💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_35 - 36_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Yana shiga falon, ɗakin momie ya wuce yana k'wala mata kira, yanayin kiran ya sanya ta tunanin ba lafiya ba, ta taso tana tamyarshi "lafiyarka kuwa Abdul, meya faru da kakemin wannan kiran?
Cikin bacin rai Yace "momie wa yace akabar subeey ta shigo da wannan Yaron gidannan?"
Da mamaki momy Tace "wanne Yaro kenan?*
Abdul ya nuna kofar fita, Yace "wancan saurayin nata mana"
Momt tace "tohh saboda me za'a hanashi shigowa tunda wurin subeey yazo? Koda laifine dan namiji yazo wurinta ita ba macce bace"
Abdul yakara tsuke fuska yana fad'an "Amma dai momie ai bai kamata ace tana shigowa da samari barkatai ba a cikin gidan, hakan zai iya tab'a matabar gidan nan"
momie tatab'e tabaki tana kallonsa Tace "Ikon Allah, banda Ahmad akwai wanda subeey ta taɓa kawowa gidannan? Kadai kawai ka fito fili ka faɗa mana kishi kake, idan kana sonta zamufi kowa farin ciki Abdul, tunda dama a tare kuka tashi"
Kasa cewa komi yayi saboda takaicin maganar momie da Yake ji, shikenan da yayi magana sai ace kishinta yake? Sonta yake? Tohm shikenan daga bazai kara shiga sabgar taba, duk a zuci yake wannan zancen,
A fili kuwa kasa furta komai yayi , Juyawa kawai yayi yabar ɗakin momie da bishi da kallo tana dariya.
Sama-sama subeey take bama Ahmad amsa tambayoyin dayake mata saboda kwata kwata hankalinta baya jikinta saboda ganin yanayin yadda Abdul yashiga gida, saitajita duk tayi wani tajima bataji irin wannan akanshiba tun ranar datayiwa kanta alkawarin zata daina sonsa kota halin k'ak'a
basu wani daɗe sosae ba ta sallameshi ya tafi. Saboda gabaki d'aya batajindadin jikinta,
Tana shiga gida ɗakinta kawai ta shige ta faɗa gado zuciyarta cunkushe da tunani. Kala-kala
*Washe gari*
Su duka babu wanda ya fito break fast duk momie na lura dasu daman babu wanda Yaci dinner jiya a cikinsu, kuma yanzu gashi safiya ta wayw sunki fitowa suyi break fast, talura da cewa suna cikin damuwa, hakan yasa tanufi d'akunansu,
Kiransu tayi su duka suka hallara a falo ta zaunar dasu tana fuskantarsu,
Abdul duk ya haɗe rai, subeey tayi kalar ba ruwanta d'in kamar wata marar lafiya, Momie ta fara magana.
"Ku duka ba kananan yara bane kunsan abinda ke cikin zuciyoyinku, idan har kunason junanku wannan abin farin cikine a wurinmu, ku faɗa mana kawai tun kafin maganar yaronnan ahmed tayi nisa a tsaida ita, meyasa kuke nema ku cutawa kanku"
Su duka shiru sukayi, kuma babu wanda yad'ago koda kansa a cikinsu,
Momie tayi ajiyar zuciya sannan takara kallonsu tace "ku nake saurare"
Abdul Ya buɗa baki zaiyi magana "amm.. Ammm.."
Subeey ta rigashi "basai kafaɗa ba Ya Abdul, momie babu maganar Aure tsakanina da Ya Abdul, ni na samu wanda ke sona kuma zai aureni, shima inai masa fatan Allah yabashi tagari"
Momie ta jinjina kai, tace "Shikenan Allah ya zab'a abinda yafi zama alkhairi"
Shiru Abdul yayi jin maganganun da subeey tayi, Yayi niyyar ya buɗa bakine ya tabbatarma momie da cewa yanason subeey kuma da aure, amma ita ta rigashi da faɗama momie ita Ahmad takeso, ita kuma subeey tayi hakane don batason ya faɗawa momie bai sonta, domin babu abndata tsana fiye da jin hakan,
Via OHW📚
0 comments:
Post a Comment