New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 41-42

```MAKASHINKA...```
         41-42

©Rabiatu sk msh

Tun daga ranar soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, koda yaushe suna tare, wani bai iya ɗaukar lokaci bai ga wani ba.

Yau ne ranar data zana jarabawarta ta ƙarshe a makaranta, cikin farin ciki take, burinsu ya fara cika ita da Yaa deen, Yanzu ba abinda ya rage musu sai maganar aure.

Yazo ɗaukarta a hanya yana nuna mata shima irin farin cikin da yake ciki tace "Ya deen yau ne fa zanjema daddy da maganar aurenmu, don na lura sam basu lura bama da soyayyar da muke ba" shru yayi yana tunani duk yayi alamar damuwa tace "yadai yaya deen? Duk kayi shiru" yace "tsoro nakeji sadeey kar daddy ya hanani aurenki" tace "tohh ka daina ji, shifa daddy ba haka yake ba, bazai taɓa hanani abinda nakeso ba"

Yace "bazai hanaki ba sadeey, anma banda wani ƙwarin gwiwa akan zan iya riƙe ki bayan aurenmu in ciyar dake abnda kikeci a gida, ni bani da komi, kakanni na ma haka, sadeey tun kafin in samu soyayyarki na fara fargabar rasa ki"

Ajiyar zuciya tayi tana aika mishi saƙon ƙarfafa gwiwa cikin wani irin salon kallo tace "bazaka taɓa rasa ni ba Ya deen, saboda ka riga da kaa zamarmin farin cikina, zan iya jurar zama da yunwa, anma bazan iya jurar zama babu kai ba, yau ina cikin farin ciki, don Allah ka daina" yace "na daina gimbiya.

Suna tafiya suna firarsu ta Masoya har sukaje gidan, tun daga harabar gidan ta hango baƙuwar mota da alama sunyi baƙi.

Tana zuwa bakin falon ta fara jiyo magana ƙofar ta buɗe ta shiga, Abba da momie ta hango sai su momma da daddy, tana yin Sallama ta tafi da gudu jikin momie ta rungumeta tana mata sannu da zuwa.

Tace "shikenan kuma momie zakuzo ba sanarwa? Abba yace "Ay da mun sanar dake tun kafin muzo murnar taki ce  zata ƙare, anma kinga murnar taki ta yau tafi ta kullum" tace "sosae ma kuwa daddy yau ina cikin farin cikin na gama makaranta, kuma gani cikin iyayena su duka, saura yayyena kuma Allah yasa da Ya Anwar kukazo" daddy yace "Anwar yaƙi nigeria, tun kafin ki fara karatu gashi harkin gama".

Tace "kuma nina ƙagara inga yayan nan nawa" Abba yace "ay yaa kusan dawowa insha Allah". Haka sukaci gaba da firarsu har lokacin Sallah yayi su daddy suka fita tare.

Ranar shima yaya shaheed ya dawo saboda yanda Sadeey ta matsa mishi yazo tana son ganinshi.

Faɗa ya dinga yi mata kamar zai haɗiyeta bayan ya gamajin bayaninta, "haba ƙanwata da hankalinki da tunaninki, wlhy ni ban taɓa tunanin baki da hankali ba sai yau, kina cikin gatanki kamar wacce ta rasa masoyi ki rasa wanda zaki so sai drivernki? Me na sama yaci ballantana ya bama na ƙasa? Ko kinfiso mu saida Akuya ta dawo tana ci mana dussa"

Tunda ya fara magana take kuka, hannu ta biyu ta saka ta rife mishi baki "don Allah ka daina mana yaya, duk duniya ina da wanda zan faɗa ma damuwata daya wuceka? Tunda nake dakai baka taɓa ɗaga min murya ba sai akan wannan maganar data zamemin farin cikina da kullum kuke nema min, kaida nake tunanin sauƙi daga gareka? Karka manta fa kune kullum kuke faɗamin in daina ƙyamatar talakawa in dinga jawosu jiki.

Ya ɗan rage fushin shi yace "mu cewa mukai ki daina wulaƙantasu ba wai kiyi soyayya dasu ba" tace "ni kaina bansan sanda na fara sonshi ba Ya shaheed anma inajin kamar idan na rasashi zan mutu ne"

Yace "Shikenan ƙanwata banison abinda zai sanya in rasa ki, Anma ki guji halin maza, zaki iya kyautata mishi daga ƙarshe ya ƙuntata miki" murmushin farin ciki take ta kwantar da kanta jikin Ya shaheed tace "Ina da kyakkyawan zato akan ya deen, bazai taɓa nunamin halin butulci irinna maza ba"

Ya shaheed yace "fatan da nake kenan a kullum, insha Allah anjima zan samu daddy da maganar" tace "Yauwah yayana nagode sosae"

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MATATAH CE 62♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             62 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 64♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡               64 ©Rabiatu sk msh       ®NWA … Read More
  • MATATAH CE 63♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              63 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 65♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             65 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 61♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              61 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts