New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 31-32

```MAKASHINKA...```
           31-32

©Rabiatu Sk Msh

Shamsuddeen ganin yayi gudu mai nisa basu biyoshi ba ya sakashi tsayawa yana wasi-wasi, ihunta ya jiyo daga can nesa, take nan ba tare da yayi shawara da kowa ba ya koma da baya bayan ya kira ƴan sanda.

Daga nesa ya hango yanda ake kokawa da ita cikin duhu, ogansu nata ƙoƙarin janta yana kekketa mata kaya, baisan sanda zuciya ta kwasheshi ba, ya dirar musu irinna jaruman maza.

Duk sukayo kanshi, ogan yace "ku tambayeshi dalilin daya maidoshi" kafin ogan ya ƙarasa basu Umarni wani yakai mishi bugu da ƙaton ƙolo, kafin ya kawo mishi ya duƙe wurin ɗagowa ya dunƙule hannunshi yakai mishi naushi a ciki, ya wuntsila yayi gefe guda.

Hannunshi ya miƙa ya jawo sadeey, duk suka taso da Manyan makamai a hannunsu, Ogan ya nunashi da bindiga yace "Kuna motsawa daga wurinnan zan fasa kanka da bindiga, ka bar wurinnan ka barta"

Duk sun ɗaga hannu a sama, kowanne cikin zuciyarshi addu'a yakeyi Allah ya kawo musu ɗauki, wani daga cikinsu ya halba mishi ƙafa, da sauri ya kwanta wurin, itama sadeey batasan sanda ta zube wurin ba tana kuka.

Tunani yakeyi yanda zaiyi da bindigar hannun ogan, ɗaga kai yayi yaga hannunshi dai dai ƙafar ogan, bai tsaya yanke shawara ba, ya saka hannu ya zame shi daga kujerar, bindigar ta ɓulle wuri ɗaya, cikin azama shamsuddeen ya miƙe.

Suna kawo mishi bugu yana kaucewa, wani naa samunshi, haka suka dinga kaima juna bugu, sadeey na gefe tana kuka.

Yaa sha wahala sosai kafin ƴan sanda su iso, suka kwashesu suka tafi, basu samu guduwa ba saboda suma duk sunji jiki.

Asibiti suka wuce da Shamsuddeen saboda yanda jini ke zuba jikinshi, tun a hanya sadeey tayi ma su momma waya lokacin dare yayi sosae.

Tana kuka tana basu labari, Su daddy sun shiga tashin hankali, Anma sunyi godiya ga ubangiji da abin yazo da sauƙi, sunji daɗi matuƙa da ceton ƴar su da Shamsuddeen yayi, ya kusa bada rayuwarshi saboda ita kawai.

Kwananshi biyu ana kula dashi asibiti, kusan sadeey ce ma take jinyarshi, makarantar ma daina zuwa tayi, ga jarabawarsu na matsowa, ƴan fashi kuma an miƙasu kotu.

Da aka sallameshi gidansu sadeey suka wuce dashi, yaji sauƙi sosae sai dai ciwon da bai ida warkewa ba.

Tun daga lokacin shamsuddeen ya zama ɗan gida, suka zama Abokai da Ya shaheed, sadeey ta daina mishi kallon drivernta ya koma matsayin yayanta, su daddy kallonshi suke kamar jininsu.

Ya zama ɗan gida sosae, suna ƙara samun shaƙuwa da sadeey.

Wani Yammaci suna zaune saman kujera wurin wasa a tsarabar gidan, shida sadeey...

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam

©Rabiatu Sk Msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts