ABDUL WAHAB 36
©Rabiatu sk msh
®NWA
Kwana biyu tayi suna jinya ita da Abdul, ko motsi zatayi ji yake kamar yayi mata, kulawa sosae yake bata, yaa tattara ya dawo 'bangarenta da zam Duk da ba wani sakin jiki take dashi ba, saima haushinshi da takeji tana ganin don yaa mata yanda yakeso ne yake kulawa da ita.
Sai magana yake mata tayi shiru taa 'kyaleshi, fira yake mata anma kamar bada ita yake ba, Yace "yaushe zamuje kiga gida ki gaishe dasu hajia? A ta'kaice tace "babu inda zanje.
Yana murmushi yace "meyasa? "wata na nawa a gidannan ko 'kofar gida ban ta'ba le'kawa ba? Zaman kurkuku maa yafi zaman gidannan dad'i, ban ta'ba tunanin akwai zama da masoyin dake da 'kunci haka ba, ka cuceni yayanmu, sai Allah ya sakamin.
Tana cewa haka ya ri'ke baki cikin tashin hankali yace "mena miki na cutarwa sadeey? Ina iyakar 'ko'kari na wurin kyautata miki, duk inayi ne danki gane irin son da nake miki.
Tace "kanayi dai saboda wata manufa taka, shima aurena da kayi ba cutarwa bane? Yace "naa aureki ne don ina sonki, kema kuma kina sona, da sauri tace "koda ina sonka, bai nufin zan iya zama dakai ba tare da kana sona ba.
Yace "tohm ay ina sonki, a shirye nake nayi duk abnda zai tabbatar miki da hakan, tace "indai kana sona, rubutamin takardata, sannan zan shirya ka maidani gida.
Wani irin iska mai zafi ya furzar daga bakinshi, tsawon lokaci yana tunani kafin ya jawota jikinshi, Yace "idan kin barni kuma wazai na bani zumar da kika d'and'anamin? Zata tureshi yace "ki barni inyi abinda yasa na auroki mna, kinga ko a hakan kin biya bashin soyayyar da kikemin.
Turashi tayi da 'karfi ta mi'ke da gudu ta tafi falo ya tashi ya rufa mata baya, a falo suka had'u da hajia dake ta ranga'da sallama, da sauri ta fad'a jikinta tana mata oyoyo sai maida numfashi take.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment