New Post

Wednesday, 16 November 2016

HAKA SO YAKE 27-28

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_27 -28_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Subeey ta bushe da dariya tace "perfect, komai ka amsa daidai" shima dariyar yake yace "ai akanki komaima daidaine a wurina"
Subeey tatsayar  da dariyarta tayi gyaran murya sannan tace "yanzu meke tafe dakai,"
Amhed yayi jim yana tunani saicen yayi murmushi yace "duk abinda zuciyar subeey ta saka mata tohm dashi ahmed yazo"
Subeey tayi fari da edonta d'aya "umm ni zuciyata ta bani cewa Ahmed yazone da sakon..." Saikuma tayi shiru tana dariya,
Ahmed yayi saurin cewa "uhim fad'i mana menene"
Subeey ta gimtse dariyar ta sannan tace "sakon so, amma saidai subeey fa tanada wanda take so"
Saida ahmed yaji gabansa yafad'i dasauri yakara gyara zamansa "dan Allah da gaske kike "
Subeey takara bushewa da dariya jin yadda ya tambayeta kamar mai shirin yin kuka,
Da kyar ta iya samu ta tsayar da dariyarta a lokacin duk ahmed ya k'agu yaji gaskiyar lamarin,
Subeey tasauke nunfashi bayan tagama dariya sannan tace "zuciyar subeey fankoce babu komai a cikin sai jiran masoyin gaskiya, mai so tsakani da Allah, mai iya zama dani a duk  halin danake ciki, mai karemun martabata da kuma kimata, mai sakani farin ciki, amm.." Sai tayi shiru,
Ahmed jiyake kamar an masa bushara da zuwa hajji, farin ciki fal a zuciyarsa, dasauri yace "uhim ina jinki karasa mana"
Subeey tace "amm sai kuma wanda zai yarda duk safiya ta Allah na wanka masa mari sau biyar, batare dayaji zafiba, saidai kawai yacemun "thanks dear" ... " dariya ta kubuce mata takarasa karasa maganar,

Ahmed shima dariyar yake sosai " dan Allah kibarni haka, cikina harya fara ciwo, akan dariya," yakara maganar yana dariya,

Subeey takara sauke nunfashi bayan tagama dariya tace "kaji sharud'an subeey, kaifa meye naka sharud'an"
Ahmed yasauke nunfashi sannan yace "duk naji kuma na amince, saidai kuma ni banada sharud'a amma inada dokah"
Subeey tace "uhim ina jinka meye dokar"
Ahmed ya yayi gyaran murya sannan yace "dokar itace karki yarda kikula wani domin inada zafin kishi akan abinda nakeso, sannan kuma ina yiwa macce so 100% banason ta yaudare, domin hakan yana sakani matsala sosai, ina sonki subeey, nasan itace kalmar dakake jiran kiji nafad'a tun d'azu"
Subeey tasauke nunfashi tare da lumshe edo, kalaman dayake fad'a  suna ratsata har cikin jijiwowin jikinta,
Tana murmushi tace "godiya nake, saidai kuma nima inason nace ..." Sai kuma tayi shiru,
"Kinason kice me, dan Allah kifad'a wlh  na k'agu naji" Ahmed yafad'a yana murmushi,

Wata irin kunya taji ta rufeta, tasa hannunta d'aya tarufe fuskarta d'ayan hannun kuwa yana rike da waya,  cikin sanyin murya tace "nima inasonka..." Tana karasa maganar tayi saurin kashe wayar, saboda kunyar dataji, tana dariya,

Abdul Yana lab'e a bakin kofa duk abinda take fad'a yana jinta, jiyake kamar ana masa zuga - zugin wuta a cikin zuciyarsa, edonsa sunyi ja sosai, da karfi ya turo kofar d'akin yashigo zuciyarsa a zafafe, saida subeey  ta razana jin anturo kofar d'akin da karfi kamar za' a karya kofar, ta mike zaune a dai dai lokacin suka had'a edo....

Via OHW📚📲

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts