New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 111-120

[11:28, 3/16/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
111-115
washe gari kamu Akayi, shima dk inda Maryama ta gifta idanun deen na kanta, Tunani take a ranta kallon me deen keyi mata?? Ko kuma hka yake da kallon mata? Wata zuciar ta gargade ta da zato tace wata qila ma bni yake kallo ba.
Ranar friday aka daura Auren Maryam da shamsudden, da dare aka dauki Amarya aka kaita danqareren gidan shams dake katsina
Da dare suna zaune da qawayensu suna jiran Abokan Ango sai tsokanar Maryam suke, Maryama tace gsky ku qyale namcyna ta huta, kuka sani ko dga yau ta fara rashin lafiya?? Su duka suka kwashe da daria Maryama ta riqe baki tace "kunga ba ruwanah ku qyale Amarya hkanan gsky!!
Shru tayi tana tuna maganganun da Ahmad ya fada mata kan hanyarsu ta zuwa gidan Maryam da yake motarshi ta shga ita kadai, kallonta yayi Yace "Abokiyah miye Abota?? Tayi murmushi tace "Abota ni ynda na dauka, shine ka samu Abokin daxai kula dkai, Yana tare dkai dk wuya dk dadi, wnda zaiyi qoqarin saka ka farin ciki, wnda zai baka shawara, Abubuwah da yawa dai Abokii, dk duniar nan babu wacce ta kaini sa'a da samun Aboki kamarka, ka tuna ranar da muka fara haduwa a ckul? Ji nake kamar ranar nazo duniah, damn tunda Aka haifeni nasanka nasan Rayuwatah zata taso cike farin ciki! Ahmad yace "xaki iya qare rayuwarki dani Maryama?? Da sauri ta dago kai cikin mamaki tace "kamarya?? Yace "Muyi aure Maryama muyi rayuwah cikin farin ciki, tun ranar dana fara ganinki soyayyarki ta shga zuciatah, naa rasa Ynda zan bayyana miki! Ki kalli cikin idonah Maryama babu komi sai soyayyarki da kka kasa fahimta!!
Da yake sun iso gdan bude motar tayi ta shge cikin gdan saboda wani irin nauyin Ahmad data dinga ji, Anma kuma ta rasa dalilin daya sanyata farin ciki!! Tohm ita wata Amsa zata ba Ahmad? Tace "gsky ni bbu soyayyah tsakaninah da Ahmad Abotah ce kawai!!
Maryam ce ta katse mata tunani tace "kije wai wurin shams zaki amsomin saqo! Tace "wane irin saqo kuma da gaki a gdanshi zamu tafi mu barku bxaki jira ya kawo miki ba?? Tace "in kinje kin gani nidai ki sauri ynxu Abokan nashi sun shgo! Yana falon baqi tace tohm ta tashi ta fita.
Rabiatu sk msh
[14:10, 3/16/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
116-120
Zaune ta sameshi saman kujera yaa jingina kanshi a sama kamar mai tunani gabanta naa faduwa data rasa dalili, cikin qarfin hali tana Yaqe tace "dk tunanin Amaryar ne? Tunani dai yaa qare tunda gata a gdanka! Tashi yayi zaune fuskarshi babu yabo babu fallasa Yace "tunani bai qare ba Maryama tun ranar laraba rabon da inyi brci mai sunan barci! Tayi daria cikin zolaya tace "haba Ango na Amarya! Ana hidimar bikinka in kace kaayi brci ay kamata Yayi a tuhumeka! Yace "Wannan daban ne Maryama ko Abnci bni iyaci dk kwanakinnan!
Tace "dk dokin Aurennan ne! Yace "ba hka bne, tunani Yaamin yawa, na rasa meke damunah! Zuciatah na rasa me take nufi..., tace "gsky kaje kaga likita cikin qosawa da mgnr! Yace "baki ganewa Maryam! Cikin jin haushi sbd taa fara ganoshi tace "ni jakkar aji ba, ganar dani! Daria Yayi sannan Yace "Ina sonki Maryama!
Wani irin tashin hnkali ne Ya dirar mata lokaci daya, qafafunta har kyarma suke zuciarta na bugawa da sauri, daqyar ta iya hada kalmomi a bakinta tace "wannan wace irin wasa ne shams?? Yace "dgsk nake Maryama ina sonki, Tun ranar dana fara ganinki! Wlhy soyayyah nake miki wadda bnsan iyakarta ba!
Juyawa tayi da niyyar fita tabar mishi dakin ya riqo hannunta, Yace "karki tafi don Allah Maryama ba tare dakin bani Amsa ba, zuciatah na cikin wani hali, idan...., kafin ya qarasa ta daddage cikin zafin nama da bacin rai hrda dan tsallenta ta watsa mishi wani irin wawan mari!! Badon yana namijin gske ba da saiya kifa qasa, ta kalleshi tana huci Tace "wannan ya isheka amsa?? Maryam taayi kuskure mai yawa a rayuwarya shams!! Maryam batayi aure ba! Batayi sa'ar miji ba! Matsalarku kenan maxa, ynxu dk son da Maryam take maka da bata hada ka da kowa ba sakamakon da zaka mata kenan?? Kaayi kuskure shams idan har kana tunanin ni zan iya cin amanar qawatah, juyawa tayi zata fita harta kai qofa yace "minti daya! Ta dakata
Yace "kiyi tunani Maryama, bn taba son Abu na rasa ba, kuma bzan fara A kanki ba, Tace "koda ina sonka bzan taba zama da Maryam a matsayin kishia ba, ballantana Ma bani sonka! Bbu Amfanin inyi tunani A kanka! Idanunshi jajir Yace "zaki dawo gareni Maryama wannan Alqawari ne!!
Tsoki taja ta fito ta fice dga gdanma ma gaba daya cikin bacin rai, ko Maryam batayima sallama ba!!
Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 5-6```MAKASHINKA...```            5-6 ©Rabiatu sk msh~ Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai ta… Read More
  • MAKASHINKA 5-6```MAKASHINKA...```            5-6 ©Rabiatu sk msh~ Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai ta… Read More
  • MAKASHINKA 9-10```MAKASHINKA...```          9-10 ©Rabiatu sk msh Tananan zaune har 10pm, saiga momie ta fito, har zata wuce ɗakin Abba ta hangota ta taho inda take tana mata kallon mamaki M… Read More
  • MAKASHINKA 3-4```MAKASHINKA...```           3-4 ©Rabiatu sk msh~ Momie ta kalle ta tace "lafiyarki kuwa? Sadeey Tace "lafia lau momie me kika gani? Momie tace "dukkin fita hayyacinki da ala… Read More
  • MAKASHINKA 7-8```MAKASHINKA...```             7-8 ©Rabiatu sk msh~ A ƙofar ɗakin ta tsaya, tace "bari inyi sauri in shirya ko ya Anwar? Yace "naji anma kiyi sauri plz &#… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts