New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 37

ABDUL WAHAB 37

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Tsayawa yayi daga baya yana sosa 'keya yace "sannu da zuwa hajia," ta amsa mishi tana mishi kallon marar gaskia.

Sai data zauna suka gaisheta, sadeey sai sunnar dakai take saboda wata sabuwar kunyar hajia da tazo mata, duk taa cika mata gaba da kayan ciye ciye taaji dad'in ganinta sosae.

Hajia tace "zuwa nayi inga d'iyar tawa tunda ka'ki kawomin ita, baice komi ba yayi shiru don babu yanda zaiyi ya kare kanshi, hajia tace "kaayi shru mana, anya Abdul wahab? Me kakeyi mata naaga duk ta rame?

'Dagowa yayi yana kallonta yace "wlhy babu abinda nake mata hajia, ay gatanan ki tambayeta, bataji dad'i bane kwana biyu, anma da sau'ki

Bata lafiya anma shine ba'a fad'a mana ba? Yace "ba wani sosae bane hajia da sau'ki, tace "ban yarda ba gatanan duk taa rame, kunma je asibiti kuwa? Yace "zamuje dai insha Allah yace, tace "a daure dai aje, ya jinjina kai.

Sai da zata tafi tace ya bata wuri zasuyi magana da sadeey, Yace "hajia ni bza'ayi dani ba? Tace "da d'iyata kawai zanyi magana ka fice nace, ya fice yana daria, sadeey ma murmushi kawai take.

Hajia tace "har yanzu baki huce da laifin da muka miki ba ko sadeey? Da sauri ta fara girgiza kai kanta a 'kasa tace "nice wa da zaku mini laifi hajia? Babu abinda kukamin, don Allah ku daina fad'in hakan, idanma laifi na muku ku yafemin, muryarta na rawa kamar zatayi kuka.

Hajia tace "babu Abinda kikai mana sadeey, naji dadin biyayyar da kike mana, Allah ya miki Albarka, ya baki yaran da zasu miki biyayya kamar yanda kika mana.

"Anma ki fad'amin gaskiya babu abinda Abdul yake miki? Ji tayi bazata iya fad'ar laifin Abdul a gaban hajia ba, d'aga mata kai kawai tayi.

Nasiha tayi mata sosae mai ratsa jiki, kafin ta kira Abdul ya maidata gida, sadeey ji take kamar ta bita su tafi, kewar maminta da Alhajinsu takeji sosae, komawa tayi d'akinta taci gaba da kuka.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

 
seo