```MAKASHINKA...```
19-20
©Rabiatu sk msh
WANENE SHAMSUDDEEN?
wani lokaci kafinnan....
Yarinyace mai kamar shekaru 18 take shigowa ɗakin, da unifoam a jikinta tana riƙe da jakar makaranta.
Momma ce da daddy zaune a ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake a cikin ƙayataccen falon, basaina tsaya faɗa muku ƙayatuwarshi ba, anma ko a kasar waje sai haka.
Da sauri ta rungume daddynta, tare da sumbutar mommanta duk suka mata sannu da zuwa, a gaggauce tayi saurin yin hanyar da zata kaita ɗakinta.
Drivernta ne ya shigo yana tafiya riƙe da wuyanshi, yana miƙar da ƙafaɗarshi da ɗayan hannu daga ganinshi yanajin azaba, saida aka bashi izini ya shigo sannan ya faɗi yayi gaisuwa ga daddynta duk suka tsura mishi ido sunsan da magana, ba kamar Abbanta daya gama tsorata sanda yaga ya zaro makullan motar da ake kaita makaranta ya miƙa musu.
Abba yace "mukullin mota naga kana miƙomin salele, bayan tun jiya dana ɗaukeka aiki nace ka riƙesu a hannunka saboda duk inda sadeey zataje ka kaita"
Daƙyar drivern ya iya cewa "nayi ritaya Alhaji" har suna haɗa baki momma da daddy sukace "ritaya daga fara aiki yau? Ya ɗaga wuyanshi daƙyar yace "ƙwarai kuwa Alhaji, saboda neman kuɗi ni bazan iya jefa rayuwatah a halaka ba, ku nemi wanda zaici gaba da kai ƴar ta'addar ɗiyarku makaranta, anma nikam ina da mata da mahaifiyar da dani kaɗai suka dogara"
Abba ya sassauta murya yace "kayi haƙuri salele duk bata kai haka ba, zan jama sadeey kunne, idanma Albashinka ne yayi maka kaɗan zan ninka maka iyakar yanda kakeso, ka daure kaci gaba da kaita" miƙewa yayi tsaye yana shirin tafiya yace "ayi haƙuri Alhaji, don wannan ɗiyar bama ƴar ta'adda bace, ta'addancinne da kanshi, nikam bazan iya ba" momma da daddy sai ƙoƙarin lallaɓashi suke, anma baima tsaya ba ajiye mukullin motar ya tafi.
Cikin ɓacin rai momma da ƙarfi ta ƙwala mata kira "sadeey!", da gudu ta taho tana dariya harta cire unifoam da riga da wando jikinta, bayan kujerar da momma take ta tsaya tare da soƙala hannunta ta wuyan momma tace "gani daddy"
Momma tace "nice nan nake kiranki marar kirki kawai, yanzu sadeey wannan halin da kika ɗaukarma kanki shine dai dai? Cikin watannan direbobi nawa aka samar miki? Ki dinga wulaƙanta na ƙasa dake don kawai gana neman abinci ƙarƙashinki? Wlhy idan kika ƙarasa kaini ƙarshe makarantarma sai dai ki tafi a ƙafa koki tari bus ɗin makaranta.
Ta marairece fuska kamar gaske tace "don Allah daddy nice banda kirki? Kowa yasan babu ruwana da zaluntar talakawa kullum kyautata musu nake, ni kawai driver ne bani so"
Daddy yace "miye na faɗa a ciki kuma hajia? Kinga ƴar gatan Daddyn ta zonan kinji" ta zagayo inda yake tana murmushin jin daɗi.
Ya kalleta yace "kindaisan daddy na sonki ko sadeey? Ta ɗaga kai cikin farin ciki, yace "kuma kinsan zai iyayin komai dazai sakaki farin ciki ko? Tace "sosae ma kuwa daddy" ita dai momma iyakarta kallo kawai.
Yace "tohh kiyi haƙuri ki ƙarasa karatun secondry sadeey, nayi miki alƙawarin ko motoci nawa kikeso zan siya miki, sannan a koya miki mota, anma yanzi tayaya zan barki ki dinga driving kanki da ƙananun shekarunki?
Nan da nan ta ɓata rai, kamar zatayi kuka tace "tohh daddy frnds ɗina nawane suke driving da kansu? Yace "kinsan na damu dake da yawa sadeey" miƙewa kawai tayi tana sharar hawayen da take ta ƙaƙala sunƙi fitowa.
Ya kamota yace "haba Auta! Daddy hidimar kasuwancinshi sun mishi yawa, ga yayanki Shaheed da baya zaune shima hidimar aikinshi, bazaki bari driver yana kaiki ba harki gama makaranta a koya miki? Komawa tayi ta lahe jikin daddyn nata a shagwaɓe tace "nidai da kaina zan dinga driving, bazan dinga shiga frnds da driver ba, ko in na tashi ckul saina jirashi yazo ɗauka na" yace "shikenan zai dinga jiranki makarantan har ki gama karatun ya dawo dake"
Tace "nifa daddy driving kawai nakeso" momma tace "kaima dai Alhaji bazaka gaji da lallaɓa wannan kafaffiyar ɗiyar ba, ganin hakanne take kara sangancewa"
Yace "ke ina ruwanki da ɗa da mahaifi? Duk don wa nake neman kuɗin ba ita ba? Shaheed ya riga da yaa kafa kanshi, don haka banda burin daya wuce yi mata duk abinda takeso a duniyarnan" ya kalli sadeey da sauri taci gaba da murzar ido, yace "zanga abinda zan iyayi kinji" ta ɗaga kai tace "yauwah daddyna, mai ji dani"
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishia)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment