ABDUL WAHAB 32
©Rabiatu sk msh
®NWA
Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi.
Tunda safe yana shirin tafiya office wayar hajia ta shigo mishi, ya d'auka ya gaisheta cikin girmamawa, Tace "wai meya sami wayar sadeey ne? Kullum fatyma sai taacemin taa kira a kashe nima ina kira ban samu kullum sai dai kacemin lafiya lau, idan lalacewa tayi ko 'bacewa baka sake mata wata?
Yace "Mantawa nake hajia, insha Allah zan bincika, zan sake mata, Tace "kodai wani Abu kake mata Abdul wahab? Da sauri yace "A'ah wlhy hajia nikau mezan mata? Inata so in kawota gida ma sai tace min ba yanzu ba wai kar ace taa fara fita da wuri," "hmm, kawai hajia tace ta kashe wayar, kamar dai bata yarda ba.
Can ya hango sadeey tana fitowa daga kitchen da kayan abnci, tana ganinshi ta fara sauri kamar mai shirin tashi sama, kafin ya 'karaso taa gama ajiyewa saman dinning table taa juya da sauri zata tafi d'akinta.
Da 'karfi yace mata "ina kwana" bata juyo ba sai dai ta rage saurinta tace "ka tashi lafiya? Bata jira amsarshi ba ta 'kara gaba.
Tana zaune a 'dakinta ya shigo da waya a hannu, "ga waya fatima nason magana dake" shru tayi kamar bata jishi ba, sai da ya mi'ka mata wayar, kamar bazata amsa ba ganin yayi tsaye sannan ta amsa.
Fatyma tace "Wlhy kina yanda kikeso matar yayanmu, wayar ma sai an gama da jan aji za'a amsa? Tace "Hmm ya kke? Fatyma tace "lafiya lau, ya amarci? Da fatan dai ba'a wahalar mana da yayanmu? Tace "Alhmdlh ngde, fatyma tace "yadai naji kamar bakison magana?
"sai anjima, tace ganin yanda ya tsura mata ido yana kallonta, fatima na "wai wanne irin wula'kanci ne wannan? Batace komi ba ta kashe wayar ta mi'ka mashi.
Duk taa had'a rai, ganin bai tafi ba ya sanyata mi'kewa zata bar mishi wurin ya tare hanyar, babu hanyar da zatabi ta wuce, ganin son maganar yake taja bakinta tayi shru ta koma ta zauna.
Yace "ina wayarki? Tace "tananan," yace "meyasa baki amfani da ita? Shru ta mishi, ganin bazata ce komi ba yasanyashi zama saman gadon, da sauri ta mi'ke ya jawo hannunta, ta fad'o jikinshi, da sauri ta fara 'ko'karin tashi daga jikinshi.
Yace "magana nake miki meyasa baki amfani da ita? Tayi shiru har lokacin 'ko'karin barin jikinshi take, Yace "ni bansan lokacin da kika iya fushi da ri'ko ba sadeey, duk kin canja gaba.
Tace "naji dad'i daka gane canjawar da nayi, kaga kuwa yanzu zan iya rayuwa babu kai, bakason farin cikina yayanmu, na rasa dalilin da yasa ka kawoni gidannan ka ajiye.
Murmushi yayi yace "dalilin so mana, kema zaki gane ne ki daina fushi da masoyinki," tace "babu ranar wlhy, sai dai kai ka gane takurar da kamun a gidannan ka sauwa'ke mun..." kafin ta rufe bakinta sai dai taji bakinshi cikin nata.
Kasa ta'buka komi tayi har ya saketa don kanshi ya mi'ke yana murmushi, mi'kewa tayi da gudu ta tureshi ta tafi toilet tana kuka, ba'kin ciki ne sosai a zuciyarta, haushin kanta takeji, ji take kamar ta cire bakinta ta huta.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment