[5:09pm, 20/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page7⃣
Wak`ar *broken angel* aka saka a lokacin shigowar Kerry, cike da k`asaita ta fito daga motar ita da saurayin ta Triple A, hannun su sak`ale da juna suna wani taku kamar basa son taka k`asa,
Ihu duka wurin aka d`auka take suka fara fiddo wayoyi suna snapping nasu, tafi kake ji sosai wurin da k`arfi, kai da kagan su kasan suna cike da farin ciki tsantsar shi, banda Feenat data ware kanta gefe cike da haushin zuwan ta wurin.
*karfe 6:30pm*
A lokacin ne za`a yanka cake, nan aka hau tafin yanda Triple A ya kama hannun Kerry ya d`ora akan cake d`in, hotuna sosai suke d`aukar su kuma a lokacin ne hotunan sukafi yin kyau saboda rana ta fad`i hasken flash lights yafi fita da kyau.
Sautin kiran sallar magrib ne yake fita kad`an kad`an daga wani masallaci nesa da dam d`in, da alamar dai can cikin garin Ajiwa yake. Feenat ce zaune tana tunanin yanda za`ayi tayi sallah, can wata dabara ta fad`o mata, a bakin wani famfo taje tayi alwala ta bud`e handbag d`inta ta zaro hijabin ta ta saka, can daga gefe inda ba`a jin kid`an ta koma tayi sallar ta sannan ta dawo cikin mutanen.
*k`arfe 7:30pm*
Cashewar su suke sosai kowanen su ya kama partner d`in shi, a hankali na fara jiyo wani sauti mai had`e da wani irin kuka_kuka kamar kukan shanuwa ko alade, sukam da yake sunyi nisa a casun su har yanzu basu fara jin shi ba, tun sautin yana fitowa kad`an kad`an har ya fara yawaita, sautin wak`a na fita daban sannan na wancan kuka kukan ma yana fita daban, sai kuma yanda kururuwar take k`ara tashi sosai.
Feenat ce keta bige hannun MD dake faman shafar gabanta har yana k`ok`arin kai hannu cikin rigar ta, kunnen ta ta kasa sosai dan yanda sautin abun yake fita har ya fara yin yawa, ido ta fara zarowa 😳 tana kasa kunnuwan ta cike da tsoro da fargaba, da k`arfi ta buge ma MD hannun shi wanda yasa shi dawowa hayyacin sa,
Da sauri ya koma wurin Reeshat dake rawa ita da MC, rungumo ta yayi ta baya ya fara shafar ta a hankali, nan sukaci gaba da romancing juna cike da jindad`i.
Itakam Feenat sosai hankalin ta ya tashi, nan ta fara tunanin to wannan kururuwar ta mecece? K`ok`arin magana take masu amma muryar ta bata fita saboda sautin wak`ar dake tashi.
"Na shiga uku ni Safeenat! Wannan k`arar ta mecece? Kar dai namun daji ne zasu cinye mu" ni kuwa Amrah nace in namun daji ne ma ai da abun yazo da sauk`i saboda akwai hanyoyi da yawa zaku iya guduwa.
Sosai wannan k`arar take k`ara yawaita, a hankali sautin speakers d`in ya fara canjawa yana komawa irin wancan sautin na kuka, Reesha ne yace "oh common! Dj wannan kukan daka kunna mana fa? Abeg ka canja shi mana, abu kamar kukan jaki", Sally dake rungume da Reesha tayi dariya tace "wuce jaki ma wannan".
Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[5:22pm, 20/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page8⃣
Sautin ne ya k`ara d`aguwa sosai, Dj`n ma hankalin shi ya soma tashi, shidai a iya sanin shi bashi da wannan sautin a duk wak`ok`in shi, k`ok`arin wucewa ya fara yi amma d`if! Wayar ta d`auke, dvd d`in ta mutu, ga hasken fitilar duka ya mutu, sai wannan sautin da yake ta k`ara yawaita.
Feenat jiki sai rawa yake, ta ambaci sunan Allah amma sam ta kasa, ga wani irin mugun duhu daya mamye wurin, Dj ma hankali ya k`ara tashi, Sally tace "mun shiga uku! Wa ya kashe mana hasken?",
Reesha yace "kila dai cikin samarin nan ne wani ya kashe ta, shegu maza! Iskanci yayi dad`i kenan",
Cike da tsoro da rawar murya Sally tace "wannan ba kashe shi akayi ba, kaji sautin da yake tashi fa, na shiga uku ni Saleemah" sai hawaye sharrrr a kumatun ta.
Wata irin k`ara da k`arfi speakers d`in sukayi wanda yasa lokaci daya kowa ya dawo hayyacin sa, tsoro duk ya kama su, wani irin iska mai had`e da guguwa ya fara tashi, Kerry uwar birthday tuni hawaye sun cka mata ido, wayar ta take ta nema amma ta rasa inda take, ita dai tasan akan table ta ajiye ta a lokacin da zasu yanka cake amma kuma yanxu ta duba nan babu ita, can daga nesa ta hango hasken ta alamar ana kira saboda wannan muguwar k`arar bazata bari k`arar waya ta fita ba, hannun ta ta zira zata d`auko amma sai taga wayar ta k`ara yin gaba kamar anja ta, k`ara zira hannu tayi amma wayar ta k`ara tafiya, binta taci gaba dayi ana jan wayar har saida tayi nisa sosai ta fara fita daga cikin mutane, har tabar baki d`aya area`n da suke party.
Ihu dukkanin su suke, daga mai kiran dady sai mai kiran momy amma babu mai kiran sunan Allah, sannu sannu kukan nan ya k`ara yawaita, da suna jin murya d`aya ne amma yanzu ya zama muryoyi da yawa babu adadi.
"Tashin hankali" na fad`a a raina, tuni biro na ya kufce ya fad`i tsananin tsoro da fargaba, ban san a ina yake ba dole sai Sis ta siyo min wani.
Muje zuwa, ba`a fara komai ba yanzu za'a fara inji Amrah.
Amrah and Rabeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
0 comments:
Post a Comment