[10:36, 3/9/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣Soyayyar whatsapp❣
@OHW
1-10
Kishingide take saman lumtsumemiyar kujerarta 2seater da remote a hannunta! Masu aiki nata yi mata hidima, daya dga cikin wayoyinta ne tayi qara ta dauka sbd ganin sunan dake jiki (U're my only) tana sanyawa a kunne yace "ina jiranki love kizo ki qarasa shryani! Murmushi tayi tace "my love kenan kullum kamar qaramin yaro yake komamin! Masu aikinsu ta kalla da keta faman jera abnci a dinning tace "kundai kammala komi ko? Ynzu d zai safko break fast! Har suna hada baki suka ce "An kammala komai hajia, sannan ta gyada kai ta haye sama!
A shagwabe ta kalleshi sannan tace "shne d zakayi wanka kai kadai ba tare daka jirani ba? Kunnenshi ya riqe da hannu biyu yana murmushi yace "soriyo Maryamar deen, bnso ki batamin wannan kyakkyawar kwalliar ne da tayi matuqar yi miki kyau! Qara bata fuskah tayi ta juya mishi baya cikin shagwaba tace "shkenan tunda hkane shrinma naa fasa bzanyi mka ba!
Batasan sanda ya qaraso ba sai dai taji yaa rungumotah taa fada jikinshi ta baya, rada yayi mata a kunne da sauri ta juyo yana murmushi ya daga mata gira, qoqarin zamewa ta farayi daga jikinshi nan da nan yaci gaba da kissing dinta ta ko ina, daria take ta qalqalawa tace my d ka kusan makara pa! Yace "bndamu ba cwthrt indai ina tare dke! Bata samu damar cewa komi sbd yanda ya fara rikitata! Sai zullewa take sbd yanda yake kissing nata ko ina!
Qaara taji a kunnenta da sauri ta farka a gigice, sai da ta dawo cikin nutsuwartane sannan ta duba dk taa yamutse er yagalgalallar katifar da take kwance! Gwaggo ce taci gaba da fada tana cewa "Maryama dga gyaran daki kuma saiki dawo daki kita sharar barcin kin barni da yunwa har rana taayi baki mana kalaci ba? Shin barcin me kke ne ma da kka cikamin kunne da daria! Saida tayi kyakkyawar miqa sannan tace "Ynzu gwaggo dan Allah idan baninan wake miki kalaci da ina cikin barcina mai dadi zaki tasheni? Sai kuma ta tuna tace "wane barci mai dadi ma a wannan katifar da inka kwanta kana jiyo qasa! Gwaggo tace "oho dai ki tashi ki hadamin kalaci ko in kira ubanki ya kawomin! Tace "Yanzu pa gwaggo, Yau inna hada miki gobe kya nemi mai hada miki, don ynzu xan fara harhada kayana gobe in bar miki gidan in komawatah makaranta! Gwaggo tace "tohm maryama in kka tafi dawa zaki barni cikin gidan? Tace "A'ah zan tattara ne in bar karatun in dawo nan ko barcin kirki bzaki barni inyi ba, ta tashi tabar falon gwaggo na cewa "kinga Maryama tawa taho kici gaba da barcinki, ko saurararta maryama batayi ba ta tafi tsakar gida ta hura wuta sannan ta daura ruwan zafin dafa indomie.
Rabiatu sk msh
08032133670
[11:25, 3/9/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣Soyayyar whatsapp❣
@OHW
11-20
Sunacin indomie gwaggo sai mita take "ni sau nawa zance miki bnson taliarnan Maryama! Idanma taliyar zaki dafamun ki dafa er gargajiya mna wadda muka sabaci, ita dai maryama tun lomarta ta farko bata qara ci ba, taa riga taa koma duniar tunani, soyayyar deen ce ke qara azalzalarta, tana yawo tana shgewa ko wanne gabobin jikinta!
Qarar wayantane ya katse mata tunani da sauri ta dauka tana addu'ar Allah yasa shne! Bashi bne sunan Aboki taga an rubuta a kan wayar! Murmushi tayi tace "Allah sarki Ahmad, dauka tayi ta kara a kunne sannan tace "Yadae Aboki? Kewatah ko? Yace "eeh mna Abokiyah kema kinsan dole ne zanyi kewarki, naayi registration naa kasa komawa mkrntar sbd dk ba dadi idan bakinan! Tace "karka damu Ahmadnah nima ina kewarka, dad kawai nake jira ya dawo qasar nan Ya sallameni! Yace "yayi er gidan dad dan Allah karki wuce week dinnan! Tace "bzan wuce ba Aboki!
Gwaggo kamar jira take ta gama wayae tace "uban waye zai dawo dga qasar waje? Kauda kanta tayi gefe tace "nipa gwaggo ba maganarki bace wannan! Gwaggo tace "tohm indai babnki ne dazu da kina barci ya aiko laure kije ki anshi kudin siyayyah! In banda abnshi ma karatun mace na minene sai yaa dage yaayita nemn kudi yana kashe miki don dai kiyi karatunnan! Tace "haba gwaggo kema pa mai biyamin karatunnan ce, tace ni rabani ina naga wannan maqudan kudin? Shidai yayita tarawa yana kashe miki!
MARYAMA kenan
Diya ga malam musa da saude, mahaifinta mai qaramin qarfine sosae da sana'ar niqan da yakeyi da kuma sayarda cefane, yake samu ya tattara mata kudin karatu da wanda zasuci abnci gdanshi, su ukku iyayenta suka haifa itace babbah, sai qannenta biyu twince hassana da usaina, tun daga yaye ta koma wurin mahaifiyar babnta gwaggo! Suna zaune a garin gada jihar kaduna, a ynxu haka tana karatune a islamic university dake jahar katsina, Anma ko babbar qawarta namcynta Maryam batasan ainihin garin da take ba don dk sun dauka a garin kaduna take zaune mahaifinta shahararren mai kudine, Yanda take fada musu kenan kuma dk yanda Maryam da Ahmad sukaso kaawo mata ziyara bata taba amincewa ba
Wurin qarfe tara tana kwance text dinshi Ya shgo kamar hka "Masoyiyah kihau online ina jiranki mu fara fira kafin muyi waya! Da sauri ta bude datar ta don damn abnda take shrinyi knan, watau tahau suyi fira da masoyinta deen!
Rabiatu sk msh
May 27 at 4:00pm · Public
|
0 comments:
Post a Comment