'ok'arin ku".

     Alhaji Abdallah in banda kallon su babu abun da yake yi, to wai miye dalilin da yasa yara matasa suka b'ata a lokaci d'aya? Kuma same case ne kowa k'arya yayi kafin yabar gida? Tambayar da yakewa kansa kenan wadda yasan bata da amsa har sai lokacin da aka gano yaran.

      Dady ya gyara murya yace "abunda ya kawo ku nima shine muhimmin abunda ya fito dani a wannan lokacin nida bawan Allah'n nan.." nan ya basu labarin duk abunda ya sani har Ummah dake gidan su akan b'atar 'yar ta itama.

    Alhaji Ma'aruf yace "tabbas yaran nan aduk inda suke suna tare, baza'a tab'a kiran wannan da coincidence ba saboda abu ne wanda yake a bayyane, fatan mu dai Allah yasa a duk inda suke suna lafiya",

    Alhaji Bashir (Baban Nuratu) yace "ai sai asan abunyi ba wai mu tsaya anan muna magana ba, ko gidajen radio ne sai mu fara xuwa kafin gari ya waye asan abunyi".

     Da wannan maganar suka rantaya su duka hud'un a cikin motar Dady, basu zarce ko ina ba sai VISION FM, nan suka bada sanarwar b'atan yara matasa wanda dukan su babu wanda ya wuce shekaru 16-17 ba.

Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:43pm, 23/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

          Page1⃣2⃣

K'arfe 11:05pm
*~AJIWA DAM~*

    Wani irin haske ne mai had'e da guguwa mai k'arfi ya haskaka wurin,
     Feenat dake gefe makure har ta sik'e da kuka tana ganin hasken ta saki ajiyar zuciya dan wani sanyi sanyi taji a ranta, d'aga kanta da zatayi taga yanda akayi kaca kaca da *AREWA STARS* kamar wasu dabbobi,
   Can kuma hasken ya canja launi izuwa red colour,
   Md da Reeshat dake gefen ruwa suna kallon ikon Allah bayan hasken ya b'ullo sukaji alamar motsi ata inda suke, cike da tashin hankali Reeshat ta k'adaddabe Md gabanta sai dukan uku uku yake, bata ankara ba taji anja gashin ta dataima mayen gyara sama ana ta wulu wulu dashi, sosai take jin zafi dan dama a ranar tayi sabuwar relaxer, sai da tayi sama sosai da ita sannan ta jefar a bakin wani k'arfe da akebi ta jikin shi idan za'a shiga ruwa, take ta sume bayan ta sai zubar da jini yake.

      Md ma ta up side down ta d'auke shi da k'arfi ta jefar a jikin Reeshat, shima sumewar yayi inda k'afar shi d'aya ta cire tun daga cinyar shi sai zubar jini take, cinyar daban ta fad'a a cikin ruwa sai sauran gangar jikin ne a jikin Reeshat.

      Nuratu, Shamow da Sady sun dunk'ule junan su suna kallon yanda wannan halittar take wuji wuji da Md da Reeshat saboda har a lokacin wannan jan hasken bai mutu ba, hankalin su tashe dan sun san dole suma sai anzo kansu, babu mai iya yiwa d'an uwan sa magana a cikin su sai faman rawar lab'b'a suke, ga wata irin zufa na keto masu duk da sanyi sanyin ruwan Dam d'in dake akwai amma bai hana masu jin zafi ba.
     A hankali wani irin ruwa ya ringa saukowa a daidai inda suke, ruwa ne bak'i k'irin tamkar ruwan kwata ga wari da yake yi,
    Da mamaki a duk inda ya d'iga na jikin su sai yayi wani irin bororo kamar masu gyambo, haka yaita sauka a jikin su har saida yayi masu kaca kaca da jiki kamar wanda suka k'ok'k'one,
   A had'e ta jefo masu wani d'an k'aramin dutse wanda baki d'ayan su ya had'a ya sumar dasu a lokaci d'aya basu kuma sanin kome yake wakana ba.

       Dariya ta kuma fashewa da ita da k'arfin gaske har sai da itacen wurin suka ringa girgiza da kansu, k'yallayen da akayi decoration dasu kuwa da kansu suka ringa yayyagewa, speakers da generator kuwa rugurgujewa suka ringayi kamar yanda ake rugurguza dunk'ulallen gishiri ko maggi,
    Ta dad'e tana dariyar kafin ta d'aure fuska wasu irin blue ruwa suka ringa kwaranya daga idanuwan ta wanda da alama ruwan hawaye ne,
    Girgiza kanta tayi taci gaba da waigawa gabas da yamma bata ga kowa ba, ta diba kudu inda taci karo da Samir wanda ya gama kid'imewa amma shi a zaton shi ya tsira saboda a wani lungu ne ya lab'e inda matuk'ar baka san yana wurin ba to bazaka ganshi ba, amma da mamaki wannan halittar ta zira dogon hannun ta ta cafko shi a tafin hannun ta, bakn ta takai a cikn wandon shi sai ga kayan marmarin sa (lol..) a bakin ta had'e da jini sai zirara yake,
     Tofar dashi tayi sannan ta jefar da Samir wanda a lokacin har ya sume tsabar azaba da tayi masa yawa.

K'arfe 11:30pm
*~kerry~*
         tayi tafiya mai nisa har sai da ta sik'e da tafiyar ta nemi wuri ta zauna sai haki take, hankalin ta tashe sai nishin gajiya take,
    A hankali ta fara jin hayaniya a kunnen ta wadda ta k'ara tsorata ta, k'ara kasa kunnenta tayi taji k'arar tana k'ara yawaita,
    "Oh Dad help me!" Kawai take fad'a,
     Da k'arfi halittar ta jawo ta da hannu ta rik'e ta da tafin hannun ta, wata shu'umar dariya tayi wadda ita kad'ai tasan ma'anar ta sannan ta busa ma Kerry iska da bakin ta adaidai kanta sannan ta jefar da ita, take  Kerry ta sume itama.

        bakin Dam d'in ta koma ta kalli Arewa nan taga Feenat takure sai rawar jiki take,
      Hannun ta tasa ta jawo ta ta rik'e ta, a hankali Feenat ta fara furta *"AU'DHU BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAKA, BISMILLAHILLADHI LA YADHURRU MA'ASMIHI SHAI'UN FIL ARDI WALA FISSAMA'I WAHUWAS SAMI'UL ALEEM"*

Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚

Related Posts:

  • MATATAH CE 46-50♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡           46-50 ©Rabiatu sk msh       ®NWA    &nb… Read More
  • MATATAH CE 52♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              52 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 53♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              53 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 54♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             54 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 51♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              51 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts