ABDUL WAHAB 19
©Rabiatu sk msh
®NWA
Bayan an gama sanya mata kaya a mota, fatyma kaasa rakota tayi saboda kukan tausayinta, kamar wacce zata bar garin, sosae hajiya da fatima kejin tafiyarta, saboda sadeeyn akwai saurin sabo, sau'kin hali ne da ita, babu abinda ke 'bata mata rai, duk inda ta shiga kowa nata ne, da wuya ka zauna da ita bakayi dariya ba.
Itama hawayen take, tana tafiya tana 'karema gidan kallo, tabbas bazataji dad'in barin gidan ba, anma yaa zame mata dole, inda motar ta take ta iske Abdul a tsaye, da sauri ta fara 'ko'korin maida hawayenta tana nemo murmushi, don koda abunnan ya faru bata canja mishi ba, sai dai bata wani doguwar magana dashi kota tsaya inda yake, duk da shima bai cika zaman gidan ba.
Fuskarshi ba walwala yace "ya akai naga an fito da motarki? Sadeey tace "kawai kwana biyu bata fita bane zan fiddata tasha iska, Yace "kayan dake ciki fa? Tace "zan kai wanki ne, sauran kuma sun gaji da zaman gida suma zan fita dasu susha iska.
Abdul ya girgiza kai Yace "kin cika wasa sadeey, komi naki bakiyinshi crioz, yanzu hajia ta kirani a waya wai yau zaki koma gida, wani abu aka miki?
Yarfa hannunta tayi tana kallon kasa tace "nikam me za'amin yayanmu? Anmafanin zaman gidan nawa ne ya 'kare, tabbas kaa cika d'aukar komai nayi wasa ne shiyasa soyayyata ma duk kake d'auka wasa ne, ko Sona ne bakayi?
Zaiyi magana ta rigashi tace "tabbas sona ne bakayi tunda gashi yanzu kaa samo wacce kakeso, don na tabbata ina gidannan kuka had'u da ita kuka fara soyayya, kenan banda wani mazauni a zuciyarka? So da yawa zukatanmu basu cika kamuwa da soyayyar wanda ke sonsu ba a lokacinda ya dace, bazance baka cancanci soyayyata ba, kuma bazan tabayin dana sanin son da nake maka ba, anma na ha'kura dakai yayanmu, ina maka fatan Alkhairi dakai da wadda ka zaba a matsayin Abokiyar rayuwarka,
Tana fadin haka ta bud'a mota ta shige, ko motsi yaa kasayi da'kyar ya iya matsawa taja mota ta wuce, kalaman sadeey sun sanyaya mishi rai matu'ka, sai yanzu ya gane duk maganar da zatayi ta hankali ce da nutsuwa, duk maganganun da tayi suka dinga mishi yawo a 'kwalwa, dakyar ya iya jan 'kafafunshi, ya isa cikin gidan, a falo jan 'kafarshi kawai yake yana hanyar d'akinshi hajia ta kirashi.
Juyawa tayi ya nufi d'akinta yana fargabar maganar da zata mishi, da kuma amsar da zaya bata.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk mashi❤❤
0 comments:
Post a Comment