```MAKASHINKA...```
13-14
©Rabiatu sk msh
Khadija bata matsa ba sadeey sai tasan abinda ke damunta ba, ita a ganinta ma ko aljanune suka taɓata, da taga dai taa warware ta shareta kawai sukaci gaba da firarsu saima ta ɗauke wayar daga wurinta.
Da yamma khadija ta fara shirin tafiya, sadeey taa shiga tayi wanka ta fito, batayi wani make up ba, ta buɗa wardrobe ɗinta zata ciro kaya, tana jawo su wata farar takarda ta faɗo da batasan da ita ba, bata kulata ba ta wuce ta shirya.
Leda biyu ta cikama khadija da tsaraba, daman koda zata dawo bata manta da ita ba wurin tsara ba, momie ma ta shigo mata da tata ledar ta turaruka da sarƙa mai tsada sosae, sai godia take.
Sadeey ta ƙara komawa ɗauko mayafi taci karo da takardarnan, ba tare da wani tunani ba ta buɗa tana dubawa, daga ƙasa kawai taga an rubuta ~masoyi~, bata tsaya karantawa bama ta nufi khadija da ita tana cewa tazo ta gani, kawai kamar an warceta ta faɗi ƙasa, basu ƙara ganinta ba.
Sadeey ta koma bakin gado ta zauna tare da dafe kai, khadija tace "kin kirani baki nunamin komi ba, kin koma kin zauna saikin sakani naayi dare kina ganin kamar garin jigawa nan kusa ne"
"ba nuna miki zanyi ba, yaa zama dole in faɗa miki damuwatah, don idan kika tafi bansan wanda zan faɗa mawa ba, bani da wacce ta fiki a duniyarnan" khadija tace "yanzu driver na jirana ki bari munyi waya kinga ko shawarace ma zan ƙara tunani.
Sadeey tace "ba maganar waya bace, kedai ki zauna kiji mana" komawa tayi ta zauna tana kallon sadeey taji ta inda zata fara, don ita tama fara bata tsoro, addu'a take Allah yasa dai bata fara bugu ba, tare da kuɗirin nemar mata magani ko nawa zata kashe kuwa.
Tas ta kwashe duka labarin abinda ke faruwa ta faɗama khadija, babu abinda ta ɓoye mata ta ƙarasa maganarta da cewa "wlhy babu abinda na faɗa miki ƙarya ya aciki, karkimin kallon marar hankali kamar yanda police sukaimin, don Allah ki yarda dani khadija wlhy Aljanine ke bibiyata.
Khadija ta numfasa tace "bawai naƙi na gaskata ki bane, ko inƙi yarda dake bane, anma ta yaya Aljani zaiyi hakan? Kuma fa shi da kanshi yayi miki rantsuwar shi mutum ne..." kafinta ƙarasa itama text ya shigo mata a waya, ta ɗauko ta duba ba tace ma sadeey komi ba sai dai taga ta miƙe ta fara dube dube itama tana zaro ido taƙi tsayawa wuri ɗaya, sadeey ta amsa wayarta ta duba saƙon.
"```tabbas ni ba aljani bane, naji daɗi da kike nunar da ita duk da farko banso ta faɗa miki ba, anma kiyi ƙoƙarin riƙe mana sirri, wannan tsakanina da itane kawai```
Sadeey wannan karon bata tsorata ba ganin yanda khadija tayi wuri wuri da ido, saima ta fashe da dariya harda riƙe ciki, hakan ya ƙara tsoratar da khadija, anan tabar wayarta mayafinta a hannu tayi hanyar fita tana waige waige, sadeey na daria ta riƙota hakan yasa ta ƙara tsurewa, kaɗan ya hanata sakin fitsari a wando, bakinta na kyarma take tofama sadeey addu'a duk wadda tazo bakinta.
Daƙyar sadeey ta iya shanye dariyarta tace "kinga malama nifa lafia lau nake, ke kinma fini tsorata, ki zauna mu ƙarasa magana mana tunda kin tabbatar da abinda nake faɗa miki" ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta koma ta zauna a ɗarare bayan taa gama ƙare ma ɗakin kallo har lokacin zuciyarta bugawa take.
Sai can ta ɗago da sauri tana gyaɗa kai da alama tunanin da tayi na wani lokaci ta soma samun mafita tace "ɗakin yaya Anwar ne kusa da naki ba? Sadeey ta gyaɗa kai, tace "babu wanda yafi kusa dake kamanshi, hakanan kike tada hankalinki kina zargin aljani, yanzu haka ban fidda rai da shine yake mana laɓe ba, jiyama yana laɓe yana jinki, babu wanda yasan da zuwanki police station sai shi, shiyasan dawowarki kasarnan, a yanda na lura babu wanda keyi miki wannan abun saishi.
Sadeey ta nisa tace "nima da a iyakar hujjojinnan aka tsaya dana yarda da maganganunki da ya anwar ɗinne, anma ya maganar numfashin da naji kusa dani lokacin dana dawo ƙasarnan? Ya Anwar maganar da mukeyi dake yanzu baima da numbata anma ina da tashi dana ansa wurin momie, ina dirowa ƙasarnan da kaina na tsaya na saya sim card ina sakawa a wayata message ɗinshi ya fara shigomin wanda na tabbata kome saida sim ɗin baisan numbar ba, kin manta dana faɗa miki na taɓa ganin wucewar mutum a mirrow? Wlhy yanzu haka saida naga takarda a cikin kayana da sunanshi a jiki, waya shigo ɗakinnan bayan momie? Kuma dai bata wuce ko ina ba iyakarta falo ma.
Khadija ta jinjina kai tare da sakin sanyayyar ajiyar zuciya tace "wannan al'amarin mai girma ne, babu abinda yake buƙata sai addu'a, kaina ya gama kwancewa, ni tsoran magana ma nakeji don nasan yananan yanajinmu.
Sadeey tace "ay shine, anma nidai ki taimakeni ki bani shawara khady" khadija tace "ta yaya? Bayan komi zan faɗa miki yanaji, ni banmasan mezan faɗa miki ba.
Duk suka ƙarayin shiru, sannan khadija harta miƙe ta koma ta zauna fuskarta wasai da alama ta ƙara samun wata hanyar tace "koda masoyi mutum ne, ko aljani ne, ko fatalwa ne, ina da yanda zamuyi dashi, don na taɓa gani a wani film kuma insha Allah nasan zaiyi aiki" da sauri sadeey tace "faɗamin don Allah ya zanyi? Tace "kawo kunnanki donma karya jiyo mu ya rusa mana shiri" da sauri sadeey ta matsa.
Ba masoyi da basu ganinshi ba, ko ni kasa jiyo abinda khadija take faɗama sadeey nayi, ina cikin dogon wuya harta gama faɗa mata, kamar bata gamsu ba dai tace "shikenan zan gwada.
Sukai sallama da khadija kamar karsu rabu, anma koba komi taji sauƙin zuciyarta tunda taa faɗama khadija damuwarta kuma ta bata shawarar da take tunanin zata ɓulle mata.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishiya)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment