```MAKASHINKA...```
45-46
©Rabiatu sk msh
Daren ranar har ƙarfe sha ɗaya na dare shamsuddeen da sadeey suna tare, saboda yanda suke jinsu cikin farin ciki sun kasa rabuwa da juna.
Hakanan ba don ransu ya so ba suka rabu.
Tana shiga gida tayi shirin kwanciya data tuna firarsu da shamsuddeen sai dai tayi murmushin jin daɗi kawai, wata irin soyayyar shamsuddeen na ƙara shigarta, ji take ya zame mata wani ɓangare na rayuwarta da bata iya rayuwa idan babu shi.
Harta kwanta barci yaa daɗe bai ɗauketa ba, maganganu ta fara jiyowa a falo, kuma sai ta jiyo alamar kuka hakanan dai hankalinta bai kwanta ba ta fara jin faɗuwar gaba, miƙewa tayi zata fita falon.
Tana buɗa ƙofar ɗakinta zata fita, saita ci karo da Shamsuddeen a ƙofar ɗakin da kamar takobi a hannunshi.
Bata san sanda ta riƙo hannunshi ba cikin firgici tana kallonshi muryarta na kyarma tace "meya dawo dakai har cikin gidanmu da tsohon darennan Shamsuddeen? Me kake shirinyi harda makami a wurinka?" hannu ya saka ya rufe mata baki, ƙara tsorata tayi ta fara tureshi daga jikinta.
Sai dai taji kamar ya buga mata wani abu akai, bata ƙara sanin meke faruwa ba ta sulale kawai a wurin ta faɗi ƙasa sumammiya.
Bata farfaɗo ba sai da safe gidan yaa cika da mutane sai koke-koke ake, wasu na mata fifita.
Tana tashi zaune cike da addu'ar Allah yasa mafarki take, kawai ta hango gawar mutum uku, miƙewa tayi tana tafiya daƙyar kamar zata faɗi ta nufi wurin gawarwakin da aka lulluɓe da fararen ƙyalle.
Wasu na cewa a riƙeta kar taje, wasu sukace a barta tayi musu addu'ah, gawar farko data buɗe ta yayanta shaheed, da sauri ta buɗe sauran sai ga momma da daddy, wata irin ƙara ta saka sannan ta ƙara sulalewa a wurin sai dai akayi asibiti da ita.
Har aka gama zaman makokin kwana uku batasan inda kanta yake ba, duk taayi baƙi taa rame.
Sai a cikon rana ta ukun ne ta buɗe idanunta, Abba ta fara gani sai momie, tsura mishi idanu tayi ko ƙiftawa batayi, abubuwan da suka faru sukaci gaba da dawo mata tana hango gawarwakin iyayenta dana yayanta.
Wasu irin hawaye ne masu zafi suke zubo mata, cikin muryar da bata fita tace "Abba ya kashemin iyayena ko?" su duka suka juyo basu sanda taa farka ba Abba, har suna rige-rigen matsawa inda take hawaye na zuba mata wasu na korar wasu.
Momie tace "sannu sadeey kin tashi? Alhaji kaje ka kirawo likita" Sadeey ta girgiza kai tace "Momie baku bani amsa ba, shamsuddeen ya kashemin su ko?" Momie tace "ki kwantar da hankalinki sadeey, keda baki lafiya"
Abba ne ya fara shessheƙar kuka saboda tausayin sadeey yace "Ya kashemin ɗan uwanah ɗaya daya ragemin, ya kashe matarshi da ɗanshi, sai da muka gama yarda dashi kuma ya gudu ya barmu, Yaa cucemu bazan taɓa yafe mishi ba,"
Cikin kuka tace "na tsaneshi Abba, tsanar da ban taɓa yima wani mutum ba" ta ci gaba da kuka Abba da momie na lallashinta suna ƙara kwantar mata da hankali.
Ranar Aka sallameta daga asibiti, kuma a ranar Abba ya wuce da ita kano gidanshi don jigawar ma gaba ɗaya ji take ta tsaneta.
Babu inda ba'a nemi Shamsuddeen a nigeria ba, duk wani office ɗin police akwai hotunanshi, har gidansu da sadeey taje saida aka kamasu suka ce su basu sanshi ba yana dai zaune dasu kusan shekara ɗaya yana taimaka musu.
Ganin hankalin sadeey yaaƙi kwanciya kullum cikin kuka da tunanin iyayenta ya saka Abba turata karatu waje, taso ta karanta lawyer ko ta karanci business, anma Abba yace sai dai ta karanta likita.
Tsanar Shamsuddeen ya saka ta tsani duk wani namiji, babban burin Abba kuma sadeey ta auri ɗanshi Anwar.
Cigaban labari.....
Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam
©Rabiatu Sk Msh
0 comments:
Post a Comment