New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 33-34

```MAKASHINKA...```
          33-34

©Rabiatu sk msh

Wani Yammaci shamsuddeen da sadeey na zaune a gefen wurin wasa a harabar gidan.

Wasa take da yatsun hannunta tana yawan satar kallon Shamsuddeen, yaa wanku cikin ƙananan kaya da suka Amshi jikinshi, sumarshi taa kwanta baƙa wulik, da ɗan sajenshi a gefen fuska dake ƙara mishi kyau.

Wani irin farin ciki takeji a duk sanda take kallon fuskarshi, cikin sigar jan hankali tace "Ya deen baka bani amsata ba, duk da nasan har abada bazan iya biyanka ceton rayuwata da kayimin ba, anma zanji daɗi naayi maka abinda zai saka farin ciki kamar yanda ka sakani.

Murmushinshi yayi mai kyau "ki share kawai sadeey" maƙale kafaɗa tayi "nidai ka faɗamin koma me kakeso"

Girgiza kai yayi "Rashin faɗin Yafi amfani sadeey, don nasan bazaki iya yimin ba" tace "meyasa? Koma miye zanyi maka" Yace "banso in matsa miki ne, kinga matsayinmu ba ɗaya ba..."

Ɗaura hannunta tayi a saman laɓɓanta "Shhh! Matsayi ɗaya nake ɗaukarka da Ya shaheed, karka ƙara faɗin matsayinmu ba ɗaya ba, nidai ka faɗamin nidai"

Yace "Shikenan zan faɗa miki" tace "Yauwah! Ina jinka Yayana" ƙwayar idonta ga tsurama ido, saboda yanason ya kalli yanda zata ɗauki maganar.

"Kin tuna tambayar da kikaimin a wannan daren kafin faruwar wannan Al'amarin? Shru ta ɗanyi tana so ta tuna, yaci gaba da kallon cikin idonta.

Juya idanunta tayi cikin salo sannan tace "ina ka tsaya a karatunka? Ya girgiza kai "kin kusa dai"
        "A ina kake zaune? Yace "ƙwarai ma kuwa, ban baki amsarta ba, Abu ɗaya dai nakeso kimin, zanyi farin ciki sosae a kan hakan" tace "ka faɗi kawai" yace "i...na...so...ki bani aron ranarki ta gobe kawai, muje kiga gidanmu, kiga iyayena, kiga inda nake zaune"

Shiru tayi saboda yanda gabanta ya fara faɗuwa farin ciki ya cika mata zuciya jin maganar daya fara, lokaci ɗaya kuma tunaninta ya tsaya jin ba abinda take tunani ya tambayeta ba, shiru tayi tana tunani, kaɗa mata hannuwa yayi sannan ta dawo daga tunaninta.

"kin gani ko? Daman na faɗa miki bazaki iya ba, shiyasa tun farko na faɗa miki basai kinmin komi ba, nima wani irin tunani ne dani, taya kawai zakije gidanmu? Shikenan kawai, karkiji ba daɗi, mu bar maganar" da sauri tace "A'ah Yaa deen, zanje"

Murmushin jin daɗi yayi "da gaske sadeey" tace "da gaske yayana" "nagode sosae sadeey" girgiza kai tayi "nima jin daɗina ne"

Sun ɗanyi fira sannan tace "bari inje in ƙara duba littafaina" Yace "badai kina nufin harkin gaji da fira dani ba? Kamar dai kanki aka fara waec" tace "ba haka bane Ya deen, nasan yanzu zaka koreni na tafi inyi karatu ne, Anma idan yanda zuciyatah keso ne ay in ƙare rayuwatah ananma tare dakai" Yace "kin faɗa dai iyakar bakinki ta tsaya, kije kiyi karatun nima bari inje yima ƴan gidanmu Albishir ɗin zuwanki" daria tayi "tohm sai goben"

Washe gari...
Tun da wuri ta Shirya, ɗakin momma ta zauna tana jiranshi sai zumuɗi take, sai duba wayarta take taga ko yaa kira.

Momma tace "kika shirya da wuri, keda bai faɗa miki bama lokacin da zaizo" tace "Da wuri ne momma, don inaso in daɗe tare da ƴan gidansu"
    "Tohh ay saiki jira yazo, sarkin zumuɗi"

Ƙarar tsayawar Mashin taji dai dai inda shamsuddeen ke ajiye mota idan zasu fita,  ta miƙe da rawar jiki zata leƙa, sai kuma ta fasa tace ƙila dai ba shamsuddeen ɗin bane.

Can ta jiyo sallamarshi a falo, nan da nan ta faɗaɗa fara'arta, jikkarta ta ɗauka da gyale a hannu, "Saimun dawo Momma" binta momma tayi da kallon mamaki tace "Saƙon nawa ma baki tafi musu dashi ba ko?" dawowa tayi tana daria tace "kuɗin da daddy ya baki ki ajiyemin ma tun ɗazu nake cewa ki ɗaukomin momma saida kika bari naa manta" tace "ay gashi na tuna miki"

Ta ɗauko ta miƙa mata tare da saƙon da zata kai musu, tare suka fito ta musu fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya, tare da jaddada musu su isar mata da gaisuwa.

Yana gaba tana biye dashi har suka fito, dubawa tayi bataga motan ba ta ɗanyi gaba zata wuce Yace "mu tafi ko? Kallonshi tayi tana dube dube tace "a ina? Yace "A saman mashin ɗinnan mana"

Zaro ido tayi tace "Ayni ban taɓa hawan mashin ba, banma iya ba" dariya ta bashi yanda yaga taayi yace "bafa koyo akeyi ba, yau saiki fara, zakiji daɗinshi" tsayawa tayi dai taa kasa hawa Yace " ki yarda dani, zamufi jin daɗin tafiyarnan a saman mashin" Matsawa tayi a hankali sannan ta runtse ido ta dafashi tahau mashin ɗin, ya bashi wuta suka tafi"

Duk jinta take kamar zata faɗo duk da a hankali yake tafiya, duka hannuwanta biyu ta saka ta riƙe kariya kamar wacce tazo daga ƙauye, ji tayi kamar itama lilo take batasan sanda ta ɗaura duka hannuwanta saman shamsuddeen ba, rufe idonshi yayi a hankali saboda wani yanayi daya ziyarceshi, ya kasa ce Mata ta ɗauke hannunta, duk jikinshi yaa canja a kasalance yake tuƙa mashin ɗin.

Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 23ABDUL WAHAB 23 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Hidimar bikin fatima kawai ake, kullum basu da zama, shirye shirye kawai suke da tsarin yanda bikin zai kasance, ga rabon i.… Read More
  • ABDUL WAHAB 27ABDUL WAHAB    27 ©Rabiatu sk msh           ®NWA                 Shi kuwa … Read More
  • ABDUL WAHAB 25ABDUL WAHAB 25 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Da'kyar ta share hawayenta, ni'kab dinta ta ciro ta maida, kanta na 'kara tsananta mata ciwo kamar zai rabe biyu Haka ta fit… Read More
  • ABDUL WAHAB 24ABDUL WAHAB 24 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Ranar d'aurin aure, sadeey ta daure ta shirya tunda safe saboda yanda fatima ke fushi da ita ta'ki zuwa bikinta, taa riga ma… Read More
  • ABDUL WAHAB 26ABDUL WAHAB 26 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A firgice ta farka, tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un, du'kar da kanta tayi yaa daina mata ciwo, fara tariyo d… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts