♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
75
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Rabi'ah ce tsaye kan Yasseer, yana kwance idanunshi a rufe anma ba barci yake ba, duk maganan da take hankalinshi ya tafi wurin tunanin halin da Saude take ciki.
Hannu ta sanya ta shafi cikinta, "mu tafi ko? Tunda Abbanka baison ganinmu"
Wani irin zabura yayi, "Abbansa kuma? Kina nufin kin shirya haihuwa yanzu?"
Ɗaga mishi kai tayi tana murmushi, ta kamo hannunshi ta ɗaura saman cikinta, yaron cikin sai motsi yake, shi kuma Yasseer yanata murmushin jin daɗi.
"tayaya zan iya cire gudan jininka daga jikina? Idan nayi haka ai koni da kaina zan iya k'aryata soyayyar da nake maka,"
Wani irin farin ciki yakeji, ya kwantar da kanshi jikin cikinta yanajin wani irin farin ciki marar misaltuwa.
"Don Allah ka yafemun, ka manta da duk wani abu dana taɓa maka, a shirye nake da zama duk irin macen da kakeso"
"kin biyani Rabi'ah, kin gama biyana indai kika haifamun abunda yake cikinki, Na gode sosai"
"naji, anma ai akwai abubuwa da yawa da nake maka wanda bakaso plx ka faɗamun in daina, kana yawan cewa Saude mace ta gari ce, anma baka taɓa cemun ba ni, plz Masoyi nima inason in zama kamarta"
"Allah ya baki iko dear, tabbas ina yima sauran mata addu'an kasancewa na gari kamar Saudat, komai yaa wuce dear"
Murmushi tayi "Ina tausayin Saude, wata rana zamuje neman gafararta"
"Nagode da wannan soyayya Hniee"
A yanzu Rabi'ah na iyakar k'ok'arinta na kauda ma Yasseer damuwa, soyayya take nuna mishi kamar jaririn goye, soyayyar da koda tana Amarya basu yita ba, sai yanzu ne yake tabbatarwa da yayi sa'ar mata, ya yardar ma kanshi kuma Soyayyarshi dai ɗayace, kuma Rabi'ah yake yimawa, tausayin Saude ne kawai mak'ale a ranshi shiyasa ya kasa mantawa da ita. Basu daɗe a gidan Momie ba suka tare a sabon gidansu da aka gama gyara musu, daman gaba ɗaya suka tattaro suka dawo Nigeria.
Najib kam kullum babu barci, babu cin abinci sai tunanin Saude kawai, yaa kasa manta zaman da sukayi da ita, ta bar mishi abubuwan da bazai taɓa iya mantawa da ita ba, duk yabi ya rame soyayyar Saude na wahalar dashi sosai, idan kuma yana tuna abunda ta mishi duk yanda yaso yaji haushinta bazai iya ba.
Momie tana lura dashi, ba k'aramun tausayawa ɗan nata take ba, da taa bashi ɗan lokaci tasan zai manta da Saude ne, anma har kusan 4 month kullum damuwarshi k'aruwa take.
Ita da kanta ta tafi ɗakinshi kai mishi abinci, yana kwance rigingine
baimasan hawaye suke zuba a idanunshi ba, tunaninshi yake da Saude a zamansu, kullum cikin nishaɗi bata yarda ta ɓata mishi rai, ranar daya fara koya mata karatu ya tuna, shi kaɗai ya dunga dariya kamar zararre fuskarta na dawo mishi tana dariya da kyawawan hak'oranta.
Motsin mutum yaji da sauri ya share hawayenshi cikin dubara, ya ɗauko wayanshi yana latse-latse, sai ga Momie ta shigo da sauri ya tashi ya amsa kayan hannunta.
"Momie keda kanki kuma?"
"ai hakan kafiso ko?" Ta zauna saman gefen gadon, ya zame k'asa zai zauna, ta kalleshi "Zaunanan magana zamuyi" ya tashi ya koma gefe ya zauna.
Kallonshi take duk ya rame ya fara fita hayyacinshi, yayi fari sosai duk ya koma sukuku dashi kamar ba Najib ɗinta ba, da alama damuwar take ranshi harta fara fin k'arfinshi.
"Ina lura dakai duk kwanakinnan, akwai abunda kake ɓoyemun, ba halinka bane ka faɗamun ko me yake damunka"
Ya lumshe idanunshu da duk sun faɗa, "Ba komi Momie"
"ka faɗamun nace, har yanzu ka kasa mantawa da Saude ko?"
"Wace Saude kuma? Nina manta da ita da daɗewa Momie, don Allah ki dainama tunamun da ita" ya k'arasa maganar cikin damuwa.
"Naji, indai hakane tun yaushe nake maka magana daka fito da matar aure? Da dai ban sanka da saɓa ma umurnina ba"
Yaja wani wahalallen numfashi, "Momie nifa gaba ɗaya matannan tsoro suke bani, bani da wani zaɓi sai wadda kuka zaɓamun"
"shikenan tunda ka barmun zaɓi, Allah yayi maka albarka ya zaɓa maka ta gari"
"Ameen Momie"
"daga yau banson k'ara ganinka cikin damuwa, in baso kake nima ka ɗauramun damuwa ba"
"Insha Allah momie naa daina"
Tashi tayi ta bashi wuri, itama a ranta duk batajin daɗi, tana mutuk'ar kewar Saude, gidan duk ba daɗi da batanan, tana ɗebe mata kewa, idan tananan komai bata bari tayi da kanta, ga Hafsat kullum cikin neman mamanta take, gidan yayi kamar ba kowa tunda Saude ta tafi duk basujin daɗi.
Najib tun ciwo na cinshi a tsaye harya kwantar dashi, gaba ɗaya ya rame sosai sai an kaishi asibiti, an maido ana tunanin ya samu sauk'i sai ciwo ya dawo sabo, gashi yak'i buɗa baki ya faɗa kome ke damunshi, idan ance mishi Saude yace ba ita ba.
Ranar daya tashi basu tsoro basuyi tunanin zai kwana ba, suma ya ringa yi daya farfaɗo sai kiran sunan Saude, ko kaɗan bai cikin hayyacinshi, Momie har saida ta zubda mishi k'walla tayi mutuk'ar tausaya mishi.
Yasseer ya isketa falo inda tayi tagumi tana tunani, durk'usawa yayi saman gwiwoyinshi, ya langaɓe kai irin yana neman alfarma a wurinta.
"Momie yanzu da kika gano damuwar Najib meyasa bazaki mishi maganinta ba? Don Allah Momie karmu rasashi"
"bansan me zanyi ba, Najib yanason Saudat anma me mutane zasu ce akan ya aura matar da yayanshi ya saki?"
"abunda mutane zasuce zamuyi tunani ko abunda addini ya halarta? Tabbas Saudat MATATAH CE a da, anma yanzu babu wani sauran alak'a tsakaninmu da ita, na rantse da Allah babu sauran wani abu da nakeji a raina game da ita, ina mata kallone a matsayin k'anwatah, indai don nine Momie don Allah karku raba masoyannan guda biyu dake matuk'ar son junansu, tabbas munyi zaman aure da Saude, anma na k'aramin lokacine watanni kawai mukai a tare kuma babu wani shak'uwa a tsakaninmu, su kuma fa da suka yi shekaru suna gina soyayyarsu? Najib shine masoyin Saude na gaske, shi yafi cancanta da ita".
Momie tayi shiru jikinta a sanyaye, "ni jikina duk yayi sanyi da maganganunka, ka tuna da abunda akama Saudat fa, kana tunanin zasu sauraremu?"
"momie kefa kika fi kowa sanin kyawawan halayenta, tana da mutuk'ar kawaici da saurin yafiya, tana kuma girmama buk'atunki, sannan itama nasan har yanzu tana nan da soyayyar Najib, kinga dai dai kenan, taa gama iddarta babu sauran neman aure cikin aure"
"hakane fa duk abunda ka faɗa a kanta, wallahi har kunyar kaina nakeji abunda na mata, yanzu da wanne ido zanje neman alfarma a wurinta?"
"karki damu Momie, insha Allah komai zaizo da sauk'i"
Dak'yar aka samo kan Najib, ya farfaɗo anma dai yana kwance babu k'arfi jikinshi, sai dai k'arfin hali kawai.
Momie dai da taga taa tashi rasa ɗanta, ta tabbatar da indai ba samun Saude yayi ba shima zata iya rasashi, batayi shawara da kowa ba ta shirya tafiya garinsu Saude, daga ita sai driver da kawunnan su Najib guda biyu.
Batasan yanda zasu amsa maganar da zataje da ita ba, tun a hanya take ta addu'ah a ranta Allah ya basu nasara ya sanya komai yazo musu a sauk'i.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment