New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 15-16

```MAKASHINKA...```
          15-16

©Rabiatu sk msh

Tunda ta dawo daga rakiyar khadija take ta zagaye falon tunani da yawa cunkushe a zuciyarta.

Da dare ta kwanta, bata samu barci ya ɗauketa ba, sai dai rufe ido da tayi kamar mai barci, tana ci gaba da ƙoƙarin kawar da tunanin daya hanata barcin.

Jin ƙarar buɗa ƙofa tayi, a hankali gabanta ya fadi, tare da tsananta bugu sanda taji an kunna fitilar ɗakin, a hankali ta kanne idonta ɗaya ta buɗa ɗayan tana tsananta addu'a a cikin ranta.

Hangoshi tayi yana tahowa inda take a hankali cikin sanɗa, duk jikinta ko ina rawa take taama rasa me zatayi, har ya ƙaraso inda take ya haye saman gadon tanajin matsowarshi a hankali.

Hannunshi ya ciro ya miƙashi ya fara yaye bargon data lulluɓa dashi, rufe idonshi yayi ya buɗe, sannan ya ƙara matsawa ya kwanto dai dai inda take, miƙa hannunshi ya ƙarayi da nufin sake taɓata.

Kamar wanda aka tilla yayi baya ya bugi bango tare da dafe kanshi, da sauri ta buɗa ido ba tare data buɗe ba, hangoshi tayi jikin bango kamar wanda aka maƙure, an cimimiyi rigarshi yana kakari kamar wanda aka shaƙema wuya sai ƙoƙarin ƙwacewa yake ana buga kanshi da bango, nan take jini ya fara fita ta hanshinshi, sai da yasha wahala sosae daƙyar ya iya ƙwacewa ya fita daga ɗakin a guje.

Barcin daya gagareta kenan, daga ita sadeeyn har yaya Anwar ɗin sun shiga firgici, da sauri ta miƙe data tuna da shawarar da khadija ta bata, ƙaramin madubi ta ɗauka saman mirrow ɗinta, ta fara kallon ko ina ta cikin ɗakin ta cikin madubin bataga komi ba.

A hankali ta hango motsi cikin labule, ta fara tafiya a hankali har inda taga motsin da karfi ta yaye labulen bataga komi ba, sai dai manyan rubutu da aka rubuta da jan abu.

```babu Anwar cikin lissafin wanda zan kashe, anma idan har yaci gaba da shige miki shima zai iya shiga cikin lissafi, ke tawa ce ni kaɗai, ni MAKASHI NE, a kanki```
              ~masoyi~

Wannan karon tsoronta yafi yawa, toh su waye zai kashe? Meya saka zai kashe su? Waye masoyi? Zaman dirshan tayi duka hannunta taa ɗaura kumatunta akai, haka daren ya ƙare ba tare data samu runtsawa ba.

Da safe
Anwar ne a ɗakin Abba, duk suna zaune Abba da momie shi kuma yayi tsaye da alamun ɓacin rai a fuskarshi cikin ɓacin rai yake faɗa, duk fuskokinsu kamar masu shirin kuka suke lallaɓashi.

Abba yace "haba Anwar! Idan bakai ba wazaimin wannan? Kai kaɗai ne na haifa, banson sadeey ta ƙara saka wani ɗa namiji a ranta idan bakai ba, sai kace yau ka fara soyayya? Mace bazata taɓa maka wahalar shawo kai ba....

Anwar ya ɗaga ma Abba hannu yace "banda sadeey, ita wannan aljanune da ita Abba tafi ƙarfina, don kaa gaji danine kawai kake nema ka sakani cikin matsalanka, akan wani burinka wanda ni bazai amfaneni ba...

Momie tace "idan bazai amfaneka ba anwar wazai amfana? Burin Abbanka ne na shekara 5 donme bazaka cika mishi ba ynzu da lokaci yayi? Abba yace "kuma kaaga ni babu yacce za'ay na aureta don ni matsayin mahaifinta nake, babu ta yanda burina zai cika har saika aureta.

Sadeey ce ta turo ƙofa ta shigo tare da sallama duk sukayi shru suka tsura mata ido, kanta a ƙasa ta samu wuri ta zauna saman carpet, tace "ashe duk kunanan momie? Tana satar kallon anwar da duk da baisan tasan abinda ya faru ba tsoranta yakeji.

Da sauri ya juyar da fuskarshi cikin sa'a wayarshi tayi ƙara, da hanzari ya saka hannu aljihu saboda sauri da ruɗewa ya zaro keys ɗin motarshi ya kara a kunne baima sani ba sai hello yake, momie tace "ay ba wayar bace ka ɗauko" sannan ya zaro wayar ya fita da sauri tun kafin ya ɗauka ma taa katse.

Duk suka dawo da kallonshi da suke, sannan ta miƙe a hankali ta fita bayan ta gama gaishesu da alama duk jikinsu yaa gama sanyi, tace "tohm meke faruwa a gdannan? Kodai ya anwar ya faɗa musune? Anma ay zaiji kunyar faɗa musu.

Tana fita har rige rigen cewa "taaji abunda muka ce? suke, momie tace "ban tunanin hakan gaskia" Abba yace "gaskia sai muna bin komi a sannu" kinga yanzu saura 2mnth birthday ɗinta na 23yrs, dolene muci gaba da lallaɓa Anwar, momie tace "hakane fa"

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishia)

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts