New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 100-110

[14:17, 3/15/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
100-105
Ta miqa hannu zata yaye labulen falon kenan wayarta tayi qara har sai data tsorata, ta duba taga sunan Aboki A hnkali ta sauke ajiyar zuciah ta koma baya, wuri ta samu ta zauna suka sha firarsu ta Abokai sannan ta tashi ta nufi sit rum din don su gaisa da shams din Maryam
Tana budewa taga babu kowa sit rum din, fitowah tayi ta shge falo ko zama batayi ba Maryam ta shgo tace "haba namcy ina kke shge inata nemnki ku gaisa? Maryama tace "Ynzunnan pa dga can nake bn iskeku ba halan ina akayi firar soyayyar? Maryam tace "kin makara ne harya tafi, anma yace bzai dade ba zai dawo! Kinsan me takwarah? Kafin Maryama tayi mgn Maryam taci gaba "wlhy namcy shams Yaa hadu da yawa, kinga wani salo da yake in yana mgn, sai in wani qara narkewa a qaunarshi, shima pa yana sonah sosae, don cewa yayi da wuri zaizo ayi bikinmu, kuma kinga mun kusan gama ckul dana gama sai aure...
Dk maganar da Maryam keyi Maryama na can duniar Tunani, ji take damn itama nata shamsuddeeen dn yana tare da ita, sai da Maryam ta gaji da surutanta taga Maryama ko kadan bata saurarta ta tabo, ajiyar zuciah tayi tace "Gsky naa tayaki Murna takwarah, Allah ya barki da shams dinki! Tace "Ameeyn namcynah!!
***
Haka shams da Maryama sukaci gaba da samu sabanin tsakaninsu, duk zuwan da xaiyi basu taba haduwah ba! Har aka sanya ranar aurenshi da Maryam bayan sun gama makaranta da 1week, Maryama kuwa tuni taa haqura da deen, Rayuwarta take kamar babu wani Abu daya taba damunta!
Yaune ranar dasu Maryama suka kammala makaranta, bayan partyn da sukasha da shagulgulan da akayi suna kwance sun baje a falo suna duba kyaututtuka, momie ta kalli Maryama tace "Ynzu maryama bzaki jira har bayan bikin takwararki ba sannan ki koma gda b? Kamar wadda ake kora dk kin qagara ki tafi ki barmu! Kanta a qasa tace "ba hka bne momie, naa dade bnje gida bne kuma kinga tun Yau nace ma su dad zan koma, Anma kwana biyu kawai zanyo in dawo a insha Allah, momie tace Allah ya yrda! Maryam tace "don hidimar bikinnan data faramun yawa Namcy ay daa tare zamuje, har Aurenah yaa kusa bn taba zuwa gidansu namcy ba 4yrs muna tare, Maryama tayi murmushi tace "bakomi wata rana ay zakizo ne, karmaa kiyi mamakin muzo tare dasu! Cikin jin dadi momie tace "da munji dadi kam!!
Washe gari tunda safe ta shrya Ahmad ya turo mata driver, Yaaso ya kaita da kanshi taqi yarda don bataso yaga gdansu, wurin qarfe biyu suka isa garin gada, yana mishi kwatance har qofar gdan gwaggo, Tace "nan zaka ajiye ni akwai saqon dazan Amsa Anjima zan wuce kadunar Yace "Tohm hajia! Ta mishi godia bayan ta miqa mishi kudi tace "yasha ruwah a hanya yanata godia ya tafi!
Gwaggo don murna taa rasa ina zata saka Maryama! Ta kawo mata wannan ta dauko wancan taa jera mata Abinci Yaafi kala biyar wanda ake kawo mata, Maryama Tace "gwaggo wannan Abinci haka ay sai cikinah yayi qaato! Nidai ki taho ki zauna mu gaisa, Tace "tohm Maryama bakisan farin cikin da nakeji bne da dawowarki, tace "nima naaji dadi gwaggo dana dawo na sameku lpy!
Qannenta ne en biyu suka shgo gdan da gudu suna rige-rige suka fada jikinta, Tace "miye hka ku kuma da har yau baku grma? Baku iya sallama bne?? Usaina tace "Yi haquri Aunty wai hassan ne yace saiya rigani tabaki, Yace "keni tsarabata kawai nazo amsa kuma data bni zan tafi in qyaleki!
Maryama tace "tohm dk ku jirani in shrya mu tafi gdan can zan baku tsarabar, sukace "Tohm Aunty.
Kwananta biyu a qauyensu ta shrya ta koma kaduna da Tunanin maganar da babnta ya fada mata "Tunda kin qarasa makaranta ki tabbatar kafin ku tafi bautar qasa kin fiddo miji! A ranta tace tohm ni daba saurayi ba ko wanne miji zan fiddo??
Rabiatu sk msh
[16:09, 3/15/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
106-110
Tana dawowah katsina suka ci gaba da shrye shryen bikin Maryam da shams! Bata da lokaci kullum cikin hidima suke, kuma har Yau bata taba ganin wannan deen na Maryam ba.
Tun daga ranar tuesday suka fara da wasan ball, Ranar wednesday kuma Arabian day! Da dare sai shri suka cikin dogayen rigunansu baqaqe, Auntynsu Maryam ce ta shgo tace "wai en matannan bzaku fito hkanan ba kunata jama Abokan Ango lokaci?? Maryama tace "Aunty dk gasunan suna fitowa mudai munanan sai mun gama shrya Amarya! Tace "kaaji maryama keda bake ke mata kwalliar ba? Maryam tace "Ay wlhy babu inda zata tafi Aunty saitaa jirani! Ta kalli sauran qawayen tace "tohm ku fito don Allah!
Motah daya Maryam da Maryama suka shga, tun a hanya gaban Maryama ke faduwah har suka qarasa gabanta naa ci gaba da matsanancin bugu! Maryam ta kalleta tace "yadai namcy? Maryama tace "gajiah kawai! Maryam tace "tun ynxu? Aikam qara ma ta sake ki tun wuri, namcy Yau dai zaku hadu da shams! Tace "Eeeh pa Yau xanga wnda ya sace zuciar takwaratah! A haka suka qarasa hall din sunata firar shams-deen
Suna zaune cikin motah Maryam tace "bzamu fita ba sai shams Yaaxo kun gaisa, kafin Maryama tayi magana Yaa bude motar gefen da take zaune Yana cewa Amaryar tawa saita wahalar da Angonta? Tsoro taji sosae gaa faduwar gaban da taji taafi ta ko yaushe! Shima tsayawa yayi yana kallon fuskarta da hasken fitilar Yaa kasa motsawa!!
Maryam ce ta katsesu da kallon juna dk hankalinta a tashe ganin irin kallon da suke ma juna cikin in ina tace, Masoyi ga qawatah kuma takwaratah Maryama, Yayi murmushi yana shafa qeya Yace Yau dai gani ga Maryama! Tayi murmushi ta sadda kai saboda Yanda lokaci guda Yanayinta ya canza
Dk sukuku Maryama take wurin partyn nan sbd irin kallon da shams Yake mata, taa kasa sukuni dk inda ta tsaya sai taji jikinta na bata ana kallonta A hka har Aka tashi suka tafi gida dk bata cikin nutsuwarta!!
Rabiatu sk msh
May 29 at 7:05am · Public

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 31-32[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts