```MAKASHINKA...```
51-52
©Rabiatu sk msh
www.babymsh.blogspot.com
Iska na kaɗo mata ta ko ina, zumbur tayi ta tashi zaune, kanta naayi mata wani irin nauyi, taa daɗe a haka cikin ɗan karamin ɗakin dake cikin garden ɗin wanda aka ƙayatashi sosai.
Kafin ta hango Shamsuddeen zaune can waje saman kujera ya juya baya, wani irin baƙin ciki ne yazo mata kamar ta kasheshi ta huta takeji, dube dube ta shigayi cikin sa'a kuwa taga wuƙa saman gefenta an ajiye tare da fruit, bata tsaya ƙara tunanin wani Abu ba, ta ɗauki wuƙar ta fara saɗaɗawa a hankali zuwa inda yake.
Ɗagawa tayi da niyyar caka mishi idonta rufe, ta kasa ta saukar da hannunta tana tunanin ƙara yunƙurawa ta kasheshi ta ji muryarshi ba tare daya juyo ba Yace "ki kasheni mana sadeey" duk da taaji mamaki anma bai sanya zuciyarta ta karaya ba, wuƙar na hannunta dai taci gaba da kallonshi cikin tsana.
Yaci gaba da cewa "banda wani sauran jin daɗi a duniya sadeey tunda har kika tsaneni, ki kasheni idan har hakan zai faranta miki" miƙewa tsaye yayi ya juyo suna fuskantar juna, har lokacin zuciyarta a dake take, rufe idonta tayi tana niyyar matsawa ta chaka mishi Yace "Anma kafinnan ki tsaya kiji Abinda zan faɗa miki" batayi magana ba sai dai ta buɗa idanunta tana kallonshi yayi ɗan taku sannan ya juya mata baya ya fara magana.
"Tabbas kin ganni gidanku da makami a hannuna cikin dare sadeey a ranar da aka kashe mahaifinki kuma na buga miki Abinda ya sakaki faɗuwa a sume wannan gaskia ne, anma Akwai wata gaskiar da baki sani ba" tsoki taja saboda ƙosawa data farayi da maganganunshi, ya juyo yana kallonta da murmushi mai ƙona zuciya a fuskarshi yaci gaba da magana".
"bayan mun gama fira dake na tafi cikin farin cikin sanyayamin zuciya da kika gamayi da sanyayyan kalamanki, da kuma murnar kin kusan zama mallakina, saina lura da gidanku a zagaye yake da muggan mutane, hakan ya sanyani fasa tafiya na dawo cikin gidan da niyyar shaidawa daddy, saina hango wasu ƴan fashin guda ukku a ƙofar ɗakinshi guda biyu a ƙofar ɗakin momma, hakan ya sakani sulalawa na haye saman bene yanda zan dinga hangosu ba tare da sun ganni ba, daman tun ranar da muggan mutanennan suka tsaremu ni da ke na daina yawo babu makami"
Ya nisa sannan yaci gaba da magana "inanan a inda nake laɓe suka gama fito da daddy da momma, Abinda ya bani mamaki shine bai wuce ganin Abbanki yaa Shigo ba yana ma daddynki kallon mugunta, takardu ne ya miƙa mishi a hannunshi, ya tsareshi dole sai yayi sighn yana cewa "bazai yiwu ba Yaya yanda na daɗe ina saka rai a dukiyarka, rana ɗaya kawai ka kyautar da ita ga ɗiyarka da zataje can ta auri wani da shine zaiyi aiki sosae ya tara kuɗin dazai biya mata buƙata".
Daddy takaici ma hanashi magana yayi Abba ya saka hannu ya damƙo bakin daddy yana zare mishi ido yace "zaka saka hannun ko kuwa?" daddy hannu ya saka ya sharara mishi mari saboda zafin zuciya, cikin ɓacin rai Yake magana "Allah ya wadaranka Kabiru, kaci Amanar iyayenmu, kuma kaaci Amanar zumunci, A yau naayi baƙin cikin kallonka da nake a matsayin ɗan uwanah, lallai babu sauran abin yarda a duniya tunda kana ɗan uwana zakaimin haka"
Cikin jin zafin marin da Daddy yayi ma Abba ya nunashi da ɗan yatsa Yace "ni tuni na daina buƙatar ɗan uwah, dukiyarka kawai nake da buƙata," daddy yace "kuma bazaka taɓa samu ba, donna faɗa maka naa mallaka ta ga ɗiyata, kuma kotu ma tasan da maganar, ko bayan raina bazaka taɓa mallakarta ba"
Abba Yace "idan fa tayi aure? Duk da haka dukiyar tata ce koda kuwa zata sakar ma mijin, Anma idan ta mutu fa? Dukiyarta taa zama mallakin mijin data aura, don haka yanzu banda buƙatarku a raye nasan yanda zan samu dukiyarnan" ya ɗaga wuƙa zai caka ma Abba, Shaheed ya rugo da gudu yana kiciniyar ƙwacewa, ganin haka nima na taho a kiɗime zanje mukayi kiciɓus dake.
"nasan idan Abba yasan kema kinsan ya kashe miki iyaye zai iya kasheki shiyasa ka na ƙwala miki abinda kika suma na maidaki saman gado na kwantar dake don karki fito sannan naje, na iske shaheed kwance cikin jini sadeey" yayi shiru yana share hawaye.
Sannan yaci gaba...
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment