ABDUL WAHAB 12
©Rabiatu sk msh
®NWA
A falo suka iske Sadeey ta 'bata ranta sosae, tana jinsu ta maida fuskarta gefe d'aya ta qara had'a rai ita a dole an 'bata mata rai, fatyma ce ta mata magana cikin fara'a tace "yadai matar yayanmu waya ta'ba mana ke? Tace "oho! Kinmasan anyimin ba dai dai ba kenan haka kawai don anga ina barci za'a fitarmin da masoyi, ta murgud'a baki tace "tukunnama ina kuka tafi? Da izininwa kuka fita? Meya hana a tasheni? Koma ina za'aje ay an fad'amin idanma baza'aje dani ba, don Allah yaushe rabonma damu fita dashi?
Magana take anma yanayinta kawai fatyma ke kalla tana dariya harda hawaye tace "kinga ni ki barni inje in fad'ama hajia mun dawo, keda in kika fara magana bakisan ki tsaya ba.
Sadeey tace "laah! Lallai fatima zaki fito ki sameni ne saikin fad'amin inda kika kaimin masoyi! Bata tanka ta ba ta shige tana dariya, shima Abdul tun shigowarsu ya kasa ri'ke dariyarshi yanda ta had'e rai shyasa ya wuce d'akinshi yasha dariya ya 'koshi, ga wani farin ciki da yakeji.
Fatima, sadeey, Abdul da hajiyah ne zaune a dinning, lokacin dinner ne har lokacin sadeey bata saki ranta ba, kowah yana cin abnci banda sadeey dako kallonshi batayi, hajia ce ta mata magana "yadai er gidan yayanta? Sai abncinki ya huce bakici ba?
Fuskarta a shagwa'be tace "niyau bazanci abinci ba, Tace "saboda me? Tace "hajia, ay Sadeey da Yaa Abdul sun sani, kawai bazanci ba! Hajia ta jinjina kai tana murmushi tace "tohm tunda tsakaninku dasu ne bazan shiga ba tsakaninku kun gyarota ni kunga tafiyatah! Sai da safe suka mata su duka.
Tana tafiya sadeey ta juya gefe d'aya ta 'kara turo baki, fatyma na dariya tace "nikam yayanmu ka fad'amin gaskiya banda sadeey baka ta'ba soyayya ba? Yace "naa ta'bayi so d'aya, saboda yaa lura da alamar da fatima ta mishi da ido.
Tace "wao! Gaskiya ta cika me sa'a, ya sunanta? Yace "Masoyiyah! Fatima ta qyalqyale da dariya tace "yayi masoya, ita da sadeey wa yafi kyau? Da sauri sadeey ta jiyo tana harararta ta sadda kai tana dariya, Yace "Haba kyakkyawar gaskece, ma'abociyar murmushi, idan kika ganta zaki tabbatar da babu wata budurwar da zata kaita kyau, sai dai sadeey idan tayi murmushinnan nata mai kyau.
Duk yanda sadeey taso d'aure fuska saida ta saki murmushi, fatima tace "anma wayafi sonka? Yace "Masoyiya mana, kinga ita kome zanyi mata bata fushi dani!
Da sauri sadeey tace "nifa ba fushi nayi dakai ba yayanmu, ay kaima kasan bani fushi dakai, kawai duk sanda zaka fita ne sai gabana yana fad'uwa, ina fargabar wata ta 'kwacemun kai, bansan halin da zuciyatah zata shiga ba, kawai dai nasan bazan iya jure rashinka ba!
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment