New Post

Wednesday, 5 April 2017

MATATAH CE 73

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             73

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Saude na can baya tana kuka batasan meke faruwa ba, saida tayi mai isarta ta fara jiyo gidan yayi tsit, ta tashi ta koma cikin gidan bayan ta share hawayenta.
   Bataga kowa ba kamar anyi shara, babu en biki babu en gidan, babu en biki, duk da su duka babu wanda takeson haɗuwa dashi, anma saida jikinta ya bata ba lafiya ba, ta tambaya ɗaya daga cikin en aikin ta faɗa mata suna can asibiti Yasseer yayi accident.
   Komawa ɗaki tayi hannunta akai tana ci gaba da rusa kuka, gaba ɗaya abubuwa sun jagule mata, tama rasa tunanin me zatayi.

  Tana zaune tana kuka ta haɗa kai da gwiwa sai dai ta jiyo sallaman Momie a ɗakinta,  wani irin kunyarta takeji, cikin muryar data gama cin kuka ta amsa, tayi shiru tana sauraren Momie.
   Ta kira sunanta "Saudat", sai da gabanta yayi mummunar faɗuwa, kasa amsawa tayi Momie taci gaba da magana,
     "Allah ya gani Saudat, na rik'e ki amana, ban rageki da komai ba tamkar er dana haifa, tun ranar zuwanki kikamun alqawarin zamui zama na amana, na yarda dake, shiyasa ban taɓa tunanin hakan daga gareki ba, tunda nake da Yasseer tun haihuwarshi bai taɓa ɓoyemun wani abu ba sai a kanki"
   Yanayin da Momie tayi maganar saida Saude ta ɗago tana kallonta, gabanta sai faɗuwa yake tana jiran hukuncin da zata yanke mata, taci gaba da magana.
   "na yarda yayi miki laifi, ya faɗamun duk abunda ya faru, na yarda da laifinshi a matsayina na mace, kuma bawai ina goyon bawanshi bane, anma laifin da kikamun na ɓoyemun ba k'aramun al'amari bane" a rikice Saude ta k'ara ɗagowa tana kallonta.
   "tabbas bazan iya ci gaba da zama dake ba, kin wargaza duk wani yarda dana miki, bazan iya haɗa jininah da mak'aryaciyah, munafukah ba,  abinda kika mana kanki kika cuta" ta wurga mata takarda a inda take.

Tunda Momie ta fara magana, ko hawayen ma nema tayi ta rasa, saurarenta kawai take mamaki cike da zuciyarta, damk'e takardar tayi da hannuwanta biyu.
     "daga yau ki fita daga rayuwar ƴaƴana, don bazan taɓa bari ki rabamun kawunansu ba"
   Batasan yanda tayi ba, sai dai kawai ta ganta gaban Momie, wani razanannar kuka na k'ara tunzuro mata, "Don Allah Momie kiyi hak'uri, nasan na muku laifi, don Allah karku yankemun hukunci cikin fushi, wallahi Allah shine shaidata, ko kaɗan ban nufin iyalan gidannan da komai sai alkhairi, wallahi komai ya faru bada son raina bane"
   Wani irin kallo Momie ke watsa mata da bata taɓa ganin ko maqiyi ta yima shiba, "ai donma kar in canja tunani nah ya saka ban baro asibitinnn ba saida na tabbatar ya cikashe miki saki uku" wani irin zaro ido tayi tana kallon Momie, "don haka ya rage naki, anma bazaki taɓa lalata mana farin cikin gidannan ba" tana gama faɗar haka ta fice tabar Saude duk'e a wurin.

   Lallai yanzu ta ida yarda da ta gama rasa damarta a wurin Momie, tun farkoma meyasa ta mata k'arya? Tana magana kamar ba mace ba, bata ga laifin aurenta da Yasseer yayi ya gudu ya barta ba, ta kirata da munafuka, tama manta da shima Yasseer ɗin munafuntarsu yayi yai aure bada saninsu ba, ita dai haka rayuwanta take, duk lokacin da ta fara farin ciki sai wani k'addarar tazo ta lalatashi. Gani tayi duk tunanin bashi zai fiddata ba, ta tashi ta fara haɗa kayanta.
    Cikin mintina da basu wuce talatin ba ta gama tattara komai nata, ta fito Momie na tsaye bakin k'ofa tana ganinta ta kauda kai, a hankali take tafiya ta k'arasa inda take, har k'asa ta duk'a tana k'ok'arin rik'e kukanta.
    "Zan tafi Momie, don Allah ku yafemun duk laifin dana muku, Nagode da duk Alkhairan da kukamun, tsakanina daku sai addu'ah, bazan taɓa mantawa daku ba"
   Ko kallonta Momie batayi ba,  ta mik'e gwiwa a sanye ta fice ko Hafsat bata nema ba, tunda taga Ubanta taci gaba da zaman a hannunshi kawai.

Kuyi haquri da ɗan kaɗan, A gurguje dai.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 35-36```MAKASHINKA...```           35-36 ©Rabiatu sk msh Sun ɗanyi tafiya mai nisa daga unguwarsu duk a cikin garin jigawan, gani tayi yaa ɗauke hanya sun nufi wata unguw… Read More
  • MAKASHINKA 33-34```MAKASHINKA...```           33-34 ©Rabiatu sk msh Wani Yammaci shamsuddeen da sadeey na zaune a gefen wurin wasa a harabar gidan. Wasa take da yatsun hannunta tana yawan sat… Read More
  • MAKASHINKA 37-38```MAKASHINKA...```          37-38 ©Rabiatu sk msh Da sauri kaka ta ɗebo ruwa a buta ta nufota dashi tana mata sannu, suma duk tsayawa sukayi suna mata sannu. Shamsuddeen da s… Read More
  • MAKASHINKA 31-32```MAKASHINKA...```            31-32 ©Rabiatu Sk Msh Shamsuddeen ganin yayi gudu mai nisa basu biyoshi ba ya sakashi tsayawa yana wasi-wasi, ihunta ya jiyo daga can nesa,… Read More
  • MAKASHINKA 29-30```MAKASHINKA...```           29-30 ©Rabiatu sk msh     A hanyarsu ta komawa gida, sadeey tayi shiru tana sauraren Shamsuddeen yana ƙara mata nasiha, ba … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts