```MAKASHINKA...```
5-6
©Rabiatu sk msh~
Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai takejin daman bata dawo ba.
Abin da yafi bata mamaki shine, duk cikin ɗakuna ciki da falo 7 dake cikin babban gidan, da kuma falo 18, sai kusa da Anwar ne aka bata ɗaki, kuma ɗakunan nasu suna nesa danasu momie.
Da dare ma sai da taji kamarta koreshi saboda daɗewar da yayi yana mata fira bai tafi ba.
Tunda asuba kira ya shigo wayarta, idonta rufe saboda barci ta ɗauko wayar tana dubawa, da sauri ta miƙe zaune ganin numbar da ake mata text ne aka kirata da ita, kafin ta ɗauka taa katse sai dai saƙon daya shigo daga baya.
```bada son raina na tasheki daga barci ba, kada gajia ta hanaki sallahn asuba```
~masoyi~
Ajiye wayar kawai tayi ta miƙe ta shiga toilet, lokacin data idar da sallarma barcin ya fita daga ranta, sai dai ta zauna tana tunanin ~masoyi~, fatalwa ne ko aljani? Don ko kaɗanma abubuwan da yakeyi baiyi kama da mutum ba.
Har wurin 10 tana kwance, ba tare da tayi barcin ba, gani tayi ana murɗa ƙofar ɗakinta za'a shigo, da sauri ta miƙe, da gudu ta shige bayan labule ta ɓoye sai dai ta leƙo da kanta kaɗan tana leƙe.
Anwar ne ya shigo yana kiranta da murya mai sanyi, "cwt ƙanwa, sadeeyna, ƙanwa!!! Sannan ta sauke ajiyar zuciyah, ta fito daga inda ta ɓuya.
Daria ya dinga mata, ganin yanda ta fito duk ta tsure tace "yadai Ya Anwar? Nifa banison daria," yace "wallahi my little sis kin cika tsoro, yanzu daga jin buɗa ƙofa harkin wani ɓuya.
Tace "nifa yaya ba tsoro naji ba," yace "ba waninnan, dana sani ay faɗowa kawai nayi inga inda zaki gudu," tayi daria tace "da fatan ka tashi lafia yayana"
"lafia lau ya kwanan 9ja? A zuciyarta cewa tayi ba daɗi, anma a zahiri tace "gayanan dai, Alhmdlh" yace "ba wani daɗi ko? Ta girgiza kai tace "tun daga dawowana kake kula dani, idan nace babu daɗi ay sai a ɗaureni, ballantana farin ciki ne fal a zuciyata" su duka sukayi daria.
Yace "aykam naji daɗi sosae, daman Albishir nazo in faɗa miki, anma bazakiji a bakina ba, sai dai ya zama surprise,"
"da gaske ya Anwar? Gaskia harna fara murna tun daga yanzu," ya koma saman gadon ya kwanta, yace "tohm zauna ki faɗamin abinda kikeso in miki kyautar kammala karatunki,"
Haka ta zauna duk da ta ƙagara ta fita ta gaisheda Abba da momie, ga yunwar da takeji, anma surutun Ya Anwar ya sakata dole ta haƙura.
Anwar fari ne, bai cika tsawo ba, anma jikinshi mai kyau, yana da ƙirar ƙarfi, fuskarshi zagaye take da saje mai kyau da kuma kwantaccen gashin kanshi da suke ƙara mishi kyau, yana da lumsassun idanu da suke saurin rikitar da mata, da muryarshi mai daɗin sauraro, baida kalar masu surutu, anma dai ya iya tsari da kalaman salon yaudara.
9:00pm
Tana kwance saman cinyar momie tana lallashinta, ita a ganinta duk damuwar sadeey na tunanin iyayenta ne da yayanta wanda masoyinta yayi silar mutuwarsu.
Anwar ne ya shigo da leda a hannunshi, ya ajiye mata yace "tohm ki tashi ki sauri ki shirya, yanzu zamuje kiga albishir ɗin naki," ta tashi zaune tana kallon momie sannan ta kalleshi tace "da darennan kuma? Yace "eeh mana, ba wani fita zamuyi ba, anan garden ne" momie tace "kayan partyn ne?"
Ya langaɓar dakai yace "momie shine zaki faɗa mata? Ay naso sai taje ta gani kawai," momie ta rufe baki tace "tohm ban faɗi mata ba, ba partyn tayata murnar gama karatunta bane".
Sadeey tayi daria tace "ni daka faɗamin ma ya Anwar da baka wani wahalan kashe kuɗi kayi hidimarnan ba, kuma kaaga ban sani ba ko frnds ɗina ban gayyata ba," momie tace "tohm idan baiyi miki ba wazai mawa? Bakisan yanda yayannan naki yakeji dake bane tun kafin ya ganki, Anwar yana ji dake fiye da yanda yayanki da kika rasa yakeji dake.
Hawaye ne sukaso zubo mata, saboda an tuna mata da yayanta da yake matuƙar kulawa da ita, ko kaɗan baiso yaga damuwarta, a hankali ta furta "SHAMSUDDEEN yaa cuceni," Abbah da yake shigowa baban falon yace "mu duka ya cuta sadeey, duk ranar dana ƙara ganin yaronnan indai yana raye saina sakashi dana sanin abinda ya aikata.
Hawayenta ne ta share Anwar yace "Allah dai yaji ƙansu, kinga tashi kiyi sauri ki shirya plz, frnds ɗina dana gayyato harsun fara zuwa, karya zama ke kaɗai ake jira" kamar bazata tashi ba ya miƙa hannu zai jawota, yauma tokare hannunshi yaji anyi.
Itama ganin zai riƙota ya sanyata miƙewa ta ɗauki kayan ta wuce ɗakinta, yabi bayanta yana cewa tayo sauri ta shirya, da yake sauri yake yauma ko kaɗan bai kula da abinda ya faru ba, duk da yanda ya ƙagara ya taɓata yaji yanda fatar jikinta take.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (Kishiya)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment