ABDUL WAHAB 38
©Rabiatu sk msh
®NWA
Tun daga ranar ta koma rufe 'kofarta da makulli ta barshi a jiki, bata fitowa ko falon d'akinta sai Abdul bainan, ta koya ma kanta zaman d'aki don dole.
Abubuwa sun farama Abdul yawa, ya rasa hanyar shawo kanta, duk wasu shawarwari da Raheem ya bashi sun 'kare sai ya jiyo 'kamshin nasara kuma Abu ya juye, gashi yanzu baijin zai iya rabuwa da ita.
Yau yaayi niyyar kawo 'karshen Abin, 'kin fita yayi office ya zauna gidan yana gadin fitowarta, ko 10 batayi ba sai gata ta fito, hanyar kitchen ta nufa, saida tayi tsakiyar falon sannan ta lura dashi.
Da sauri ta juya zata koma, ya tashi ya rigata shan gaban, Murmushi yayi yace "yau dai naa kama mai guduna! Gefe 'daya ta maida fuskarta ko kallonshi batayi ba.
Juyawa tayi zata koma kitchen din, hannunta ya ri'ko ya juyo da ita, cikin ɓacin rai take mishi magana, "ka sakarmin hannu," Yace "magana nakeso muyi ki bani lokacinki kaɗan.
Batace komi ba tayi fuska ta tsaya yace "don Allah sadeey ki faɗamin koma miye zan miki ka gane sonda nake miki, wallahi koma miye naayi alƙawarin zanyi, tace "kaa tabbata koma miye zakayi?
Da sauri yace "zanyi wlhy koma miye, Alƙawari nayi miki, tana taɓe baki tace "ka bani takardar saki kawai in tafi gidanmu, nan danan damuwa ta mamaye fuskarshi, yace "banda wannan babu wani abin sadeey? Ki zama mai tausayi mna, wannan yaamin tsauri da yawa.
Tace "kawai ka faɗamin ba sona kake ba ay nasan da hakan, ka bani wuri in wuce tunda bazaka iya cika alƙawari ba, Yace "zan cika sadeey, wlhy zanyi duk abnda zai sanyaki farin ciki, in har hakan zai tabbatar miki da son da nake miki.
Juyawa yayi hanyar ɗakinshi ta tsaya tana kallonshi duk tayi sukuku, tananan jikinta duk yayi sanyi ya dawo ɗauƙe da takarda da biro.
Zama yayi ya rubuta mata takardarta, sannan ya miƙe idonshu jawur ya kasa ɓoye damuwarshi, hannunta na kyarma ta amsa daƙyar tana kallonshi, juyawa kawai yayi da ɓacin rai yabar gidan.
Kasa ɗaukarta ƙafafuwanta sukayi, daƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna saman kujera, tagumi tayi kamar ta fashe da kuka takeji.
Kasa barin gidan tayi kusan awa biyar, taa kasa buɗa takardar ta karanta, ganin hakan bazai mata ba ta tafi ɗakinta, ajiye takardar tayi tana ta kallonta zuciyarta cike da dana sani, ji take daman Abdul wahab ya dawo yace tunda bata karanta ba yaa fasa.
Wayarta ta nemo ta kunnata, messages suka dinga shigo mata, jikinta ba ƙwari ta shiga na fatyma tana duddubawa, saina ƙarshenne ya sanyata buɗa idanu cikin tashin hankali take kallon wayar.
A firgice ta maimaita yayanmu yayi accident yana asibiti? Na shiga uku na jawo ma kaina, yayar mayafinta kawai tayi ta fito anan ta saki kamar zararra ta fito daga gidan.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment