[14:07, 3/14/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW📚
81-90
A rude Maryam ta duqa tana tattara wayar, Maryama tayi tsaye kamar ana hura mata wuta a qirji don sosae ta qagara taga hotan deen, Maryam ta dago da kwankwatsattsar wayar tana kallon Maryama tace "kiyi haquri namcy! Maryama ta harareta cikin wasa tace "wannan ma ay cin mutunci ne takwarah don kawai waya taa fadi harda wani bni haquri! Maryam tace "naasan ynda kka qagara kiga hotan deen ne kuma ynzu naa bata miki damarki, Maryama tace "damar ganin hotan deen kawai na rasa Maryam, anma bn rasa damar ganinshi ba! Ki bni wayanki guda in saka sim dina in kirashi cikin satinnan zamu hadu in ganshi ya ganni!
Maryam kamar tana jira cikin murmushin nasara ta miqa mata wayarta, ita da kanta ta ciro mata sim din ta saka mata, Maryama ta zaro ido ganin sim din yayi deactivated tace "na shiga uku Namcy ynzu ya zanyi muyi waya da deen? Gashi har yau naa kasa hardace numbrshi kullum mntawa nake! Maryam ta sauke ajiyar zuciah damn abnda take fargaba kenan! Ta dafa kafadar Maryama tace "karki damu takwarah zuciar deen na tare dake a koda yaushe, tunda yayi miki nisa.... Maryama ta dago idonta ta sukayi jajir sbd wani irin azaba da zuciarta ke mata, soyayyar deen taa dawo mata sabuwa fil tace "deen bzai tabamin nisa ba Maryam, b zuciarshi kawai ke tare dani ba, zuciah ta da tashi a tare suke, soyayyarshi a cikin jininah take kamar yanda tawa take yawo a jikinshi, naasan dk dadewa zamu hadu dashi, Maryam tayi murmushi tare da daga kafada Alamar maganganun maryama basu dameta ba!
Haka Maryama ta qare weekend dinta cikin qunci da tunane tunane har suka koma ckul ranar monday, Maryam kuwa ko yaushe cikin farin ciki take yini take danne dannen waya, har cikin dare saita dade bata kwanta ba!
Ranar monday dk bata cikin sukuni hkanan take sauraren lecture anma dk bata cikin tunaninta, ji tayi an jefeta da wani abu a razane ta dago fuskarta taayi zatan lecturer ne ma, suka hada ido da Ahmad ya sakar mata murmushi, itama yaqe ta maida mishi ta duqar da kanta har aka gama lecturen suka fito.
Sun jera da Maryam suna tafiya sai faman latsa waya take, Ahmad ya qaraso yasha gabnta yace "yau kuma laifin me Aboki yayi da ba'ason magana dashi? Tayi murmushi tace "wace ni ince Aboki yaimin laifi? Ynxunnan hangen inda zan ganoka nake!
Yace "ba wani in hkane miyasa kka kashe wayarki inna kira bn samu? Tace "taa lalacene har sim din! Yace "shne ko wayar maryam baki kirani da ita ba ki fadamin? Ni naayi fushi? Tace "dgsk kaayi fushi Aboki?? Yace "eeh din yana Murguda baki da murmura ido kamar wani mace! Maryama naa gumtse daria ta tabo Maryam dake latsa waya su duka suka kwashe da daria a tare! Maryam tace "Ahmad kamar dai yaaro! Yace "ayni yaronne tunda ina gabn Maryama!
Wayarshi ya ciro aljihu iphone 6+ ya cire sim dinshi ya miqa mata, tace "me za'ai? Yace kiyi haquri Abokiyah ki saka sim dinki kafin in siya miki wata! Tace "A'ah Aboki kaa siyamin waccan, ka riqe taaka dad ya turamin kudi yau zanje in siya! Yace "kyautah ce tsakanin Aboki da Abokiyah ba wai saurayinki ba da zakiji kunyar amsah ba, in kuma baki Amsa ba nasan me kke nufi da hakan! Maryama miqa hannu tana murmushi tace "naa.... ya dora hannunshi a baki yace "bnson hka Abokiyah, bbu godia tsakaninmu!
Rabiatu sk msh
[15:40, 3/14/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW📚
91-100
Da saurinta ta gama dk abnda zatayi bayan sun koma gida sannan ta koma bakin gado ta kwanta, tasha wahala kafin ta tunano numbr deen sannan tayi saving ta bude whatsapp, cikin sa'a kuwa numbr tashi ce saboda dp dinshi da kuma status nashi da koyaushe na addini ne, ba qaramim farin ciki taji ba data ganshi online da saurinta mishi sallama
Maryama:slm
Deen:wa'alaikis salam
Sai haquri pa bn gane waye ba
Maryama:ka canka da knka
Deen:fadamin kawai
Maryama:Rayuwah nada matuqar wahala a gareni idan bbu kai masoyi, kwana biyunnan na azabtu sosae da rashnka
Deen:bn gane bpa
Maryama:haba mna! Hrka mnta da masoyiyar? Maryama ce pa
Deen:bnson rainin hnkali, ga Maryama ta nan muna chat da ita, kuma yau dinnan zan gnta, don hka canza wani salon!
Kafin maryama tayi magana har yaayi block dinta, cikin tashin hnkali hawaye suka fara kwarara a idanunta, da sauri ta fara qoqarin kiranshi don tana da tabbacin deen bzai taba mnta muryarta b, cikin rashin sa'a nanma yaa sakata black list! Jefar da wayar tayi samn gado ta lumshe ido ta fara hawaye!
Maryam ce ta shgo cikin fara'a da waya a hannunta tana rera waqar nura m inuwa ta *gudun wuce sa'a* baitin da yake cewa "Murnah ake a fili farin ciki in aka sameshi, niyau na samu dai dai da zuciah wanda nake kishi, sanyin zancensa ke ratsa zuciah dajin kalamnshi! Ba mai.... turuss ta tsaya ganin Maryama dake qoqarin share hawaye, cikin Yaqe maryama tace "ci gaba mna namcy, ay naasha studio zamuje! Maryam tayi murmushi tace "kin tashi barcin knan? Maryama tace "Ehh harma naayi sallah na koma na kwanta
Maryam ta shge toilet tayo wankanta sannan ta fito, taa dade gaban madubi tana tsara kwallia, sannan ta tashi ta bude kayanta ta dade tana qare musu kallo sannan ta fara gwadawa tana cirewa dk taa watsar da kayan saman gado, maryama ta taso tace "ina zuwa hka dk kka rasa kayan da zaki saka, kamar zatayi kuka maryam tace "wlhy namcy shams zaizo na rasa shgar da zanyi! Maryama tace "waye shams kuma? Maryam tace "saurayinah mna?? Cikin mamaki maryama tace "ynzu takwarah kina da saurayi shams anma sai zaizo zaki fadamin lbrnshi??
Nan da nan zufa ta fara karyoma maryam kamar marar gsky ta fara in ina tana shafar fuska, Maryama ta dafa kafadarta tace "mnta kawai bari in tayaki zaben kayan da zaki saka! Wata hadaddiyar doguwar rigar material ta zabo mata golden taayi matuqar haduwa, Maryam ta ansa tana murna tace gsky kin iya zabe namcy bari in shrya yana sitting room yana jira, Maryama tace "tohm bari inje kitchen a harhada mishi abnda zaici, Maryam tace "so nyc ov uh takwarah, kizo da wuri ku gaisa don Allah, Tace "ba dole inzo inga jarumin namcy na ba!
Bayan taa sanya masu aiki sun gama kai mishi girke-girken da aka mishi, ta taho sai qaqaro murmushi take dk qoqarinta na son mntawa da deen, ta nufi sit rum din taa kusa kenan taji gabnta yaa bada rasss, ya fadi da sauri ta furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un, taci gaba da tafiya gabnta na bugawa da sauri
Rabiatu sk msh
|
0 comments:
Post a Comment