```MAKASHINKA...```
17-18
©Rabiatu sk msh
Kwananta biyu bata kula wayarta ko saƙo yaa shigo, ko kiranta akai tunda ta lura ko kasheta tayi tana kunnuwa, duk inda zataje komi zatayi da madubi a hannunta
Ya Anwar kuma taa daina sakashi a idonta, itama batason haɗuwa dashi saboda abinda yayi niyyaryi mata, ita damuwarta kawai yanzu tasan waye masoyi? Mutum ne ko aljan?
Momie ta katse mata tunani wajen dafa mata kafaɗa, da sauri tayi firgigit tare da juyowa tana kallonta ta cikin madubi, saida taga momie ce sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da ajiye madubin.
Momie ta zauna kusa da ita tana murmushi tace "lafiyanki kuwa sadeey? Meke damunki kwanannan dukkin canja, yanzu wannan madubin da kika tsiri yawo dashi me kkeyi dashi? Tace "bakomi momie, kawai ina yawan duba fuskata ne" momie tace "da dube-duben duk inda zaki zauna ta cikin madubi ba," sadeey tayi murmushi tace "hakane momie, akwai abinda ke damun rayuwatah ne" nan ta kwashe komi ta faɗa ma momie cikin nutsuwa.
Momie ma duk da taa girgiza, anma maganganun sadeey daria ma suka bata, tace "wannan kuma ay shirmene, ita kuma khadija ta biye miki harda cewa ki dinga duba madubi koma wacce irin halitta ne zaki ganshi? Wannan shirmeni shiyasa kikaga Abbanki baya so kina kula kowa, bayason kina fita ko ƙofar gida, kin san dalili?
Sadeey ta girgiza kai da sauri tana jiran ƙarin bayani daga momie, anma saita canja maganar da cewa "tunda kike duba madubinnan kin taɓa ganin wani abu? Sadeey tace "A'ah" momie tace "don haka ki fidda tunanin wani masoyi a ranki, wata ƙila ma hasashene kawai kike kina tayarma da kanki hankali, sadeey tace "tohm momie"
Sannan ta ɗauko madubinta cikin sanyin jiki tana kallo, zumbur ta miƙe hango mutum ya juya bayanshi dai dai ƙofar fita daga falon, ta juya da kanta ba tare da madubinba ta kalli ƙofar falon bataga komi ba, sannan ta ƙara kallon madubin, har lokacin yananan tsaye sai dai lokacin ya buɗa ƙofa ya fita.
Da sauri take cema momie ta taso ta gani, anma kafinta taso ya fita, cikin ruɗewa take cewa "wlhy dgsk ne momie, Allah na ganshi, banga fuskarshi bane anma Allah yau na ƙara ganin masoyi a cikin madubinnan,"
Momie tace "kinga ni rabani da wannan shirmen naki, dole ne in faɗama Alhaji wannan abun tun wuri ayi mishi tufkar hanci, a gabana dukkin wani susuce akan wani masoyi? Sadeey tace "nidai don Allah momie ki yarda ki barni in koma police station in nuna musu hujjata, su tabbatar da ba hauka nake ba, yau na samo hujjar dazan basu su rabani da masoyinnan tun kafin in sanshi ma, saboda ni ya takuramin"
Momie ganin kamar sadeey ba cikin hankalinta take ba ya sanyata buɗa baki tana kallonta kawai, anma jin sadeey so take a rabata da masoyi ya sanyata cewa, "shikenan ki jirani in shirya muje, don bansan me zancema babanku ba idan ya dawo ya tarda na barki kin fita, gashi anwar kuma bayanan" cikin zumuɗi da ƙosawa tace "don Allah momie mayafi kawai zaki ɗauko"
Suna isa police station tun kafin driver ya ida gyara parking motar da suke ciki da momie ta fita, har gaban mai ɗaukar statement da madubinta a hannu take cewa "yau dai na kawo maka hanyar da zaka kama masoyi" duk mutanen dake ciki suka tsura mata ido saboda wasu sun ganeta.
Yace mata "ta yaya? Ta nuna mishi madubin, duk suka kwashe da daria lokacin momie ta shigo, yace "ayni nan banga komi ba, ko kina nufin madubinne masoyi? Tace "ba madubi bane masoyi, anma zaka iya ganinshi ta cikin madubi, yana da matuƙar hatsarin gaske, har ƙoƙarin kashemin yayana yayi, kamar yanda shamsudden ya kashemin yayana da mahaifana.
Shru sukayi jin ta ambaci shamsudden ɗin daya kashe mata yayanta da mahaifanta, kusan duk police station ɗin dake ƙasar nigeria kaɗanne basu san da neman da akema shamsudden ba shekara biyar ana nemanshi, da duk kafafan yaɗa labarai, ga kuma shigowar momie matar Alhaji muhammadu da babu wanda ya kaishi kuɗi a duk jahar kano, ga kamfanoni da dama harda ƙasashen waje, kuma shine ya sakasu nemo shamsudden ɗin.
Hankalinta yaa tafi can tana zagaye station ɗin da madubi tanaso taga inda masoyi ya maƙale ta nuna musu shi, A hankali kamar raɗa taji a kunnanta maganarshi.
```idan har kinason ganina, basaikin wahalar da kanki ba, ki tsaya yanzu zan bayyanar miki```
Kamar wadda aka cire ma lakka, ta tsaya cak ƙwalwarta na yawo, nan ta fara ayyanama ranta ko muryar waye, don koda a cikin mafarki ne bazata taɓa manta muryar da taji ba, a hankali ta ƙurama madubin ido.
Jininta bai gama tsinkewa ba saida ta hango suffarshi bayyane a cikin madubin, murmushi yayi tare da ɗaga mata gira, ta kasa ko motsi kamar wacce tayi suman tsaye.
Kamar ku masu karatu, nima tunani nake waye masoyi? Wanene idon sadeey ya gane mata? Ƙyallara idona nake ina dogon wuya duk ƙoƙari na nason leƙa madubin inga wanene, a hankali ta sakeshi ƙasa ya tarwatse, sannan ba tare da buɗa baki ba cikin rawar laɓɓa tace
"SHAMSUDDEEN ne masoyi momie" sannan ta sulale ta faɗi ƙasa.
Wanene shamsudden? Yanzu zakuji komi daga bakin sadeey.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishia)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment