ABDUL WAHAB 39
©Rabiatu sk msh
®NWA
Tafiya kawai take tana jefa ƙafarta harta fito daga gidan, batasanma unguwar ba ta tsaya tana kallon hanyar da zatabi ta gano titi, saida ta koma ta tambayi mai gadinsu sannan ta tafi.
Mai napep ta tsaida ta faɗa mishi asibitin dazai kaita, duk da ruɗewar da tayi bata kasa ganin canjawar da garin yayi ba, sai kalle-kalle take, cikin zumuɗi duk taa ƙagara su isa asibitin taga halin da Abdul wahab yake ciki.
Dubu ɗayane hannunta, ta miƙa mishi kawai ta ƙara gaba, tunanin ɗakin da yake take, gashi taa baro wayarta haka ta dinga zagaye asibitin taa rasa inda zata nufa, canta tuna sannan ta nufi emergency.
Likita ta hango naa fitowa daga wurin ta ƙara sauri ta isa inda yake, tace "likita! Likita!! Patient ɗin da aka kawo bada daɗewa ba, don Allah shi nakeson gani? Yace "ya kike dashi? Tace "mijinah ne" ya sunanshi? Tace "Abdul wahab, wani fari haka yana da....!
Dakatar da ita yayi ganin tana bayani duk cin ruɗewa yace "tambayarta, da sauri ta juya, hango fatima tayi taa juya baya, da sassarfa ta ƙarasa inda take tace
"fatyma ya jikin Abdul? Fatyma tace "ya kike sadeey? Yaushe kikazo nan? Tace "manta dani ki faɗamin ya condition ɗin yayanmu yake? Tace "ki share yayanmu kawai sadeey ki faɗamin ya kike? Girgizata tayi tace "miye haka fatyma? Ki faɗamin ina yayanmu yake.
Fatyma tace "kin damu dashi ne har haka sadeey? Duk wani hali da yake ciki kene sila, kamata yayi kiyi murna tunda yaa tafi yaa barki," ban taɓa tunanin dalilin aurenki yayanmu zai iya samun damuwar da zata sa mishi ciwon zucia ba.
Faɗawa sadeey tayi jikin fatyma tana wani irin kuka, sauke numfashi fatyma tayi ta dafa bayan sadeey tace "wannan kukan da kikayi ya sanya kin goge laifinki a wurina, share hawayenta tayi tace "muje ki ganshi.
A ƙofar ɗakin da aka kwantar dashi kabir ne kawai, tace "su hajia da mami basu zoba? Fatyma tace "suna hanya, sannan suka shiga ɗakin shi da raheem ne kawai.
Da sauri ta ƙarasa inda yake, kwance yake jikinshi, kayanshi duk jini, ga wani dake fitowa daga bakinshi, sai maida numfashi yake daƙyar, faɗawa tayi jikinshi ta saki wani irin kukan tausayinshi da tausayin kanta.
Jijjigashi ta farayi tana faɗin "ka tashi don Allah yayanmu, karka tafi ka barni cikin damuwa da tsanar kaina, ka yafemin don Allah ka tashi muyi rayuwarmu cikin farin ciki, wayyo naa shiga uku naa cutar da masoyinah, kaa koyamin rayuwa dakai, mutuwa zanyi idan har baka tare dani, don Allah ka buɗa idonka in nemi gafararka mijina....
Sambatu kawai take ita kaɗai, tana jijjigashi, kwantar da kanta ta ƙarayi saman ƙirjinshi, tana shessheƙar kuka, ji tayi yaa ƙara matseta a ƙirjinshi, yaa ɗaura hannu saman kanta, ya saki wata roba da wani abu ke ciki kamar jini zumbur ta tashi zaune tana kallonshi.
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment