```MAKASHINKA...```
25-26
©Rabiatu sk msh
Shamsuddeen zaune ya haɗe fuska wuri ɗaya, ranshi a ɓace yake kallon hafeez dake ta dariyarshi hankalinshi kwance harda hawaye, don tsananin dariya har sai da ya sauka daga saman bencin da suke zaune ya duƙe ƙasa, yanaso yayi magana anma daria taci ƙarfinshi.
Shamsuddeen yace "banson iskanci fa hafeez, zaka dainamin dariyarnan ko saina baka wuri? Ya miƙe yana shirin tafiya hafeez ya riƙoshi yana ƙoƙarin shanye dariyarshi yace "duk bata kai haka ba, abin dariyar shine, masoyinda ya daɗe da soyayya a ranshi da kuma burin mallakar wacce yake son, sai gashi yaa ƙare da zama drivern ta"
Shamsuddeen tsoki yayi yace "kana tunanin idan zan ƙare rayuwata a matsayin bawan sadeey zan damu? Banda shirin yi ma sadeey ƙarya hafeez, nafiso ta soni a yanda nake talakkana, kamata yayi ka tayani da addu'a da fatan alkhairi, wata ƙila Allah ya nufa ta wannan hanyarne zan samu in bayyana mata soyayyata.
Hafeez yace "hakane Abokina, Allah ya shige maka gaba, ya sanya ka samu soyayyar sadeey, sannan ya miƙa mishi hannu suka tafa "ina tayaka murna da aikin daka samu" inji hafeez kenan.
Haƙuri shamsuddeen yaci gaba dayi da halin sadeey, babu abinda ta canja saima sabbin halaye data dinga tsirowa dasu, ganin haƙurin shamsuddeen nema da nacinshi ya saka ta ƙara tsanarshi.
Wata rana ya ɗaukota daga makaranta bayan ta gama mishi wulaƙancin data saba, suna tafiya ta juyar da kujerar da yake zauna tana daga baya, ta yanda a duƙe ma yake driving ɗin yaa kasa mata magana, kawai sai yayi parking gefe ɗaya ya tsaya.
Ta zuba mishi manyan idanunta kyawawa masu ƙara jan hankali namiji cikin masifa tana kallonshi, "badai kaace bazaka gaji ka daina kaini makarantarnan ba? Kaci gaba da driving ɗin haka in gani mana" ta murguɗa baki ta juya kai tana karkaɗa ƙafa.
Shi yanzu dariya ma take bashi komi zatayi, hakanma ƙara burgeshi yake, Yace "yanzu kiyi haƙuri ranki shi daɗe in kaiki gida, bayannan duk abnda kikeso inyi miki zanyi" tayi fari da ido tace "kaafi kowa sanin abinda nakeso ay, ka faɗama daddy ka haƙura da kaini duk inda zanje, kona samu nim ya saka a fara koyamin mota kamar sauran ƙawayena"
Yace "idan fa zan koya miki? Tsayawa tayi da yatsina fuskarda take farin ciki ya fara bayyana a fuskarta da sauri ta gyara zama "don Allah da gaske zaka koyamin? Yace "zan koya miki harki iya, idan Abbanki ya amince daki fara jan mota da kanki, shikenan sai in ajiye aiki na"
Ta ɗan ɓata rai tace "Anma ay Abba bazai yarda a koyamin mota yanzu ba" yace "saimuƙi sanar mishi mana" cikin jin daɗi tace "yauwah yayi sosae" yace "anma dai da sharaɗin zaki saki jiki mu dinga fira," ta ɗan mintsini kafaɗarshi cikin wasa, duk da haka saida yaji wani irin shock tace "daga yauma mun zama Abokai" cikin jin daɗin ya fara samun nasara yaja mota suka tafi.
Da murnarta ta shiga gidan tana tsalle-tsallenta, tana tafiya tana cilla jikkarta.
Haɗaɗɗiyar ƙofar ɗakin yayanta shaheed ta hango kamar a buɗe, fasa shiga ɗakinta tayi ta dawo da gudu ta shiga ɗakinshi ko sallama bata tsaya yi ba, ya gama saka kaya kenan ta faɗa jikinshi ta baya ta rungume.
Ya juyo yana cireta daga jikinshi da murmushi a fuskarshi yace "my little sista, sai yanzu zaki dawo tun ɗazu nake duba agogo har lokacin dawowanki yaa shige? Tace "tohm ay baka faɗamin zaka dawo ba, da ko ckul ɗinma bazanje ba" yayi murmushi tare da jan hancinta yace "nasan hakan, shiya sanyama ban faɗa miki ba"
Tace "ba komi ay kaine kayi rashin speacil girkin da naketa so na maka,"
"haba ƙanwata, ban sani ba ay dana faɗa miki, saboda ke fa na dawo weekend ɗinnan"
Tayi er dariya "shikenan naji, bari na ciro kayan makaranta in dawo akwai labarai, dana daɗe ina tanadar maka" yace "ina jiranki a ɗakin momma"
Ita kaɗai tace a ranta "Allah sarki yayana, Allah ya barni dakai dasu momma" don ba ƙaramin shaƙuwa bane a tsakaninsu, shne ɗan uwanta, abokin shawararta, abokin firarta da kuma yawonta, duk sanda yazo weekend ba ƙaramin farin ciki takeji ba, tana son mutane ukunnan fiye da komi a duniyarnan, mommanta, daddy da kuma yayanta shaheed.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment