ABDUL WAHAB 27
©Rabiatu sk msh
®NWA
Shi kuwa Abdul yana kulle dakin ya fice daga falon ya shiga motarsa, tunani barkatai y shiga yi, to shi ynx mai xaiyi ma Sadeey ta tabbatar da cewa yana sonta? Wata xuciyar tace dashi Haba Abdul sai kace ba namiji ba? Kasan hanyoyin da xaka bi don ganin ka fahimtar da ita kalar son da kake mata. Yayi murmushi yaja motar ya fita daga gidan. Bai fi 10mnt b sai gashi ya dawo ya fito dauke da ledoji a hannunsa wanda ni kaina bn san ko miye a ciki ba.
Ya xarce cikin gidan, kai tsaye dakin da Sadeey take can ya nufa, koda ya bude dakin a kwance ya isketa saman carpet tana ta sharar barcinta. Murmushi yayi ya qarasa inda take ya tsugunna yana kallon kyakkywar fuskarta, wani irin masifaffen son sadeey ne ke 'kara shigarshi. Yamiqe ya ajiye ledojin hannunsa sannan ya dauki Sadeey ya maidata kan gado. Har lokacin bata farka ba. Nan ya xauna ya xuba mata lumsassun idanuwanshi yana kallonta har na tsawon wani lokaci sannan ya miqe ya rage kayan jikinsa ya fada toillet.
Yana fitowa ya xura jallabiyarsa sannan ya dauke ledojin ya kai cikin fridge sannan ya dawo dakin. Kan gadon yaje ya kwanta tare da jawota xuwa jikinsa. A firgice ta farka tare da fixge jikinta tace Abdul miye haka?. Sakin baki yayi yana kallonta cike da mamaki yau ita ce ke kiran sunansa kai tsaye ba ko yayan da ta saba. Ta miqe xata sauka daga kan gadon yayi saurin riqo hannunta yana cewa Ina xaki Sadeey? Ko kallonsa batayi ba ta fixge hannunta ta miqe tayi hnyr fita. Yayi saurin isa gabanta yana cewa Don Allah karki fita ki kwanta a nan ni bari naje daki na na kwanta. Bai jira mai xata ce ba ya fice tare da jawo kofar ya kulle sannan ya tafi dakinsa.
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment