```MAKASHINKA...```
57-58
©Rabiatu sk msh
www.babymsh.blogspot.com
Ba tare da yaa kalli sadeey ba yake magana "kinga dai abinda yaronnan yayi mana ko? Har yanzu bazai barmu ba ƙila yafison duk saiya ƙarar da danginki sannan kema ya haɗa dake"
Tace "me nayi mishi da zai kasheni Abba? Ya kalleta cikin mamaki wai yau sadeey ce take mishi wannan tambayar ita da tafi kowa tsanar shamsuddeen Yace "su iyayenki me sukai mishi ya kashesu? Da kuma wannan baiwar Allahn da take kwance taa kusan zama gawa saboda shi.
Shiru tayi taa rasa amsar da zata bashi haushi kamar ta shaƙeshi takeji, ganin tayi shiru yaci gaba "Macuci ne shamsuddeen ɗinnan, yana da haɗari sosae, bazamu san sanda zai aikata kisan ba shiyasa ma za'a bamu ƴan sandan da zasu na kare mana lafiyarmu" sadeey tace "to ay Abba MAKASHINKA DAKE TARE DAKAI a koda yaushe yaafi wanda baka gani hatsari"
Shiru yayi yana auna maganarta, sosae tana mishi yawo ko ina a ƙwalwa, zarginshi naa ƙara zama gaskia, Yace "wanene Makashinki da yake tare dake? Tace "bansanshi ba Abba, anma dai shamsuddeen yaa tabbatarmin da ba shine yayi kisannan ba" jikin Abba fa ya fara zufa, kayanshi suka jiƙe daƙyar ya iya cewa "tohh idan bashi bane wanene? Tace "bai faɗamin ba"
Sannan ya samu bakin faɗa "Aikin banza da wofi, ke zai maida shashasha ya kashe miki iyaye ya kalailayeki da daɗin baki, tohh wlhy koda kin haƙura ni bazan yafe mishi kashemin yayana da yayi ba, saina ɗauki fansar jinin yayana"
Ya sassauta Murya "kece kaɗai zaki bada gudummuwa wurin ɗaukar fansar nan sadeey, ki duba halin da yaronnan ya sakaki, ki taimaka mana wurin kamashi bamasai mun kaishi kotu ba zan ɗaukar miki fansar iyayenki kuma ɗan uwanah"
Duk da ɓacin ran da take ciki, da kuma haushin da maganganun Abba ke bata saida tayi dariyar takaici tace "tohm miye banbancinmu da shamsuddeen ɗin kenan Abba indai bamu ƙyale doka tayi aikinta ba? Idan haka ne ay shima zan iya yarda da cewa ba shine ya kashemin iyayena ba, kuma in haɗa hannu dashi kamar yanda ya nema wurin kashe wanda ya kashemin iyayena, bazan taɓa ɗaukar doka a hannu na ba Abba" ci gaba yayi da lallaɓata tana sharewa.
Yace "tohm idanfa da hukuma ne zaki taimaka wurin kamashi? Shiru tayi tace "Abba nifa ba ganinshi nake ba ta yaya?" yace "ta yaya ya faɗa miki ba shine ya kashe iyayenki ba? Karfa ki zama mai taimakawa mai laifi" shiru tayi saboda yanda ya tsattsareta da magana, Allah ya taimaketa sai ga likita yaa kira Abba ya tafi suna magana.
Ta ɗan bugi kanta tohh ita wace irin magana ce tayi da Abba? Duk taa rikicema batasan yanda suke fita ba.
Har suka kwana a asibiti momie bata farfaɗo ba, kuma bata ƙara yarda sunyi magana da Abba ba.
Tunda safe Yace "suje gida da Anwar ta haɗo break fast da kayan da zasuyi Amfani dasu" Anwar yanata kakkaucewa Abba ya matsa mishi su tafi tare harda yi mishi gargaɗin ya kula da ita.
Suka fito sai ɗari-ɗari yake don tun ranar da yaji shaƙa wurin shamsuddeen a daren da yaje ɗakin sadeey yake tsoran zama da ita, sai sauri yake yayi gaba tana biye dashi ya buɗe mata motar ko makullin bai cire ba ya matsa gefe yana jiran ta shiga.
Ta buɗa baya ta shiga yananan yana tunanin tafiya tare da ita sai dai yaga anja mota taayi gaba.
Sadeey ma sai dai taga mota ta tafi, suna fita ya fara sharara gudu da ita, Da taayi shiru saboda fushi take dashi da taga yaƙi tsayawa ta matsa ta fara kai mishi bugu tana taɓa jikinshi "ka tsaya, ka tsaya nace ina zaka kaini? Yaja uban burki sannan ya tsaya har sun fara fita daga gari, ta buɗa motar ta fita shima ya fito a suffarshi ta mutane.
Tace "miye haka kayi yaya deen? Yace "zuwa ganin masoyiyatah mana" tace "ba maganar wasa ake ba, me ka yima momie? Yace "Shine nima nake Shirin tambayarki meke faruwa da momie na ganku a asibiti?
Tace "karka maidani wacce bansan me nake ba Ya deen? Munyi dakai bazaka yi musu komi b, kuma harka manta abinda ya faru jiya da maraice har aka kaita asibiti?
Yace "wlhy bansan komi ba sadeey, duk jiya banje gidanku ba" tsoki taja tace "wannan yaa tabbatarmin baka da gaskia shamsuddeen, ni zaka yima yawo da hankali?
Shima yaa fara harzuƙa Yace "wane irin yawo da hankali kuma, ni bansan maganar da kike ba" tace "bazaka taɓa sani ba kuwa," ta anshe makullan motan daga hannunshi ta shige kawai ta barshi nan yana mamakinta.
Sadaukarwa ga sadeey s adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment