New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 43-44

```MAKASHINKA...```
          43-44

©Rabiatu sk msh

Tun daren ranar take saka ran kiran daddy bai kirata ba, har barci ya ɗauketa suna cikin waya da Shamsuddeen daddy bai aiko kiranta ba.

Da safe ma har ta gama duk abinda zatayi duk cikin jiran daddy anma shiru, harta shirya ta tafi gaisheshi.

Su duka ta gani zaune daddy da momma, sai momie da Abba Ya shaheed da Shamsuddeen na zaune ƙasa duk sunyi shiru, ji tayi kamar ta koma da baya, tohh meya kawo Ya deen da sassafennan kuma?

Ƙarasawa tayi itama ta russuna sannan ta gaishe da kowa, ta miƙe zata koma, daddy Yace "dawonan sadeey wannan taron da kika gani ke kaɗai ake jira.

Ta koma ta zauna duk idanunta sun raina fata daddy yace "Ban taɓa tunanin hakan daga gareki ba Sadeeya" nan da nan hawayen data daɗe tana adanawa suka fara zubowa tace "Kayi haƙuri daddy laifin Zuciyatah ne" Yace "laifin zuciyarki har kina da buƙata a wurina ina matsayin mahaifinki bazaki iya faɗamin ba?" sai lokacin zuciyarta tayi sanyi da alama daddy bai ɗauka da girma ba.

Yace "Kin tabbatar kina son shamsuddeen? Kunya ta saka ta ƙudundunewa tana rufe fuska, Abba yace "wane irin tana sonshi yaya? Harma kaa yarda zaka aura mishi ita kenan? Daddy yace "Tohh ya zanyi tunda tana sonshi? Zan hanata abinda takeso ne?

Abba yace "nima ba nace ka hanata abinda takeso ba, anma gaba zaka dubar mata, bawai ka biye mata ba, har yanzu yarinya ce fa bata san inda yake mata ciwo ba, mutum da ko karatu baiyi ba, baida sana'a ta yaya zai iya cidata?"  daddy murmushi yayi yana kallon Abba yace "Allah ne yayi sadeey zata rayu, anma a sanadinshi ne take gabana a yanzu, Suna son junansu, kuma ni banda burin takura ƴaƴana"

Abba zuciyarshi kamarta tafaso Yace "naaji duk wanna, baka bani amsata ta yanda zai ciyar da ita ba, tunda dai bata taso cikin wahala ba" daddy murmushi yake irin nasu na Manya yace "Shamsuddeen yayi karatu, kuma daman ina da niyyar bashi Manager a ɗaya daga cikin Company na"

Abba Yace "kuskurene kake, talakan mutum bai iya samun wuri b....." daddy Yace "Don Allah ya isa hakanan, bakasan waye shamsuddeen ba shiyasa kake faɗar haka"

Tashi daddy yayi ya buɗe wadrobe ɗin da yake ajiye takardu, ya zaƙulo wasu ya taho dasu a hannunshi sannan ya zauna, Abba ya miƙa mawa ya Karanta da ƙarfi.

"Ni Alhaji Sa'idu, na Sadaukar da duk dukiyata ga ɗiyata sadeey har lokacin da zata cika shekara 23, idan tayi aure kafin lokacin zata zama ƙarƙashin kulawar mijinta, ko kuma mariƙinta kafin tayi aure"

Abba na zuwa ƙarshe daddy yaci gaba da cewa "naa daɗe da mallaka mata dukiyata tun kafin takai haka, akwai copy ɗinsu a kotu, original ɗin kuma na kaisu ajiya a bank, Shaheed ma yana da tashi dukiyar, don haka duk abinda na tara saboda sadeey ne, burina koda yaushe in ganta cikin farin ciki.

Tashi tayi ta kwantar da kanta da saman cinyarshi tana hawayen Murna tace "nagode sosae daddy, ina sonka sosae" momma tace "muma muna sonki da yawa sadeey"

Wani irin murmushi na hango a fuskar Shamsuddeen dana rasa gane Ma'anarshi, Abba kuma duk yayi kicin-kicin da fuska kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu.

Kowanne dai na rasa gano Abinda ke zuciyarshi, murna ce? Tunanin Alkhairi ne ko akasin hakan?

Daddy ya cema shamsuddeen "naa baka auren Sadeey, duk sanda ka shirya na ɗauki nauyin komi, Na yarda dakai Shamsuddeen, Kayimin Alƙawarin zaka kulamin da sadeey ko bayan raina, zaka riƙeta amana kuma zaka cika mata burinta na karatun lawyer"

Yace "Insha Allah daddy bazaka sameni da cin Amanarka ba, Bazakayi dana sanin yardar da kayi dani ba"

Daddy yace "idan kayi hakan kaa gamamin komi shamsuddeen"

Haka taron ya tashi kowa da Abinda yake saƙawa a zuciyarshi.

Da dare.....

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam

©Rabiatu Sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts