```MAKASHINKA...```
39-40
©Rabiatu sk msh
Taaji daɗin furar tasha ta sosae suna ci gaba da firarsu.
Sai da maraice yayi sosae sannan Shamsuddeen yazo yafiya da ita, taaji daɗin zama tare dasu ji take kamar ta ƙara ma ranar tsawo, suma basu so rabuwa da ita ba, kuɗin da daddy ya bata ne ta ɗeba ta rarraba musu.
Duka tsarabar da momma ta bata ta ba su kaka duk da tsadar su bata dace dasu ba, sannan ta miƙa ma Malam duka kuɗin hannunta, daƙyar ya ansa saboda taace daddy ne ya bata ta basu sannan yayi mata godiya da sanya Albarka.
Haka suka tafi cike da kewar ƙauyen, taayi farin ciki sosae, tana cikin ranakun da bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta.
Sai da suka shiga gari suna tafiya saman mashin ita da shamsuddeen ta fara bashi labarin unguwarsu da yanda ta burgeta da alama cikin farin ciki take.
Ta tafi surutu tana bashi labari kawai ta tsinkayo muryarshi "wane irin miji kikeso ki aura?" daria tambayarshi ta bata tace "idan na faɗa bazakace naayi rashin kunya ba Ya deen" Yace "nifa na tambayeki? Hannunta ta cire daga saman kafaɗarshi kamar yana ganinta ta rufe fuskarta.
Tace "mijin dazai soni ki kaɗai ya deen, wanda zai girmama buƙatata, ya bani duk lokacinshi da kulawarshi, damuwarshi ta zama tawa kamar yanda zamu raba farin ciki a tare, mijin dazai ɗagamin tafin ƙafarshi cikin sauƙi in shiga aljannah" murmushi yayi yace "gaskia kina da tunani sosae ƙanwata, ba kamar wasu matan da sunfi son auren mai kuɗi ba, ba kamar ke da kika tashi cikin jin daɗi" tace "ay kuɗi bazasu kawo musu farin ciki ko soyayyar gaskia ba" yace "hakane maganarki, daman ko wacce mace tana da irin tunaninki"
Tace "tohh kaima Ya deen ka faɗamin wacce irin mace kakeson aure?" Yace "Mace mai ilmi, wacce zatamin biyayya, da bazata saɓa ma umarni na ba, wacce zata iyamin tarbiyyar yarana, da duk wacce zatamin abnda kika lissafa, sadeey bansan daɗin mahaifiya ba, ina son macen da zata kula dani, ta zamemin tamkar mahaifiya"
Shiru tayi tana saurarenshi duk jikin ta yayi sanyi yaci gaba "kusan shekara ukku kenan ina fama da soyayyar ta a cikin raina, kullum nake baro unguwarmu inje har inda take cikin sanyin safiya kawai don in hanta ko daga nesa ne, na rasa hanyar da zanbi wurin bayyana mata soyayyata a tunaninah tafi ƙarfina, kuma hakanne daga ƙarshe saina zama mai mata hidima, ban tunanin zan so wata mace kamar yanda na sota"
Shiru tayi ta kasa bashi amsa saima ta tafi duniyar tunanin maganganun shamsuddeen,ba ƙaramin tasiri sukai a zuciyarta ba, kyawawan halayenshi da tunaninshi na matukar burgeta, ga kuma daɗaɗan kalamai.
Har sukaje ƙofar gida babu wanda ya ƙara Mata magana lokacin ana gaf da kiran Sallar magriba, ya Shigar mata da ledar tsarabarta har falo ya iske momma na jiransu, ta musu sannu da zuwa a gurguje ya fito don ya sami jam'i a masallaci.
Sadeey ta rakoshi har ya juya yanda zaiji tace "Yaya deen ni ƙanwarka ce, kuma ƙawar shawarar ka, basai ka faɗamin abinda ka daɗe kana ɓoyewa ba" juyowa yayi yana kallonta suka haɗa ido bata fasa magana ba tace "Ya deen zan iya zama tamkar mahaifiyarka daka rasa?.
Bakinshi ya buɗe saboda farin ciki yaa kasa cewa komi, sun daɗe tsaye a haka sannan Yace "kimin uzuri sadeey kada inyi ba dai dai ba a gabanki, zan fita daga waje inyi murnata" murmushi kawai ta bishi dashi ta shige cikin gida.
Yana fita waje ya fara tsallen murna, kamar yaro, yama rasa mezaiyi don tsananin farin ciki.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment