```MAKASHINKA...```
23-24
©Rabiatu sk msh
Ana tashi ckul, ta hangoshi yana jiranta, anma ta shareshi sai data ɓata mishi lokaci sosae, duk en makarantar anzo ɗaukarsu, saida khadija zata tafi sannan ta tafi inda yake itama.
Fuskarta ɗaure don har yanzu bata haɗa ido dashi ba, tana kallon gefe tace "bani mukullin motan, Yace "mukullin mota kuma ranki shi daɗe? Tace "kaji abinda nace kenan? Bai mata gardama ba ya zaro ya miƙa mata, taja tsoki ta shige motar ta barshi nan tsaye.
Da karambani ta saka mukulli ta tada mota, saiku rantse da Allah daman can ta iya, wurin ta danne 'gear' ta danno 'reverse' da ƙarfi, sai dai taji mota taa fizgeta da karfi taayi baya, jikinta ya fara kyarma, ido ya raina fata, ta ƙanƙame sitiyari taa kusan kaima bangon gate ɗinsu karo ta samu ta take 'gear' ta karayin gaba da gudu duk ta fita hayyacinta, ta shiga juya sitiyari motar ta dinga juyi cikin makarantar mutane an zagaye sai kallo ake.
Hankalin shamsudden daya gama zuwa ƙololuwa wurin tashi hango masoyiyarshi cikin tashin hankali, ya dinga ɗaga murya yana faɗa mata yanda zatayi, duk ta jigata daƙyar ta iya tsaida motar.
Tana tsayawa da fito da sauri har tanajin juwa,ga
Cikinta daya murɗa, ta duƙa ta fara kwarara amai kamar mai shirin amaye kayan cikinta, nan aka shiga yi mata sannu.
A fusace kawai ta miƙe, ta tilla mishi da mukullan ta shiga bayan motar ta kame, kanta na sara mata har lokacin bata ƙarasa jin kanta dai dai ba.
Shamsudden baice mata komi ba, anma a tsorace yake da hali irinna sadeey, a darare ya shiga motar ya tada suka tafi, saida ya tsaya ya sai mata ruwan faro mai sanyi ya bata, ko kulashi batayi ballantana ya saka ran zata amsa, sai dai ya ajiye mata kusa da ita, da yake tana buƙatar ruwan ta ɗauka ta kwankwaɗa sannan ta zubama fuskarta.
Wai ita da take wahalarda direbobinta, yau wannan ne zata wahala sanadinshi daga fara aikinshi yau, lallai ya ɗebo da zafi, tohh anma miye laifinshi tunda ita tace ya bata makullan? Da sauri ta kauda wannan tunanin don koma miye haushinshi yananan cikin ranta, shima sai tasan yanda zatayi ya daina kaita makaranta.
Haka har sukaje gidan kowa da abinda yake tsarawa a ranshi, har ƙofar shiga parlon ya ajiyeta da yake mota na zuwa, ta fita fuuu cikin ƙunar zuciya, sannan ya koma da motar yayi parking.
A dinning ta wuce su momma suna launch, bata tsaya gaishesu ba ta haye ɗakinta, duk suka bita da kallo.
Toilet ta shiga ta watsa ruwa, sannan ta canja pad da yake bazatayi sallah ba, ta saka doguwar rigarta tashan iska ta fito daman kaya masu nauyi basu dameta ba.
Shamsudden ta iske tsugunne gaban daddy ya gama mishi tambayoyi, gabanta ya faɗi Allah yasa da bai faɗama daddy Abinda ya faru a makaranta ba.
Daddyn ne ya katse mata tunani "ƙaraso mana sadeeyn daddy, ki faɗamin ya makarantar da sabon drivern ki? Tayi sanyayyar ajiyar zuciya tace "komi lafiya lau daddy, yau dai bani da ƙorafi akan driver na" yace "yauwah doughter daman nasan zakiji maganar daddy"
Sai yanzu momma tayi magana tace "nifa ban yarda ba ƙara ka tambayi yaronnan, kasan halin sadeey indai akan direbobinta ne," ta kalli shamsuddeen tace "ina fatan dai bata maka halinta data saba ba, babu masifa, babu tsokana, babu ɗauke mana hankali in kana driving ko duka? Da sauri sadeey tace "haba momma....." kallonta kawai tayi, tayi shiru bata ƙarasa ba, sai dai ta fara aikama shamsudden da harara tana jiran taji mezaice.
Kanshi a ƙasa yace "duk babu ko ɗaya hajia, namaji daɗin aikinnan na yau, komi na tafiya lafiya lau," momma tace "ka faɗamin gaskia fa nasan halin yarinyar nan, daga ganinka zakayi haƙuri da ita, kowanne driver bai iyawa da halinta, kusan kullum sai an canja mata, masifaffiyah ce yarin...." daddy yace "haba, ya isa hakanan mana tunda dai da bakinshi ya faɗi komi lafiya lau," ya kalli shamsudden yace "tashi kaje, kuma ina ƙara jaddada maka daka kula da sadeey, banison ɓacin ranta," yace "insha Allah, Alhaji"
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishia)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment