💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_9 -10_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
*Washe gari*
Subeey tana kwance kan gadonta tana tunani a zuciyarta, tunanin samun mafita take, kullum kanta cunkushe yake yana ƙk'ara daukar zafi, zafin soyayyar wanda baisan kanayi ba da tafi komi ciwo.
A fili take faɗa ma kanta, "wai meyasa nake sonshi? Meyasa na kasa faɗa mishi? Wannan wane irin masifaffen so ne daya hanamin sukuni ```HAR A ZUCIYA?``` Meyasa Abdul ya kasa gane son da nake mishi, *DAMA HAKA SO YAKE* baicika kai kansa inda aka damu dashiba? A lokacin wasu zazzafan hawaye suka dararo mata akan fuska, a hankali take bud'e bakinta tana fad'an "Na gaji wlh, nagaji da wannan Zurfin cikin, na gaji da ɓoyan abinda ke wahalar dani, yau zan tilastama zuciyata faɗa mishi, Zaifimin idan nasan matsayina a wurinshi".
Da wannan k'warin gwiwar data samu ya sanyata share hawaye, ta mik'e tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa da sukayi matukar k'ara mata kyau.
A hankali take tafiya, duk da a zuciyarta ta k'agara taje ta faɗa mishi sirrin dake a cikin zuciyar tata.
Tana tura k'ofar ɗakinta zata buɗe kamar wanda aka jefo ya nata mata, wuuu! Ta razana sosai har tana shirin komawa sannan taga shine sai dariya yake mata, yace "ke kin cika tsoro da yawa wlhy."
Ta harareshi da wasa tace "kai kuma kaa ciki tsokana ba, Allah ka tsoratani da yawa, banyi tunanin kananan ba."
Yace "kinsan kuwa lokacin dana ɓata ina jiranki? Yaja hannunta suka jera tana ɗan tsayawa tace "nifa da maganar dazan faɗa maka, ka tsaya kaji mana"
"wace magana kuma ko break fast bakiyi ba? Kinga ni yunwa nakeji kuma ke kaɗai naketa jira, kizo idan mun gama saiki faɗa min.
Ba don taso ba yaja hannunta, kitchen suka shiga tare suka haɗa break fast ɗin suka fito, don duk yunwar da zasuji sun saba ma kansu dacin abinci tare, kuma indai ba nata bane Abdulƙ baijin daɗinshi.
Yana ci kuwa yana santi, cikin nishaɗi yake faɗin "wlhy kanwata kin iya girki da yawa, bazan gaji da faɗa miki duk mijin daya aureki yayi dace sosae, don saima naa faɗa mishi, ya dage wurin kulamin da k'anwata, don mai sa'a ne kawai zai sameta".
Shiru tayi saboda wani abu daya tokare mata a wuya, abincinma kasa haɗiyeshi tayi, idan akwai abinda tafi tsana a duniya bai wuce kalmominnan na yayanta abdul ba ```Duk mijin daya aureki yayi sa'a,``` idanma yanayi ne don yabonta ita ba burgeta suke ba.
Tafiso taji yana cewa "idan har na aureki ƙkanwata naafi kowanne namiji sa'a".
Jin da yayi tayi shiru ya sanyashi kaɗa mata hannu da sauri ta ɗago, murmushin yake ta mishi kawai sannan taci gaba da cin abincinta cike da tausayin kanta.
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment