♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
77-100
K'arshe✔
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Ahmad ya turashi, "Miye haka zaka wani faɗomun? Kaa damu mutane da Saudat! Saudat!! Saudat!!! Yanzu kuma ta zama taka da ganinta kaa wani rugo?"
"tohh aini naa kasa yarda ne, da gaske Saudat MATATAH CE?"
"gaka gatanan dai, sai ka tambayeta" Najib sai murna yake yama rasa inda zai saka ranshi don farin ciki, Ahmad ya k'ara zai fita yasha gabanshi,
"ka faɗamun gaskia da gaske nayita kiran sunan Saudat?"
"gaban Momie da Yasseer ma kuwa"
Hannu ya saka ya toshe bakinshi, "ashe ina sonta har haka?"
"Gashi kuwa da ganinta a gidanka harka warke"
"hakane fa" ya faɗa bakinshi har kusa da kunne don daɗi ma ya kasa rufuwa, sai kuma ya juya ɗakin Saude da sauri ya koma don gani yake kamar zai koma ya iske batanan.
Tananan a inda ya barta, yayi sallama, da zazzak'ar muryarta ta amsa. Ita ɗince kuwa, ya faɗa a ranshi, ta wani k'ara yi mishi kyau sosai a ido, ya kasa daina kallonta ga wani irin soyayyarta da ke fizgarshi, a hankali yayima kanshi mazauni a bakin gadon.
"Saudat!!" ya kira sunanta, har saida tayi murmushi kyawawan hak'oranta suka fito, yaushe rabon da taji ya kira sunanta? Tayi kewar ganinshi sosai, ga tausayinshi da takeji ganin ya rame.
"Da gaske ke ɗince kuwa? Da gaske ke MATATAH CE? don Allah karki faɗamun mafarki nake, idanma mafarki nake ki faɗa musu kar a tasheni, don ko a mafarki nake tare dake, bazanso in tashi ba har abada"
Ganin yanda ya ruɗe saboda farin ciki, itama sai murmushin jin daɗi take, gangarawa tayi inda yake, ta ɗaura hannuwanta biyu saman k'irjinshi sannan ta kwantar da kanta, tanajin bugun zuciyarshi.
Ajiyar zuciyah ya saki, ita ɗince kuwa, ya sak'alo hannunshi ya ida mak'ale ta a jikinshi kamar wani zai k'wace mishi.
Ya tafi duniyar jin daɗi, yau Saudat ta zama tashi, kuma sai tunanin Yasseer ya faɗo mishi, anya kuwa yasan da aurennan? Wanne irin kallo zai mishi idan yaji yaa aura matar daya saki? Bazai iya yin abunda zai taɓa ran yayanshi ba gaskia! Zare hannunshi yayi daga jikinta. Ta ɗago kai tana kallonshi lokaci ɗaya taga yanayinshi ya canja.
Ya mik'e zumbur, yayi hanyar fita, "ki kwanta, ina zuwa" ta kalleshi cikin rashin fahimta, yaɗan dawo ya durk'usa a gabanta shima baiji daɗin yanda ya mata ba.
"Abunda na miki kin yafemun?"
Hararanshi tayi da wasa, "idan kaci gaba da tuno abunda ya wuce bazan hak'ura ba"
Murmushi yayi ya ware hannunshi, "naa daina, Meyasa ma nake mantawa da Najib baya laifi wurin Saudat?"
Murmushi, yanzu hankalinshi ya kwanta da bata cikin damuwa, ya juya ta tafi ɗakinshi, shidai yasan suna matuk'ar son junansu shida Saudat, anma tayaya zai iya rayuwar aure da matar da yayanshi ya saki?. Ɗakin da yake a matsayin nashi ya koma, anan ya kwanta ya kwana tunani.
Tun tana zaman jiranshi taji shiru, kaɗan kaɗan taa duba lokaci, sai taayi kaman ta kirashi a waya saita fasa, duk ta damu tana tunanin ina ya tafi, zuciyarta ce ke zugata ta k'yaleshi kawai duk inda ya tafi dai yasan yaa barta tana jiranshi ai, tana kishingiɗawa barci ya kwashe ko kaya bata canja ba.
Da wuri ta farka duk da bata samuyin barci da wuri ba ga gajiyan tafiyan da sukasha kuma, bata nema komawa ba ta shiga kitchen da niyyar ɗaura musu girki.
Muryanshi ta jiyo, "badai girki zaki ɗaura ba? Momie tace zata aiko dashi"
Ta jiyo har yayi wanka yana cikin shirinshi, anan ya kwana ko gidan Momie? Bazata iya tambayanshi ba, sai dai ta gaisheshi kawai.
"lafiya lau ya kika tashi? Ya gidan?"
"Alhamdulillahi" sai kuma sukai shiru, shi bai tafi ba, kuma bai bata hanya ba.
"kin jirani a jiya?" ta ɗaga mishi kai, ya wani zaro ido.
"kindaiyi barci ko?" ta k'ara ɗaga mishi kai tana murmushi yanda ya zaro ido.
A tare sukayi breakfast, suna gamawa yayi kamar ya fice, ya shige ɗakinshi kawai, banson yana yawaita zama kusa da ita saboda yanda soyayyarta ke fizgarshi, gashi baison fita, gani yake kamar insun haɗu da Yasseer zaice mishi bai kyauta ba.
Haka zaman nasu yake, sai tayi da gaske, zata ganshi sau ɗaya a rana, duk yanda zata tsareshi da fira bazai zauna ba sai yayi dubara yabar inda take, kuma bai wani nuna mata a fuska, tun abun bai damunta harya fara, gashi ita ba wata k'awah ba da zata nema shawararta. Kullum Momie zata kirata taji ya suke, koda abunda take buk'ata, wani lokacin har ta haɗata da Hafsat a waya suyi fira.
Suna wata ɗaya da aure Husna ta mata waya Rabi'ah ta haihu, ita kaɗai ta ringa tsallen murna, yanzu zata fita ta huta da zaman kaɗaici a gida.
Saiga Najib ya fito daga ɗakinshi, yana ganinta yasan tana cikin farin ciki, "Rabi'ah ta haihu" yace mata
"Yaushe zamuje mu gano Baby?"
"Bazaki je ba"
"Ganin Babyn Rabiah fa nake nufi, ina son inje plz zamuje yanzu?"
Cikin kakkausar murya Asalin Najib ɗin data sani tunda yace "bazakije ba nace"
Jikinta duk yayi sanyi tace "tohm" sai kuma duk baiji daɗi ba, ya ɗan rage murya anma dai cikin faɗa faɗa, "Duka yaushe akai auren da zaki fara fita? Ko so kike kowa sai yasan kin dawo?" ya ida magana duk don son ta tanka, baiji daɗin tohh ɗin data ce ba tunda ya ɓata mata rai, shiyasa yake so ya gyarota.
"A'ah" kawai ta k'ara cewa a tak'aice, saima ta tashi ta barshi kawai, don batason ganinshi cikin ɓacin rai.
Har daren suna, bataje ganin jaririn Rabiah ba, sai dai Husna ta tura mata da hotanshi, ko maganar ma taa daina mishi, suna zaune Husna ta k'ara mata waya.
"Gaskia Auntie Saudat da alama gobenma Ya Najib bazai barki zuwa ba, wannan irin kulle haka?"
"Zanzo Insha Allah Auntie, Baby dai kar yayi fushi da Auntienshi plz"
"Mamanshi dai tace har yayi, don wannan Autien tashi bata damu dashi ba"
"A'ah auntie Rabiah kartace haka mana, Allah inanan ina fama da hotanshi, kamar inyi tsuntsuwa inzo, ɗan kyakkyawan Babyn mu kamar bab...."
Sai kuma tayi shiru maganar ta mak'ale mata, ganin Najib ya tsura mata indo tunda take magana yake kallonta, "Sai nazo dai Auntienah" ta katse wayan.
"Rabiah ma tasan kina gidannan?"
"ya bazasu sani ba? Muna waya dasu sosai" shiru yayi yana tunani, anma ya akai insun haɗu da Yasseer bai taɓa nuna mishi ba?
"ki shirya muje siyayyan Babyn"
"Da gaske zamu fita?"
"da wasa nake" ta ɗan ɓata rai duk murnarta ta koma ciki.
"idan kina ɓata ɗai bazamuje ba" tayi dariya, da murnarta ta shirya suka fita.
Siyayya sosai suka masa, sannan suka wuce gidan Momie, murna sosai tayi da ganinsu, bama kamar da taga Hankalin Najib a kwance, ba k'aramin murna tayi ba, saiji take dasu gaba ɗayansu.
Hafsat ma tunda ta mak'alema Saudat tak'i barin jikinta, sai labari take mata duk wanda yazo bakinta, ita dai amsa mata kawai take saboda kunyar Momie gata er fari, Najib ya mik'a hannu zai kamota, "ni bakiyi kewata ba sai mamanki ko?"
"kaima naayi taka, anma nafi daɗewa banga Mamanah ba"
"ai tare zamu tafi ko? Kiyita kallon mamanki kullum bazaki k'ara kewanta ba" sai kuma ta mak'ale kafaɗa, "idanna tafi kuma chohuwarnan zatayi kewata"
"laah! Waye chohuwan?" yace mata
Momie dai dariya take musu, "ai bama zan barki tafiya ba, su Rabi'ah ma sunyi naci sun bari, Hafsat tananan wurin tsohuwa"
"anma dai za'ana bamu aronta ko?"
"saina duba dai"
Hafsat tace "Mamana wai menene soyayyan gaskia?"
Kamar ta buge bakinta saboda kunyar data sakata, gashi Momie na wurin don ma Allah ya taimaketa kaman bataji ba, "ke ina kika taɓajin wannan maganar?"
Yasseer dake shigowa yace "nizan baki baki amsar wannan tambayar! Soyayyar gaskia itace kaso mutum tsakaninka da Allah ba don wani abu nashi ba, ka zama mai rik'e amanarshi, duk laifin daya maka zuciyarka bazata taɓa ɗaukan laifinshi ba, kullum kuna cikin fahimtar juna, Masoyin gaskia shine wanda zai kasance dakai a kowanne hali, shine wanda bazaka iya jurar rashinshi ba na kowane lokaci, Soyayyar gaskia shine kaso mutum a duk yanda yake"
Hannu ta ɗaga tana tafa mishi, su Saudat kam sai dai dariya kawai, "ya isheki hakanan ko kinason na baki misalin masoya na gaskia?"
"yayanmu ashe kana kusa?"
Saude ta katse musu firan, Najib ya kalleta da mamaki,
"yanzu na iso, ashe rabon in gaisa da Amaryarmu,"
"Ina wuni"
"lafiya lau fatan duk kuna lafiya"
"Alhmdlh, ya baby?"
"Rabi'ah bata faɗa muku yana fushi ba?"
"yau dai zamu goge laifi, don wannan tafiyar tashi ce shi kaɗai, ko yaya?" ta kalla Najib ya ɗaga mata kai, sannan Yasser ya mik'a mishi hannu suka gaisa, firansu sukaci gaba dayi.
Ba Momie kaɗai ba, har Najib sunji daɗin yanda Yasseer da Saudat suka manta da baya, suka manta da komai suka rungumi k'addara.
A gidan Rabi'ah kowa sai ji yake da Amaryan Najib, bama kamar danginshi sun hana bakinta shiru, wasu ta sansu tun wurin biki wasu kuma sai suna sukazo, cikin sakin fuska take gaisawa da kowa, kamar en uwanta, sai faɗi suke gaskia Amaryan Najib nada kirki.
Rabi'ah taa yaba sosai da kayan da Saudat ta kawo, sai ɗaga kayan ake ana tayasu Godia, Yasseer har kamar yayima Najib faɗa, wai miye sai sunyi wani hidima, sai dare sosai suka koma gida, washe gari da wuri ta saka ya maidota suna, haka sukaita hidima har bayan suna.
A gajiye ta dawo, suna shiga falon tayi hanyar ɗakinta, hutu kawai takeso, saida ta kusan shiga yace "inajin yunwa fa"
"Me zakaci?"
"komai ma indai daga gareki ne"
Jikka kawai ta ajje, ko kaya bata tsaya ragewa ba, ta shiga kitchen, mai sauk'i ta girka mishi, fried couscous, ta haɗo mishi da cocunut juice, yana falo ya baje yau kallo yakeji, ta ajje gabanshi ta fara zubawa.
Ya zuba mata ido, "Momie fa ta hanamu Hafsat, Haka zamu zauna ba yara a gidannan?"
A ranta tace 'A'ah satosu zamuyi, ko kuma insha a ruwa tunda kaa nema hak'k'inka naa hana'
A zahiri kuma tace "ai tace zatana bamu aro ai"
"abun aro kam an taɓa ado dashi? Kamata yayi fa muma da namu"
"hakane" ta tak'aita zancen, tana gama zuba mishi ta wuce ɗakinta.
Da mamakinta yana gamawa ɗakin nata ya shiga, sai da ya tadata sukayi sallahn godia ga ubangiji, suna gamawa suka kwanta, ga mamakinta ko kaɗan bai nemeta ba, ita abun nashima yanzu yaa wuce bata mamaki, har hak'urinta ya fara k'arewa.
Hakan zaman nasu ya koma, zasu kwana a ɗaki ɗaya, anma ya bata baya kawai, da rana ma indai yana gida suna tare da juna, yana k'ok'arin sakata nishaɗi a koda yaushe, anma babu wani bayani.
Ta gaji da zamansu a haka, da taga da gaske yake dai, ta k'udura lallai yau zata kawo k'arshen komai.
Wata fitinanniyar rigar barcinta ta gyarama zama, yana fara kallonshi ta rigashi tafiya kamar kullum, tun wurin wanka saida ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito, ananma ta daɗe gaban mirrow tana shafa mayuka, turarukan da Husna ta bata kusan duka ta juye ma jikinta, duka ɗakin ya ɗauka k'amshi, maganunguna kam ta ɗuresu ingantattu wanda Husna ta haɗa da kanta ta san mata, data zura doguwan rigan ita da kanta tasan taayi kyau, milk ce mai santsi, shara-shara gata er qarama ko gwiwa bata kai ba, ta kwanshe gashinta data nannaɗe, ya zubo har wurin k'ugunta, shima yasha gyara ta ko ina k'amshi take, kashe wutan ɗakin tayi ta koma ta kwanta.
Tana kwanciya ya shigo shima da shirin barcinshi, ya kunna wutan ɗakin, gaba ɗaya daddaɗan k'amshin dake tashi yaa cika mishi hanci, ai da sauri ya maida ya kashe yana hangota, ga wani irin kwanciya da tayi mai jan hankali.
Ya k'ara kunna fitilan yana k'are mata kallo, anya kuwa zai iya kwana a ɗakinnan? Gaba ɗaya ganinta ya gama birkicewa, k'afafunshi dak'yar suka kaishi inda zai kwanta, duk k'amshinta ya cika mishi hanci, sai juyawa yake yana satar kallonta, anma dai k'ok'arin lallasar zuciyarshi yake, shifa ba abunda yakeso ba kenan, Sauden dai yakeso.
Tsawon lokaci ta jishi shiru? Anya kuwa Najib lafiya yake? Yau zata gane ma dai, wani irin juyawa tayi ta k'amk'ameshi ta baya, jikinshi har kyarma yake, ba k'aramun ruɗewa yayi da jinta a jikinshi ba, ya saka hannu ya fara janyeta, cikin wata rikitacciyar murya, a hankali cikin raɗa tace "mafarkin tsoro nayi, tsoro nakeji plz karka sakeni" tuni ta k'arasa kashe mishi jiki, baija da tsawo ba, nan take labarin ya canja.
Tun daga ranar wani son juna ya k'ara shiga tsakanin Najib da Saude, koda yaushe yana manne da ita, kullum k'ara sonta yake, koda na rabin second baison ya ganta nesa dashi, ko ina ta saka k'afarta suna a tare.
Sanda ta fara laulayi kusan a tare sukayi, idan tana wahala kamar ya mata kuka, ganin yanda yake damuwane take k'arfin hali indai suna a tare.
Gashi Cikin daya tashi girma sai yayi k'ato, dak'yar take tashi, hutu musanman ya ɗauka don ya ringa kula da ita, don hana Momie ma yayi a koma da ita gida.
Sanda ta tashi haihuwa ma ba k'aramin wahala tasha ba, kwana biyu suna asibiti tana aikin nak'uda, har saida aka kawoma Najib takarda ya saka hannu za'a mata C.S, yak'i ya saka, shi babu mai yanka mishi mata, ana cikin rigima dashi nurse ta rugo tana faɗa ma likita ai kan jaririn ya fara fitowa.
Lafiyayyun yaranta uku ta haifo, maza biyu mace ɗaya, ita ɗinma tana cikin k'oshin lafiya, a ranar ma aka sallamesu, duka iyalan suna cikin k'oshin lafiya.
Najib sai murna yake, gashi tsakiyar yaranshi har uku, sai dai ya ɗauka wannan, ya aje ya ɗauka wannan, ya rungumo Saude a k'irjinshi, "bansan dame zan biyaki ba akan wannan kyautar da kikamun ba, Allah yayi miki albarka, Allah ya biyaki da Aljannah MATATAH"
"Ameen"
"wanne suna kikeso mu saka musu?
"banda wani zaɓin daya wuce naka, sai yanda kace"
"Muna da mai sunan Momie dai(Hafsat), su bruz sun mana wayau sunyi Daddy, tunda Maza biyu ne, sai mu saka mishi sunan su Mama da baba, Allah yaji k'ansu shi kuma ɗayan mu saka sunan bruhh"
K'ara k'ank'ameshi tayi, tana k'ara jin soyayyar Mijinta, "Kaa biyani, wallahi ka biyani Mijina, Allah ya qara mana Soyayyar juna, mu zamu miji da mata har k'arshen rayuwarmu"
"Ameen, Insha Allah ke MATATAH CE, har a Aljannah"
Waih😃 TAMMAT BIHAMDULILLAH.
Anan na kawo k'arshen wannan littafinnan nawa, godia ga Allah (S.W.T) daya bani ikon kammalashi, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mun.
Jinjina mai yawa gareka,
Abdul'azeez ililee,
A thank you is never enough Especially for you, you have done end number of things to me, I don't know how I would be able to repay back. But, still thanks a lot for everything, you are the best.
RAZ, tsayawa faɗar matsayinku a gareni badai a wannan ɗan guntun littafinnan nawa, komai zan faɗa bazaiyi dai dai da irin matsayinku a wurina ba, hakik'ah ni Rabi'ah banda kamarku, sisinah AMRAH A. MSH da MY ZAHRA BB, Allah ya qara haɗe kanmu Ameen.
Dole kuna da fili a cikin littafinnan.
My waliyya wally
Kishiyatah Sadeey S Adam
Sis beely badaru
Aunty jegal
Pharty bb
Miemee bie
Kwaiseh maryama
Sistonah Zahra bukar
Autar hajia
Aneelurv
Aunty sis
Momienah didi Aneesa
Shafa'atu
Baby Amrah
Basma er lele
Basma mai sanyita
Chohuwa Candy
Kazar layyatah
Maman Adnan
Meesha lurv
Mrs Umar
My stylish
Ummiee Agos
Miss xoxo
Zeey Alk'aseem
S.A Azeez
My Inlaw Mjay
Kdeey
Maman Haneep
Ayusha
Jiddah
Munayshat
Fiddausi sodangi
Biebie Isah
Ummul fadeela
Ashnur.
Aunty Maijidda musa
Aunty bilki Maman Sarki (Shaheed)
Aunty Asma'u musa Barah.
Ummu Zainabu (Haneesa).
Harma da wanda ban faɗa ba, bawai na manta daku bane, har kullum kuna raina.
```Fertymerh zahra``` tawa, kullum tunaninah dai INA ZANGA PHERTY? Dolene nazo ganin pherty don bazan gaji da gode miki ba, Allah ya qara basira.
My Abdul jega
Raheem jege
Abdul'azeez AAJ
Abba Gana
Gaisuwa mai yawa gareku👍🏻
En uwanah banda kamarku.
Hauwa'u sk msh
Fiddausi sk msh
Aysha sk msh
Masoyah na: Hak'ikah kune silar yin murmushina, ina ma ace zan iya lissafoku gaba ɗayanku? Tabbas banda kamarku masoyanah.
Na gaisheku en group ɗin da nake ciki, dama duk inda littafina yake zuwa, nagode sosai masoya.
RAZ NOVELLA 1&2, ku masoyane na hak'ika, nagode da wannan soyayya taku.
IYAYENA
Allah yaji k'anshi mahaifinmu da rahma ya gafarta mishi, Allah ya k'ara tsawon kwana momienah, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, hak'ik'a Uwah ce ta gari, ina sonta fiye da rayuwatah!
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
Ina Alfahri daku, Allah ya k'ara ɗaukaka, ya k'ara mana haɗin kai, gaisuwa ta musanman ga dukkan members na wannan k'ungiya mai Albarka.
Masu neman wannan littafin dama sauran littafaina, zasu iya ziyartar blog ɗina.
www.babymsh.blogspot.com.
08032133670 whatsapp and imochat plz comment kawai, banda Maza👏🏻 follow me @instagram, Rerbee'art_sk, Snapchat Rerbee'at_sk
Nice dai taku Babynmashi😊
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment